*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_Written by *NEESHAR.JAY*
*NEESHEJAY* @wattpad
Not edited 🤧💔
Page 12
#Miracle🦋
Sai washe gari da safe akayi discharging dinda daga hospital din har muka koma gida ban ko kalli sulaiman ba ballantana na mishi magana, muna isa gida bedroom dina na shiga tare da cire kayan jikina na fada toilet wanka nayi da ruwan zafi hakan yasa naji jikina ya Dan samu karfi, kayan da na cire kuma cikin washing machine na zuba su dan warin asibiti suke yi riga bubu Mara nauyi na saka gyaran dakin na fara yi Bayan na gama na fita parlour shima na gyara duk da ba dirty yayi ba Bayan na gama na kunna burner nan da nan ko Ina ya dauki kamshi, wayana na dakko tare da connecting Bluetooth da fan din parlourn dan irin fan din nan ce Mai bulb da Kuma Bluetooth, wakar aurena da Ali jita yayi na kunna na wuce kitchen ina Dora lunch dan yau nice da girki, white rice na dafa da sauce dinda yaji liver da veg. Bayan na gama na hada cucumber and lime juice na saka a fridge, koda na gama lokacin sallah yayi hakan yasa na wuce dakina.
Bayan na gama sallah na fito na kunna tv saboda wani irin kadaicin da bansan dalilin sa ba nake ji ba wacca nake son gani yanzu irin mommy saboda ita kadai ce nake gani naji kamar naga Ammi na hakan yasa na dauki wayana na kirata ringing biyu ta dauka sallama nayi Bayan ta amsa na gaida ta cikin fira take cemin "Auntyn ki ta gaya mun cikin ki ya zube" wata irin ajiyar zuciya na sauke tace "nan gaba ki kula kinji daughter duk abunda kika san zai saka ki aiki Mai wahala ki bar yinsa kinji saboda ba'a son Mai ciki na aikin wahala" da toh na amsata haka muka cigaba da fira duk sai naji kaso 40 na damuwa na ya ragu sosae, Ina cikin tunani ne naji muryar Faty tana sallama bayanta Kuma Farouk sai twins, sosae naji dadin ganin su dan ko ba komai bazan zauna zaman tunani ba, Bayan mun gaisa muka barke da fira kamar bani bace akayi discharging daga hospital nan suke gaya min an call on strike din da akaje ranar monday za'a cigaba da lectures.
Ba karamin dadi naji dan na gaji da zaman gida gashi saura mana shekara daya da few months tun da muna 300level ne. Sai yamma lis suka tafi bayan magrib Sulaiman ya shigo Kamar yanda na Saba haka na tarbesa yayi mamaki sosae bayan ya dawo sallahr isha mukayi dinner muna gamawa na kwashe komai na maida kitchen na koma daki da kallo ya bini dan yasan ba haka muka saba ba kullum sai na kalli series dina kafin na koma daki sometimes har gajiya yakeyi da min magana sai dai nace masa zuwa 10 an gama dan bana so nayi missing ko daya, Bayan na shiga daki wanka nayi na shirya cikin kayan bacci na, fata na kunna Ina nan messages suka fara rige rigen shigowa sai da na bari sun gama kana na fara dubawa tallan wani littafine ya tafi dani sosae wato Barikin sojoji na Neeshar.jay da gani book din zai yi dadi duk da free page kawae na gani koya daddyn jawaheer zaiyi ya gane wanda yama yarsa fayde duk da shima dabi'arsa ce bin matan aure da yan mata, 200 nayi transfer saboda samun cigaban book din. Chatting na cigaba dayi da frnds dina da yan gidan mu sosae muka sha fira da Waheedah data dameni da surutu har 10 kana na ajiye saboda shigowar da Sulaiman yayi luf nayi kamar mai bacci Ina jinsa har ya gama abunda yake yi ya kwanta, jawo ni jikinsa yayi ni kuwa na kara lafewa dan zuwa yanzu daya saba mun da kwana a jikinsa bana iya kwana sai cikin jikinsa idan yayi tafiya kuwa haka zanta juyi har safiya.
