Page 13
Cire hijab dina nayi tare da kallon Waheedah nace "ke mai ya hadaki da matar nan"
Tabe baki tayi tace "shigowa tayi ta tarar Ina girki shine fa ta shiga kitchen din ya bude mun tukunya dana mata magana tane mi karanta min shit shi yasa na taka mata birki amma Adda haka take miki idan kina girki?" Girgiza kai nayi nace mata "aa inaga yau na dan tasan bana nan ne shiyasa" tabe baki Waheedah tayi tace "uhmmm gulma kawai bari na zubo mana abincin sai muci a nan kawai" nace "toh Husna bita kizo mana da ruwa akwai kunun aya a freezer ki dakko mun ku kuma 'yan gayu nasan bashan irin wnn kuke ba akwai drinks ku dauka" dariya Husna tayi tace"kai Adda Allah muna sha" nace "a toh Ina na sani". Bayan mun gama cin abinci na shiga dakina dama already nayi sallah a skl kayan jikina na cire na kwanta ba jimawa bacci ya tafi dani dan na gaji sosai yau. Ban farka ba sai pass 4 da sauri na sakko ganin time ya tafi toilet na shiga duk Ina so nayi wanka ban tsaya yinsa sbd time alwala kawai nayi na fito, Bayan na idar na shiga nayi wanka ma shirya cikin wani material red and black na saka takalmina flat shoe red dan bana son hills vail dina Mai three in one na saka duk da ba wani kwalliya nayi ba nayi kyau abuna handbag dina na dauka na fita, dakin su Waheedah naje na tarar sun shirya suna zaune da alama ni suke jira kallon su nayi duk sun cakale abun su suk da suma ba kwalliya sukayi ba gwanda ma Waheedah ta saka nude lipstick kuka tayi kyau vails dinsu R&S ne kallon su nayi nace "lallai yaran nan baza ku daina saka irin wadannan vails din ba ko laifin mommy ne na da ta barku" turo baki sukayi Waheedah tace "kai Adda dan Allah Meye laifin wannan vail din so kike mu fito kamar wasu matan aure" girgiza kai kawai nayi nace "Allah ya shirya ku mu tafi" dariya kawai sukayi muka fita Waheedah ce tayi driving din mu zuwa gida. Abu kamar hadin baki gidan ya cika duk su Adda Maryam sunzo ya Ashir ma da matarsa suna gidan gida ya cika Abba ma na nan gaidasa mukayi muka fito zuwa part din mama dan ita kadai ce bata parlourn, Kamar yanda ta Saba amsa gaisuwarta ba yabo ba fallasa haka ma ta mana yau, part din Abba muka koma nan aka baje ana ta fira da barkwanci kallon Waheedah Abba yayi yace "Wahee zonan" mikewa tayi ta isa gurinsa ta zauna yace "ya kika jiki acikin yan uwanki yau" smiling tayi tace "abbana baki na ma bazai iya fada ba Allah naji dadi sosae sai nake ji ma kamar na dawo cikin ku" dariya sukayi gaba daya Abba yace "ai da nan da can duk daya ne Waheedah Allah dai ya maku albarka ya Kara hada min kanku" suka amsa da Ameen Adda Maryam tace "amma yau gidana zaki kwana ko" da sauri nace "Haba Adda kidai bari sai gobe yau so nake tamin snacks" Adda Maryam tace "toh naki wayon" mararaicewa nayi nace "Haba Adda" tace "toh naji gobe zanzo na dauke ta da kaina" nace "Yauwa" Ya Ashir yace "nikam kun Ware ni" dariya sukayi Waheedah ta koma kusa dashi ta rada masa magana a kunne dariya muka ga sunyi harda tapawa Adda Maryam tace "gulmammu" ya Ashir yace "Ba komai" ya Adam yace "toh ni yaushe zaki je gidan nawa" tace "karka damu yah zanzo ba dai Ina nan ba" Adda hadeexa tace "nikam ko magana bazanyi ba tunda naga ita Waheedahn ko time dina bata da" zaro ido tayi tace "kai Adda hadeey ai kin San bama haka dake kin manta ni dake 5&6 ne" dariya sukayi yah ukasha yace "ni dai banda gida amma zanzo na dauke ki muje tawon gari "rungumesa tayi tace "thanks bro" Falmata ta tabe baki tace "hmmm mu da ake gani kullum ba Mai neman mu gidan sa sai aiki ya tashi toh ba gidan wacca zan kara zuwa yasin" dariya mukayi gaba daya nace "kai Twinie don't be jealous" tace "ba wani jealously nan na cewa yah ukasha dan Allah ya kaini Azbir amma yace bashi da time fita zaiyi" caraf yaran gidan suka fara mita Abba yace "nikam ba ruwa a tsakanin ku ne" dariya kawai muka dinga yi" sai Bayan isha muka koma gida cike da kewar yan gidan mu, yau ma sulaiman ba part dina zai kwana ba hakan yasa muka zage muka fara aikin snacks dinmu dan gobe Banda lectures sai 4.Bayan kwana biyu aka fara biki sosae abun ya kayatar dan iyayen amarya sunyi kokari sosae ranar saturday aka dauka aure aka kai amarya dakin ta. Bayan kwana biyu da gama biki dai ga mommy da ya Fu'ad sosae naji dadin ganin su barin ma mommy da rabona da ita tun aurena Bayan mun gaisa na kawo masu snacks da drinks komai yah fu'ad bai taba ba ya mike yace "mommy idan kin tashi tafiya sai ki kirani zan fita" tace "toh" kallon sa nayi nace "yah bazaka tsaya ko ruwa kasha ba" ko jiyowa bai ba yace "am okay" daga haka ya fita fira mukayi sosae da mommy kafin da yamma yah fu'ad yazo daukan ya Leda na samu na zuba masa snacks din na kai masa mota Mommy Kuma wata lifaya da turare masu tsada na oil na bata sai addu'a take saka mun kamar na bita nake ji harda hawayena.
