Diary 3

247 34 2
                                    

*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_

Written by *NEESHAR.JAY*

*NEESHEJAY* @wattpad

#diary3

Page 22

A hankali ma fara bude idona da suka min nauyi ga zafi kamar an watsa min barkono na daura su a saman dan din da ke aiki a hankali da alama dai an rage mata gudune ko Karin mikewa na fara yi da sauri na koma jin wani irin azaba da radadi a kafa na da suka ziyarceni ga wani nauyi da ciwo da kaina kemin hakan yasa na koma ba shiri na kwanta tare da runtse idona komai ya shiga dawo mun daki daki wani irin razanannen kuka ya kwace min duk da azabar da nake ji a kaina bai kai wacca nake ji a zuciyata ba.

Jin kukana ne ya saka su Aunty dake bakin kofa shigowa da sauri sai juye juyaen kai nake gaba dayan su rudewa sukayi ya ukasha ya fita da sauri kiran dr ko da suka dayo dr din yace suyi hakuri su jira a waje allular bacci ya kuma min kafin ya fita yana kallon Aunty yace "dawa zan iya yin magana cikin ku" Aunty tace "Ba komai muje" dr ya bi hanyar office dinsa tana  biye dashi a baya har suka isa zama yayi tare da nuna mata kujerar dake gabansa ya cire glasses dinsa yace "hjy ku kwantar da hankalin ku insha Allah zata samu Lpy sai dai wannan kukan nata bashi da nasaba da wannan ciwon nata ga dukkan alamu akwai abunda ke damunta dan har yayi mata causing hawan jini and jininta ya hau sosai shi yasa ma na mata alluran bacci dan ya samu hutu" gujum Aunty tayi kirjinta na kugude tabbas akwai abunda Afeefah ke boye masu da basu sani ba dan yarinyar akwai zurfin ciki kamar me godiya tama dr kana ta fita tunani falll zuciyarta bata iya samu tama ko daya daga cikin bayanin abunda dr yace mata ba duk da tambayar da suke mata.

Bani na farka ba sai Bayan sallahr isha sosae na galabaita kallo daya zaka min na baka tausayi gaba daya na rame kamar ba ni ba harda wani baki ya fuskana data kumbura suntum kaina kam yasha bandage haka ma kafa na wasu siraren hawaye ne suka dinga bin kuncina idan ba kukan nayi ba bazan taba samun nutsuwar zuciya ba.

Aunty data fita karbo kayan da zasu bukata na zaman asibitin ce ta shigo dauke da flask sai wani basket dake dauke da Kayan tea a Bayan ta kuma ya Ashir ne da matar sa, lumshe ido na nayi tare da mayar da kaina wani direction cike da karfin hali.

Zama sukayi suna min ya jiki amma ko magana bana son tsabar aabar da kaina keyi ji nake kamar ya tsage ya rabu biyu na huta Ammi dake Bayan Aunty ta fara kananun kuka alamun dai ta tashi daga baccin da take, karbar ta matar ya Ashir tayi tana rarrashi madarar yara Aunty ta hada mata ta bata dan tasan yarinyar dai yunwa take ji kuma ai tayi kokari gashi sai bacci take tun Bayan la'asar.

Suna zaune har kusan 9 shigowar Sulaiman ne ya saka su ya Ashir mana sai da safe suka tafi Aunty ma cewa tayi zata je ta dawo hakan yasa aka barmu mu biyu kawai cikin dakin. Duk da idona a rufe suke bai hanani gane shi bane ko dan kamshin turaren sa da nake ji ya zame min kamar guba yanzu bana jin iya magana shi yasa koda ya kama hannuna ban tanka  ba dan ki bude idona banyi ba haka ya koma ya zauna saman kujera. Ji nake kamar ana watsa mun wuta ko garwashin ta a jikina zaman sa dakin ya haddasa min wani irin ta shin zuciyar da nake jin ta  can gefe ta makale ga wani nauyi da tayi kamar dutse har wani amai amai nake ji ba abunda nake bukata yanzu daya wuce ruwa masu sanyi da zansha dan ji nake kamar wuta na ruruwa cikin kirjian ya makoshi na daya bushe kamar sahara.

Shigowa Aunty tayi ta zauna kan carpet din da ke a shimfide daga chan gefe tana faman rarrsahin Ammi sai  10 kana yama Aunty sallama ya tafi sosae na sauke ajiyar zuciyar da har Aunty sai da taji da sauri ya ajiye Ammi ta taso zuwa gareni cikin muryana da bata fita nace "zansh ruwa" jimmm Aunty tayi kana ta bude fridge din dakin ta dakko min ruwa masu sanyi kadan ta zuba min a cup sbd dr yace kar a bani abu mai ruwa saboda yawon fitsari sosae.

