*Haka Nawa Mijin Yake*🦋
_(Nefarious Hubby)_
Written by *NEESHAR.JAY*🦋
*NEESHEJAY* @wattpad
*TAQABBALALLAHU LINNA WAMINKUM EDIL_MUBARAK ALAINA WA'AIKUM am wishing All the entire Muslim ummah a very happy Edi-Mubarak May almighty accept our inadat forgive us and have mercy on us, may He (Lord) take away this Covid 19 away from us and the entire universe in general*
#staySafe*PAGE 1*
" Na kore ka Dan Allah ka bani takar dana na huta wlh ko ganin ka Sulaiman bana Son yi a rayuwata na tsaneka tsana mafi muni ka barni na huta da tabon da kabar ni dashi bazan iya daukar masifar da tafi wannan ba hakan na nufin barin numfashi na a doron kasa"
Dago idonshi da suka rine suka sauya kala sbd tsabar rikici zuwa ja ya daura su a kanta ba abunda yake gani na fita daga idonta sae wutar dake tafasa acikin zuciyar ta wani kalar rikicin da bae san ranar karewarsa ba yake hangowa haka kuma yake hango zallar soyayyah da qaunar da Afeefah ke masa zuwa tsana mafi muni.
Dafe Kansa dake barazanar barin Kansa yayi yana fitar da wani kasalallen numfashin mae fitar da zafin da tafarfasar za zuciyarsa keyi ko Magana gaba daya ya kasayi sbd yanda yake jinsa ji yake kamar zae fashe.
Juyawa tayi zata fara tafiya tace "karna Kara ganin ka kofar gdan nan idan har bada takardana kazo ba idan ba haka ba kotu ce zata rabamu na barka lpy"
Wani irin naushi ya kaiwa motarsa da ace acikin hayyacinsa yake da yaji zafi sosae amma yanda yake ji a zuciyarsa bae kae ko rabin zafin hannun bae ji ba ya rasa gane wace irin masiface yake hangowa a idanun yarinyar da tafi kowa hkr ba yasan cewa ya cutawa Afeefah cutar da shi Kansa bae San adadi ba amma haka ta hkr ta zauna dashi.
Mota ya shiga ya fige a guje ko gani bayayi motocin kan titi sae basa hanya sukeyi ikon Allah ne kawae ya kae sa inda zashi, ko parking bae tsaya gyarawa ba ya fito yayi cikin gda cikin sauri kamar zae Kifa addu'a kawae yakeyi Allah yasa kar ya hadu da Atika a hanya dan komae zae iya faruwa a yanda yake Jin kansa.
Tana parlour zane tana kallon daily series dinta Deception ya shigo ta tsorata matuka da ganin yana yinsa bata taba ganinsa a irin wannan halin ba sae yau haka take ganinsa kamar mayun wacin zakin da yayi shekara baega abinci ba a ranta tace "oh Lord what could be on earth happing to this man"
Da sauri ta nufesa ya daga mata Hannu hakan bae sa tayi shiru ba ganin zata masa mgn ne ya saka shi zabga mata wata tsawar da ta saka hantar cikinta hautsinewa jijiyar Kansa da tayi rudu rudu da idonsa da suka sauya launi ya zuba mata yana bata kallon irin ki shiga hankalin ki kana ya wuce daki.
Gaba daya Atika ta tsorata da ganin yanda Sulaiman ya sauya yau din nan, haka ta koma ta zauna kallon na gaba daya ya fice mata a kae wani uban ya gumi ta zuba da bata San dalilin sa ba tun ranar da ya bama Afeefah kashin da yayi sanadiyyar kwanciyar ta asibiti ya sauya amma na yau yafi na sauran ranakun.
"Haba addah Afeefah dan Allah kiyi ki daena ruzga wannan uban kukan wlh zaki sakani kuka nima ga Ammi sae kuka takeyi kalli yanda jijiyan kanki ya tashi dan Allah kiyi hakuri haka nan"
Share hawayenta tayi da Bayan hannunta tace"toh Hafsa nagode insha Allah zan rage"
Tace "yauwa adda Afeefah Koke fa ki cigaba da addu'a kawae Allah zae kawo mafita"
Smiliny tayi mata kawae a ranta tana cewa "mafita dayace shine bani takardata da sulaiman zaeyi"
_______________•••*SUBSCRIBE ON MY YOUTUBE CHANNEL DAN SAMUN VIDEO DIN ABINCI, KWALLIYA DA SAURAN SU*
____________•••
Vote
Comment
Share
YOU ARE READING
Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ
RomanceBana gaya miki bana son haihuwa ba wlh saena zubar da wannan cikin naki dan a tsari na haihuwa ki shirya karbar magani" "Wlh baka isa ka sakani zubar da kyautar da Allah ya bani ba Sulaiman kayi duk abunda zakayi" "Kayi hakuri Sulaiman bazan iya kom...