*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_Written by *NEESHAR.JAY*
*NEESHEJAY* @wattpad
Page 23
#EndOfDiary
Shiru nayi Ina kallon Aunty duk yanda naso dakewa kasawa nayi sai kawai na fashe da wani irin matsanancin kuka bata rarrashe ni ta barni sai da nayi mai isa na tambayar dazun ta kara jefo min cikin kuka nace "dan Allah aunty karki matsa da tambayar nan zuciyata zata iya bugawa wlh na roke ki aunty ki dan Allah..." kuka ne yaci karfi na hakan yasa sauran magana na makalewa.
Shiru aunty tayi bata kuma min magana ba ta gyara mun kwanciya na ta koma itama ta kwanta gaba daya wannan daren haka muka kwana cike da tunani daga karshe Aunty data ga baccin ba zuwa zaiyi ba ta mike ta shiga nayi ta dauro alwala ta fito ta shimfida carpet ta tada sallah Ina kallon ta daga karshe ban San lokacin da bacci yayi awan gaba dani ba.Haka na cigaba da jinyar kafana Kuma alhmdllh kullum Ina ganin cigaba, ga yan gidan mu da kullum a asibiti suke yini Ammi ma yanzu komai nata ya koma gurin Aunty kasancewar banda Lpy yasa ake hada mata da madara yanzu tayi mulmul da ita ga sonta kullum kara ruruwa yake a zuciyata. Su mommy gaba daya sun zo har da ya Fu'ad da matar sa, tambayar da Aunty ta min ba wanda bai min irin ta ba a cikin su sosae kowa ke ganin damuwa karara a tare da ni wanda ba sai ka tambaya ba mommy haka taji kamar ta make ni su Adda Hadeexa da Adda Maryam ma haka kai harta da kanni na sai da suka tambaya meke damuna.
Amsa daya nake basu wacca ta firgita kowa a cikin wato *Saki* neman Sakina da nake a gurin Sulaiman ne ya tabbatar masu da akwai matsala babba kuma yau ni da baki na nake neman saki a gurin mijina lallai koma menene Sulaiman ya mun to yakai karshen hakuri na ne gaba daya familyn mu ba wanda bai sanni da hakuri da sanyin hali ba shi yasa kullum suke tausaya min saboda sun San Koda wuka aka saka ana deban naman jikina bazanyi magana ba ba wanda yace min ko kala a cikin su haka ma abbana daya ji wannan maganar ba karamin rudu ya shiga ba hakan yasa ya nema sulaiman shi kuma yace bazai iya magana sai dai su jira idan naji sauki dan shi gani yake kamar zafin ciwo ne yake saka ni fadar wadan nan maganganun.
Few weeks later.......🦋
Alhmdllh baki sauki dan yanzu har na fara takawa da kafana nakan dan zagaya cikin asibitin da yamma ko da safe, yauma kamar kullum Bayan da dawo daga motsa fakar sai ga sulaiman yazo kallo daya na masa na dauke kai, gaba daya yayi zuru zuru kamar bashi ba sai kace wanda ya shekara yana jinya ko dai ni da nake rashin Lpy na fisa kyan kallo. Zama yayi kan kujera dama aunty taje gida ita da Ammi su dawo nurse din data rakoni dakin kuma ta fita bayan ya taimaka min na zauna duk da yanda ya koma hakan baisa naji dingon tausayin sa ba burus nayi dashi kamar nan San da zuwan sa ba na cigaba da using waya na.
Numfashi ya fesar tare da lumshe ido ya bude na saka hannu a aljihu nace "kace yau kayi abun kirki Sakina zaka bani?" dan har ga Allah tunanin da nayi kenan ganin ya saka hannu cikin aljihu.