Tsakanin mata da miji sai Allah Bayan kwana biyu muka shirya duk fushin da nake dashi sai da ya nema hanyar da yasan zan sakko mu shirya, yau ne su mommy zasu zo kebbi saboda bikin yar kanwar daddy da zasuyi hakan yasa suka taho gaba dayan su in Banda yah fu'ad saboda aikin sa ya tsaida shi hmmm dama ko ba aiki bazai zo ba yanzu tunda auren sai next week suma kawai sun zo ne ayi shirye shiryen dasu, a gidana Waheedah da Husna suka ba karamin dadi naji ba, dakin dake kusa da nawa suka zauna tunda dama part din nawa 3bedrooms ne ranar yini mukayi fira har muka raba dare dama gashi Sulaiman part din Atika yake. Washe gari da safe ba yanda banyi dasu ba akan su tashi daga baccin safe har kusan karfe 9am gashi am having lectures by 10 haka na hakura na gyara gidan nayi breakfast na ajiye masu na fita coux am almost late, Allah yasa jiya nayiwa mota na full thank saboda bana so na tashi naga empty.
A gajiye na dawo gida na tarar da Waheedah da Atika suna fada kamar zasu daki juna dakyar na samu na lallaba Waheedah dake cewa "ai wlh adda da kin barni da ita da sai ta gane bata da wayau ballazagar mata kawai" cakumar Waheedah Atika taso yi Husna tayi saurin kwabar da hannun ta ta bugu da bango ba karamin zafi taji ba hakan yasa ta kwala kara sosae hankali na ya tashi dan bana son hayaniya ko kadan dakyar da sudin goshi na samu na rabasu Atika ta fita tana kumfar baki, cire hijab dina nayi na zauna Ina fadin "washh Allah Husna dan bani ruwa nasha Allah na gaji" mikewa tayi tare da dauko min ruwa da cup na bulbula nasha dan na dauko kishi sosae gashi yau road din ya zama busy saboda accident dinda akayi dai dai junction fin FMC numfashi na fesar na kalli Waheedah dake ta cika kamar zata fashe girgiza kai kawai nayi Ina mamakin hali irin nata son fada kamar me "hmmm Wlh baku San me na gani ba yau hankali na ya tashi" da sauri Waheedah tace "me kuma kika gani" kwanta da kaina nayi nace "accident akayi dai dai junction din FMC Wlh baku gani ba abun tausayi wani Mai Machine ne ya gitta ma wasu mata da miji da yara biyu daya macce dayan kuma namiji baku gani ba abun gwanin tausayi, gashi kafar matar ta shiga cika tayar machine dinsu kuma shi wancen ya gudu baku ga mutane ba amma kawai yan kallo ne gashi harda motar wani babba ta wuce sai dai kawai aka masa clearing hanya ya wuce abunsa, sae da akaje aka dakko bakanike kafin ya kunce tayar machin din, ko da aka ciro kafar har kashinta ana gani naman kafar ya wani bullutso Wlh ta bani tausayi sosae" sosai zaka ga alamar tausayawa a fuskarsu duk da ba'a gaban su akayi abun ba Husna tace "toh Adda an kaita hospital kuwa" "ehh wani bawan Allah aka samu ya cika ambulance aka shiga da ita asibiti sai ni dana bada gudumuwar kudin da na tsaya na cire na cefane 10k duk da nasan ba isa zasuyi ba Inaga ba Abba zan kira na gaya masa sai ya taimaka masu dan suna bukatar taimako gashi yaran duk sunji rauni amma ba sosai ba baban sune kawai Allah ya tsare masa wahala" Waheedah tace "Allah dai ya kyauta duniyar yanzu ba Mai din taimakawa kai Allah ya kyauta ya tsare gaba ya kuma bata lpy" suka amsa da Ameen.....
__________________
*Dedicated to Hassan Atk with love❤️*
___________________Wattpad people naga bakwa commenting and zuwa yanzu 400+ na karanta book din nan am expected to see more than 300 vote but no Ko comment bakwayi I don't why , is it that the book is not interested or what I don't know plsss keep voting and commenting guys. Love you 😍
Vote
Comment
Share
YOU ARE READING
Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ
RomanceBana gaya miki bana son haihuwa ba wlh saena zubar da wannan cikin naki dan a tsari na haihuwa ki shirya karbar magani" "Wlh baka isa ka sakani zubar da kyautar da Allah ya bani ba Sulaiman kayi duk abunda zakayi" "Kayi hakuri Sulaiman bazan iya kom...