Unforgettable Memory

180 28 1
                                    


#unforgettableMemory🦋

Sallah Adda Maryam tayi tare da daura masu macaroni da taji sardined,  sallah isha tayi kafin ta idar ya yayi, bayanta ta gama ta juye a tray dan d'a bi'arta ce a tray daya suke cin abinci duk da yaranta biyu waleedah sai Taufeeq, da yake yau ma mijinta ba'a part dinta yake ba hakan yasa da suka gama cin abinci ta saka waleedah dauko skl bag dinta sukayi assignment dinda aka basu a skl tare kafin taja su daki, wanka sukayi tare da saka kayan bacci suka kwanta sae da ta tabbatar da sunyi bacci kafin ta jawo diary ta cigaba da karatun ta.......

••••••••••••••••🦋

Kwana biyar kenan da fara azumi yau Kuma haka kullum Faty zata zo ta tayani aiki da dare ta koma, ba yanda banyi da ita ba akan ta dawo nan gidan da zama amma firr taki a dole kunyar Sulaiman take ji.

Yau gaba daya kannin sa a gidan zasu sha ruwa duk da bani bace da girki bai hanani hada abubuwa ba dangin su Kunun Aya zobo fruit salad sai kuma Arabian rice da Faty ta dafa a dole so take ace abincin yar uwarta yafi dadi, dariya kawai nayi nace "ba ruwana idan Atika ta jiki" tabe baki tayi tace "toh ita Atikan uwatace taji mana ko karya na mata bata iya girki ba" murmushi kawai nayi Ina dauraye bowls din da za'ayi amfani dasu ta teaspoon.

Tun karfe biyar da rabi suka zo gidan da yake basu cika shiri da Atika ba har dai mazan yasa suka dawo parlour na suka zauna dama su Bakwai ne a gidan su daga babban yayan su sai sulaiman sai mace Fareeda wacce ke bi masa sai maza biyu Tahir da Zayd sai kanwarsu Hauwa suna kiranta ukty sai auta Afreeya, tare da Fareeda muka karasa aiki tana tsokanana "matar yaya idan fa zanyi aure nan gidan zanzo nayi wata daya ina koyon abunci" dariya nayi nace "u are highly welcome" a haka muka hada duk abunda zamu bukata a gurin buda baki dan yau cikin yazo mun da sauki cikin rahamar ubangiji, filin dake tsakanina da Atika muka shimfida manyan tabarma guda biyu da carpet gaba daya muka fito har sulaiman, ana kiran sallah muka fara bude baki bamu wani tsaya cin abubuwa saboda kiran tada sallahr da akayi yasa mazan suka fita masjid.

Ba yanda banyi da Fareeda akan sallah amma firr taki tace ita a gida saita cika ciki take tashi dariya nayi nace "lallai kice kema irin Waheedah ce" dariya tayi tace "ai yafi kam da kayi sallah kana tunanin abinci" dariya mukayi nida Faty muka shiga ciki........


*Enjoy this page with your Guava smoothie🍹*


#TeamAfeefah
#TeamSulaiman

*Aslm Alaikum sisters*

*ykk ya gda da yara fatan komai lpy am writing this to inform you all that book dina Barikin Sojoji ya koma na kudi hope you guys will patronize as usual*

*Am repeating my self book Dina na kudi ne if you read without paying is your own cup of tea*

*my book is very cheap 200 Naira only you can transfer your card through this no 08100705645 or transfer through this account 2103696276 Balkisu Muktar Gulma UBA show your evidence of payment through this no 08100705645

*Dont forget to share this message plsss*

Vote
Comment
Share


*Lioness👑*

Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ  Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ  Where stories live. Discover now