Girgiza kansa yayi tare da watsa min manyan ida mun sa yace "you're unbelievable gsky Afeefah" tabe baki nayi nace "Uhmm as u said ni dai yanzu ka tashi ka bani guri kuma ina nan aka bakana karka sake zuwamin nan sai tare da saki na" kallo kawai yake bina dashi har na kai karshen zancena ya matso kadan ya kama hannuna yana dubawa kwace hannun nayi Ina watsa masa harara yace "I thought you're fine ashe har yanzu da sauran ciwon naki Toh idan kika ji sauki zamuyi magana nasan zafin ciwo ne ke damun ki"
Harara na watsa masa idona na chanza kala zuwa ja cikin dacin rai nace "stop making fun of me malam Lpy na qalau and am in my right sense idan ma akana tunanin zafin ciwo ne ke saka ni wannan maganar then you're wrong Sulaiman am tired of begging since from the first day na gaji sulaiman sai yanzu nake nadamar auren ka ban gane komai ba a zamana gidan ka kai kanka ka takura ma rayuwata duka ba irin wanda baka mun ba haka ma zagi you really showed me the other side of you Bayan kai matar ka ma ba bari na tayi ba kai da ita kun saka ni gaba duk hakurin da nayi bai chanza komai ba a tunani na kuma haifar abun ciki na da zanyi zai kawo komai to an end ashe nice kawai ke haukata kullum cewa kake kana so na but for once ban taba ganin wannan son da kake min ba why Sulaiman why you've ruined my life and my reputation I don't have any piece of mind yanzu komai ya jagule min abunka bai tsaya a kaina kadai ba har yar cikin ka Anya kuwa akwai imani a tare da kai kuwa Sulaiman?" Da sauri ya rufe min baki da hannun sa yana girgiza min kansa kawar da kaina nayi tare da rike masa hannu nace "ka taba nunanin yanda nake ji acikin zuciyata kasan me yan uwana zasu maka if they find out the truth, they wouldn't take it likely with you Sulaiman kap gidan mu ba wanda ake so irina kaima shaida ne abunda yasa Abba na ya baka aurena saboda yasan baban ka and yanzu ka bata zumuntar dake tsakanin su" shiru nayi Ina sauke ajiyar zuciya hawaye na cigaba da zubo min a idanu jinginar da kaina nayi jikin bango na lumshe ido murya can kasa nace "get lost" shiru bai amsani ba ni kuma sanin cewa yaji abunda na fada yasa nayi shiru ban maimaita masa ba.
Chan ya mike ya fita jiki a sanyaye da harara nabi bayansa dan yanzu ba abunda nake so daga gurinsa sama da Sakina I just want him to free me from this kaddararren relationship that has no value neither respect, yana fita na sauke ajiyar zuciya tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Aunty da zasu shigo suka kusa cin karo da Sulaiman ko gaisuwa bai samu damar mika masu ba dan shi kadai yasan abunda yake ji a lokacin jin kuka na kuma a ciki ne yasa suka karasa shiga da sauri itada Faty da sauri suka karasa gurina Aunty ta zauna kan gadon tana tambayar Lpy fadawa nayi kanta ina kara sakin wani kukan sosae suka ji tausayina Faty ma harda hawayenta, cikin kuka nace "Aunty Kice ya bani Sakina wlh bazan koma gidan sa ba Aunty Allah bazan koma ba" rarrashina tayi ta yi har nayi shiru na koma sauke ajiyar zuciya daga karshe bacci ne yayi gaba dani. Gyara mun kwanciya tayi ta mike ta koma waje ta zauna Faty na haka gaba daya abun duniya ya ishe su.
Kullum abunda ke daruwa tsakani na da Sulaiman kenan Bayan sati daya akayi discharging dina daga asibitin muka kwashi kayan mu sai gida kafa ta kam alhmdllh sai dai ban cika motsa ta ba hakan yasa su Aunty kullum fada suke min.............
•••••••••••••••••🦋
Adda Maryam ta ajiye diary din ta sulale a gurin tana hawayen tausayin yar uwarta lalai taga jarabawar rayuwa shiru tayi tana tunani chan ta mike ta shiga ciki saboda kiran sallahr magrib din da aka fara.
_______________
AFEEFAH
_______________i will not update sai lokacin da kuka shirya voting and commenting so know this
Bye👋#TeamAfeefah
#TeamMalamSule😹Vote
Comment
Share*Lioness👑*
YOU ARE READING
Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ
RomantizmBana gaya miki bana son haihuwa ba wlh saena zubar da wannan cikin naki dan a tsari na haihuwa ki shirya karbar magani" "Wlh baka isa ka sakani zubar da kyautar da Allah ya bani ba Sulaiman kayi duk abunda zakayi" "Kayi hakuri Sulaiman bazan iya kom...