Page 17
#PeaceOfMind
Ta karasa magana cikin daci da kunar zuciya kallon ta dr din tayi for few seconds kana tace "mrs stop beating around the bush and tell me directly what had happened" kara mayar da kaina kasa nayi idona fall hawaye cikin rawar murya nace "my husband is behind all that had happened baya son haihuwa baya son yara shi yasa ya zabi duk time din da nayi ciki ya zubar" na karasa Ina goge kwallar data zubo min cike da tausayi na tace "lallai kin hadu da kaddarar rayuwa Afeefah lallai ke abun a tausaya ma ce is this the first time that he try to impregnate you?" girgiza kai nayi nace "this is the second time" jinjina kai tayi tace "tasan cewa cikin ba gaba daya ya zube ba?" Nace "aa yanzu yazo ai" tace "good I will talk to ur mom dan I don't want him to know about this har sai cikin ya fito...yes and one more thing yanzu wane shawara kika yanke akan komawar ki gidan" da sauri na dago nace "bazan koma ba ni gida zan tafi wlh" na karasa wasu sabbin hawayen na zubo min tace "smart girl good idea idan kika tafi you shouldn't let anyone know about this pls idan yayi realizing that you're important to him maybe ya gyara halinsa sai ku zauna Lpy" godiya na mata Ina kara tunatar da ita akan karta gaya ma yan gidan mu tace "promise" kana ta fita.
Shigowar sa ce yasa nayi saurin komawa na kwanta tare da rufe ido dan bana son abunda zuciyata ke gina mun ya cigaba da habaka shi yasa kawai nafi so na kyalesa for a mean time maybe zan daina jin abunda nake ji.
Kallo na yayi tare da maida kallon sa ga hannuna dake kan flat tommy dina ya kama Ina jinsa na masa banza dan i will not open any door da zai bashi damar samun bani hakuri har sai ya gane ya mun ba daidai ba sannan kuma ya gane abunda yake aikatawa ba Mai kyau bane. As always cikin cool voice dinsa ya fara magana "ban san meya shiga kaina ba Afeefah ban sani ba har cikin raina bana son abunda na aikata maki but bakya ji da ace kina Shan drugs din da nake baki da duk hakan bai faru ba I told you several times without number bana son haihuwa wlh bana sonta Afeefah tun banyi aure ba na ratsara ma kaina wannan abun bana son lalaura ta mun yawa and what I hate most is kukan yara abun na damuna har cikin brain dina nake jin kukan su and hakan na dagula mun lissafi Afeefah...."
Daga masa hannu nayi nace "me yasa ka kasance daya daga cikin wadan da basa son kyauta da ni'imar da Allah ya masu wasu na chan suna neman haihuwar ido rufe amma kai da Allah ya bama ka kasa gode masa na tabbata sulaiman da ace haka sauran maza suke da ko ni da kai bamu zo duniyar ba bana tunanin ko iyayen mu za'a haifa Ina mai shawartar ka da kayi gaggawan tuba ga Allah dan ka nuna masa baka gode ba ni yanzu idan aka you discharging dina am going home coux I need to rest a lot zaka iya idan duk ranar girki na ya zagayo kazo gida kasha ruwa amma na barma Atika kwana har naji sauki na dawo" da mamaki yake kallona he was even out of words at that time shiru tayi Chan yace "thanks LOML❤️ Allah baki Lpy zanyi tunani akan maganar ki mrs Ba komai kije gidan Allah baki Lpy" Ameen nace Ina mai rufe ido na daga nan shima yayi shiru sai dai kallona da yake yi ajima ajima ya sauke ajiyar zuciya a haka dai har ya dora kasan a kan gadon hannun sa cikin nawa ni dai bacci nake saboda drugs din da nasha akwai na bacci dan dr tace I need to rest a lot shima ashe baccin ya fara.
Aunty ce ta bude kofar ta shigo ganin mu a hakan yasa taji tausayin mu sosai cikin ranta ta fita gaba daya maganar da sukayi da dr ta daure mata kai me yasa zata ce kar a sanar da sulaiman cikin matar sa ba gaba daya ya zube ba Bayan sun san hankalin sa ba'a kwance yake ba kuma abin jin dadi ne idan yaji nasan ma zaifi mu murna" shiru ta danyi Chan tace "Koma dai mene nan bada jimawa ba ai cikin zai bayyana kansa" da wannan tunanin ta karasa kan carpet ta zauna.
