Page 5

310 47 4
                                    

*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_

Written by *NEESHAR.JAY*

*NEESHEJAY* @wattpad

Page 5

Bayan ta tashi daga gurin Abba dakinta ta wuce Kota kan Ammi bata fi ba bata son gayawa iyayenta abunda ya faru sbd tasan halin Abba da zafi Aunty kuma da fada yanzu sae su yanka ma Sulaiman sammacin zuwa kotu tafi so su rabu lpy maganar bashi yar shi kuma koda duniya ce zata taru akanta ba zata mae data hannun shi ba, wani irin radadin zafi take ji cikin zuciyarta kunci ya mata yawa bata Jin akwae wata 'ya mece data taba going through the same pain da tayi going through, ko a movie , novels ko labari bata taba jin wacca tayi rayuwar aure irin nata ba tayi tunanin cewa aure ana yinsa ne akan so kauna da aminci amma bata taba tunanin things will turn out haka ba auren soyayya sukayi da sulaiman suna son junansu kamar su hadeye juna amma bayan amarcinta komae ya fara sauyawa rayuwa ta fara mata zafi amma bata taba gayawa kowa ba duk da yan gidan su sun san halin kishiyarya amma bata taba kae masu korafi akanta ba. Share hawayen da suka zubo mata tayi tare da jawo wani hadadden diary Red colour da decorations din rose flower katuwa akae, budewa tayi kusan karshe ta fara rubutu tana hawaye.



.................🦋


"Haba Sulaiman dan Allah ka gaya min meke damunka tsawon shekara 8 kuna tare ban taba ganinka a rin wannan yanayin ba"

Furzar da iska yayi yace "ba komae Atika ki dae na matsamin da tambaya kin San bana so na farko dae ni ba yaro bane ko?"

Tace "toh Allah ya baka hkr dama kudi nake so zan sayi ankon bikin maryama yar wajen mama Yaha toh kasan"

Yace "ok bikin ya tashi kenan?"

Tace "ehh"

Yace "ok nawa kike bukata"

Tace "ko 20k ka bani ya isa dan anko biyu ne to sae kuma kudin dinki da takalma da jaka nasan ma bazasu isa ba but I will manage"

"Hmmm Atika kenan toh zan tura miki a account"

Rungumeshi tayi tace "thanks my man" kana ta fita da kallo kawae ya bita ji yake kamar ya saka ihu ko nauyin da zuciyarsa ta masa zae ragu ko yaya ne.

Atika kuma tana fita kitchen ta wuce ta Kira kawarta Bayan sun gaisa tace "zan turo miki da dubu goma kinga sae ki hada da wancen dubu hamsin din ki siyomin lace din sae ki bada dinki tunda kinga Abuja sunfi nan din iya dinki ko"

"Shegiya kawata matar lecturer karki damu zaki samu dinki mae shegen kyau da zaki kece raini dashi duk inda kika shiga sae an kara kallon ki ta wajena"

"Yauwa mutuniyas zakiji alert harda na dinki duka"

"Tau yayi sae na jiki"

"Uhmm" tareda kashe wayar wani irin nishadi take ji itadae ba yar gidan masu shi bace amma ta auri miji mae kudi da yake mata maganin matsalarta

*Asalin Atika*

Malam Shamsu shine sunan mahaifin Atika da matar da Hajiya Huraira yan kebbi ne suma.

Malam shamsu shagon siyar da turare yake dashi a cikin kasuwa itace sana'ar sa yana da rufin asiri dan yana da zuciyar yi kuma yasan zafin nema.

Atika ita kadae ce yar da Allah ya bashi hakan yasa suka dauki son duniya suka dora mata duk abunda take so shi ake mata bugu da kari daurin gindin da ta samu a gurin mamanta dan itama macece mae son abin duniya hardae gashi tana ganin yanda yaran 'yan uwanta ke auren masu hannu da shuni hakan yasa ta dauki kudurin aura ma Atika Mai kudi ko cikin dangi idan wani yace yana sonta idan har bashi da kudi ko kallonsa bata yi. Wannan itace bakar akidar da Atika ta tashi da ita dan a kan wannan turbar uwarta ta daurata.

Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ  Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ  Where stories live. Discover now