Shanyewa nayi tasss nace ta kara tace "aa Afeefah yi hkr dai ki bara su hakanan" a hankali hawaye suka fara bin ido na sbd wani bakin ciki daya dirarmin yanzu da Sulaiman bai min haka ba taya zaayi ma ace karna sha ruwa saboda Allah.
Aunty kuma ganin hawayen da nake yi yasa ta karamin dan na bata tausayi sosae. Bayan na shanye na koma na kwanta itama tayi shirin kwanciya.

Washe gari da safe masu zuwa dubiya suka dinga shigo mana wasu ma tun ban farka ba sai da dr yace kar a bari kowa a koma shiga kama na samu salama duk da bawai Ina amsa su bane. Haka ma yan  su Sulaiman sun zo da yawa.

Ammi kam sai kuka take sosai take bani tausayi dan ba yanda za'ayi na iya bata Nono saboda yanda nake kwance nima kaina na gaji da kwanciya a haka gaba daya jikina sama yake kallo ba halin na juya dama ballantana kafar haguna dana karye.

A haka har akayi sati daya kullum baki na zuwa haka ma Sulaiman shima kullum sai yazo amma har yanzu abu daya nake ji gane dashi Sam bana bukatar ganin sa kusa dani ko kadan, zuwa yanzu kam alhmdllh kaina ya rage ciwo dan har an kunce min bandage din da aka daura sosai nake shan jinya, abban mu daya zo ma kamar yamin kuka ganin halinda nake ciki na zama abun tausayi ga kowa.

Ranar Wednesday da dare Bayan sallahr isha Ina zaune na jingina bayana da pillown da aka dora mun da bango kafana kuma na dora ta akan wani dan table din da tsayinsa tsayin gadon ne kuma a kai nake dora kafana duk lokacin da na bukaci zama, Ammi ce a hannu na Ina bata Nono idona a lumshe na fada duniyar tunani daya zame min aboki yanzu a koda yaushe. Banji sallamar sa ba sai kamshin turaren sa daya fara kaima hancina ziyara bude idona nayi a sukayi ja kamar garwashi na zuba su akan sa kallon seconds na masa tare da kawar da kaina gefe Ina sauke numfashi a hankali Ammi kuma na cire  nonon daga baki na ajiyeta Ina gyara mata kwanciyar ta nace "kazo kaga na mutu ne ko me?" Jiyayi  ta masa dirar makiya a kunne baice komai ba ya zauna na tabe baki Ina janyo wayana dake gefe.

Kallona yayi yace "ya jikin ki" still kaina a kan wayar nace "Kamar yanda ka gani"

Smiling yayi yace "Allah Kara afuwa" banza na masa shi kuma ya cigaba da kallona dago idona nayi daga kan wayar ina zuba masa su nace "burinka ya kwanta yanzu abu daya nake jira daga gareka bana son sake ganin ka a asibitin nan saida takardar Sakina dan shine alfarma ta karshe dazan iya nema daga gareka sannan ina so ka cire ni daga cikin zuciyar ka dan wlh bazan taba komawa gidan ka ba ko a mafarki kuwa dan haka ka tashi ka fice mun daga gani karka dawo sai da abunda na bukata idan ba haka ba kuwa alkali ne zai rabani da kai now get out" still yayi yana kallona nasan cewa he was very shocked da abunda na fada kawar da kai na nayi gafe Ina tabe baki shi kuma ya cigaba da kallona a masifance na jiyo nace "get lost malam ka wani tsareni da idanu kamar maye" nan ma banza yamin sai ga aunty da Adda Hadeexa sun shigo dan su jin muryana da sukayi a sama yasa suka shigo da sauri sa dai ganin sulaiman zaune hankalin sa kwance kamar ba daga nan bane akayi tsawar yasa suka koma.

Mikewa yayi yana kallona da idonsa da sukayi jajir ya fice kamar iska wani marayen kuka ne ya kwace min aiko na hau yin sa kamar zan karar da hawaye na sai da naji an bude kofa nayi saurin goge hawayen da suka ki daina zubowa.

Zama Aunty tayi tana nazarina sosae can tace "ban San meke damun ki ba Afeefah sai dai nasan koma menene ba karami bane tunda aka kawo Ki asibitin nan na kula akwai matsala tsakanin ki da mijin ki sai dai kin ki ba kowa damar tambayar ki abunda ke damun ki wai me aka maki meke tsaka nin ki da mijin ki ki sani boye damuwa baya maganin ta sai dai ya Kara haddasa wata damuwar baki da wanda ya fini a duniyar nan idan baki fada min damuwarki ba wa zaki fada ma Afeefah?" Aunty ta karasa maganar murya a karye................

     Toh fans ku zo ku bama Hajiya Aunty answers din tambayar ta dan ku komai kun sani🤩⛹🏻‍♀️🤾🏻‍♀️

*Alhmdllh am getting better yanzu thanks so much for your concern lallai naga kauna from you guys DM messages wasu ya grps wasu Kuma sun kirani Allah ya bar zumun ci nagode I lobiyu wijiga wijiga* ❤️🔐

#TeamAfeefah
#TeamSulaiman


Vote
Comment
Share

*LIONESS👑*

Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ  Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ  Where stories live. Discover now