Kiran sallahr da akeyi ne a cikin masjid din hospital din ya tasheni daga baccin da nake yi kallon sa na tsayayia cikin raina da zuciyata Ina jinjina girman son da nake masa amma yanzu ji nake kaso 30% cikin din da nake masa ya ragu, shafa kansa nayi da dayan hannuna ina kokarin cire hannuna daya rike cikin nasa, ji nayi ya Kara rike hannun hakan yasa na kara kokarin kwacewa sai ya bude idon sa da suke cike da bacci dauke kai nayi daga kallon da nake masa nace "an kira sallah fah" kiss ya kaima hannun nawa ya mike ya fita, Koda su Aunty suka shigo Ina toilet ban jima ba na fito carpet din da Faty tayi sallah ta shimfida min tare da miko min hijab na saka nima na gabatar da sallahr Bayan mun idar muka zauna zaman fira Aunty na tambaya na ya jiki nace "alhmdllh" tace "Yauwa dr ta miki magana akan karki gaya ma sulaiman cikin ki ba duka ya zube ba" girgiza kai nayi nace "aa bata fada min komai ba" Aunty tace "toh yayi" kallon Faty tayi tace "kin gaya ma su Maryam abunda ya faru" tace "ehh Adda tace zata zo Bayan sallah maybe ma tana hanya Adda Hadeeza kuma sun tafi sokoto siyan kayan babynta na sallah" Aunty tace "toh yayi dr tace zuwa dare zamu tafi" kallon Faty nayi nace "wai waya kayo ni hospital ne" faty tace "nice mana koda nazo na ganki a kasa dan inata doka sallama naji shiru sai Atika da taleko ta Koma shine abun ya bani mamaki ba shiga cikin gida da taimako mai gadi na saka ki a mota muka zo nan dan nasan waccen banzar kishiyar taki ba zuwa zatayi ba ni na rasa wace irin macece ko last fa da cikin ki ya zube bata zo ba maybe kuma tana bakin cikine dan ita ko bari bata taba yi ba" Aunty tace "ya isa bana son wata magana" daga a Faty ta kama bakinta tayi shiru. Ba jimawa Adda Maryam tazo daga nan muka cigaba da labari sulaiman kuma sai dai ya kirani a waya akan anjima zai dawo nace toh. Sai Bayan Shan ruwa aka bani sallama muka hada kayan mu muka koma gida.
Tun daga wannan lokacin kullum sulaiman sai yaje gidan mu idan ya dawo daga skl kuma Bayan Shan ruwa ma sai ya dawo a haka har na fara jin abunda nake ji a kansa ya ragu idan nace Sulaiman baya kula da iyalansa nayi karya Sulaiman na bani duk kananin wani farin ciki da ya mace zata nema a gidan mijinta sulaiman namiji ne Mai son kyautata ma iyalin sa yana bakin kokarin sa ban rasa ci ko sha ba haka ma sutura dan duk lokacin da taga wani abun kyale kyale zai siya ya kawo mana sai dai kuwa da kalar nasa kuma shi ba ruwansa da maganar sai waccan ta zaba aa a Leda daban zai saka ya kawo maki idan ba gani kikayi a jikin yar uwar ki ba bama zaki San Wane iri bane nata har kiji haushi amma duk da haka Atika na jin zafi idan taga nawa sai taita korafin nawa yafi nata kyau amma duk da haka bazai hana sa yin yanda ya saba ba kuma sosai yake kimanta yin adalici a tsakanin mu gashi duk wata 30k na kayan abinci dangin su kayan Miya da Kayan yaji sai 10k na kashiwa wannan ka'idar sa ce. Yanayin lecturing ne dan he has passion for it amma banda shi suna family business hakan yasa yake samun na kansa.
Matsalar sulaiman daya ce wannan rashin son haihuwar itace babbar matsalar sa da a kullum Ina masa addu'a akan Allah ya yaye masa wannan abun.
_________________________
*Dedicated to Hassan Atk with ❤️*
_________________________Don't forget if you want my book Barikin sojoji zaku tura card through this number 08100705645 and send your evidence through the number also don't forget at 200 only
Vote
Comment
Share#TeamAfeefah
#TeamSulaiman*Lioness👑*
![](https://img.wattpad.com/cover/210623472-288-k184867.jpg)
YOU ARE READING
Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ
RomanceBana gaya miki bana son haihuwa ba wlh saena zubar da wannan cikin naki dan a tsari na haihuwa ki shirya karbar magani" "Wlh baka isa ka sakani zubar da kyautar da Allah ya bani ba Sulaiman kayi duk abunda zakayi" "Kayi hakuri Sulaiman bazan iya kom...