*Few days back*🦋
Lokacin azumi sai karatowa yake yi duk wani siyayya da zanyi na gama sbd sulaiman ya bamu kudin siyayyar azumi bana so sai lokaci ya Kure naje kasuwa saboda cinkoson mutane. A yau nake expecting ganin period dina amma Shiru hakan yasa nayi tunanin ko zai fara mun wasa ne, har aka fara azumi ban gani ba ni kuwa nan kawo tunanin komai ba a raina. Ina kwance cikin daki naji amai yazo mun da sauri na mike na shiga toilet haka na dinga kwararasa kamar zan fitar da yan cikina sosae na galabaita dama gashi azumin yau ya bani wahala kitchen na koma na dauko ruwan sanyi nasha, kamshin girkin da na dora ya daki hancina ji nayi cikina ya hautsine min da gudu na fada toilet din parlour sai amai kuma sosae hankalina ya tashi dakyar na koma daki dan bana son kamshin girkin ko kadan wayana na ciro na Kira Aunty nace ta turo mun Faty ta tayani aiki tace toh ba jimawa sai gata tazo, sosai ta tauyasa mun nan ta tambayeni aikin me zata mun na fada mata abubuwan da zata hada dan yau a nan sulaiman zai sha ruwa, sosai ta gama hada komai ta jera. Gab da kiran sallah Sulaiman ya shigo ruwan wanka na hada masa ya shiga ya fito ya shirya, nan fada masa abunda ya faru ba muka fito parlour gaba daya muka sha ruwa ya fita sallah.
Kallo na Faty tayi tace "wai meke damun ki ne" nace "Allah Faty warin abuncin ne bana so ya turaren da sulaiman ya saka gaba daya ya hautsine min ciki" kallona tayi na 10seconds tace "when last kikayi period" nace mata "last month" tace "this month fa" nace mata "baizo ba" shiru tayi can tace "hmmm Kamar fa cikine dake dan duk alamu sun nuna" zaro ido nayi gabana na faduwa nace "ciki?" Tace "ras kuwa cikine dake Afeefah" sosai na shiga tashin hankali ganin kamar Faty zata gano tashin hankalin da nashiga saina waske nace "alhmdllh" koda sulaiman ya dawo ban masa mgn ba na daure na zuba masa abinci yaci sai fira suka da Faty Bayan sallah isha ya maidata gida. Fada maku tashin hankalin dana shiga ma bata lokaci ne tunani barkatai na dingayi daga karshe na mike zuwa sallah sosae nayi addu'a akan cikin nan nawa nasan ba karamin tashin hankali zan shiga ba idan sulaiman yaji wannan labari........
••••••••••••🦋
Shiru Adda Maryam tayi tana tunani sosae tsanar Sulaiman ta dirku acikin zuciyarta wani iska ta fesar ta mike zuwa sallahr magrib da ake kira da tunani barkatai cikin ranta tunanin take shi kuma wannan cikin Ko sulaiman zai San dashi? Idan ya gani Afeefah na dauke da ciki wane mataki zai dauka zubarwa zaiyi ko kuwa? da wannan tunanin ta shiga toilet tayi alwala ta fito Bayan ta gama sallah ta fita kichen dan nema masu abunda zasu ci ita da yara.
*Tho readers ku bana Adda Maryam answer questions dinta* 😂😂
____________________________
*Dedicated to Hassan Atk with love ❤️*
____________________________#TeamAfeefah
#TeamSulaimanVote
Comment
Share*Lioness*👑

YOU ARE READING
Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ
Lãng mạnBana gaya miki bana son haihuwa ba wlh saena zubar da wannan cikin naki dan a tsari na haihuwa ki shirya karbar magani" "Wlh baka isa ka sakani zubar da kyautar da Allah ya bani ba Sulaiman kayi duk abunda zakayi" "Kayi hakuri Sulaiman bazan iya kom...