*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_Written by *NEESHAR.JAY*
*NEESHEJAY* @wattpad
Page 19
*My Instagram and Snapchat was acting weird the other day and obviously didn't post my status, but I just wanted to say thank you so much to everyone who wished me a happy birthday! I got to celebrate this week with my amazing friends and awesome family! I am so blessed and couldn't ask for more.
I thank each and every one of you for your lovely birthday wishes and for loving me. All of your wishes and blessings mean a lot to me! Sorry, I was busy so I wasn't able to reply all the messages from my friends and some close ones. I hope you guys don't mind. I thank my besties for being around me. I love you guys for making my birthday such a wonderful and a memorable day of my life. Thanks for making me feel special and for being a special part of my life. Love you all, I so feel humble! Stay blessed. I'm sure that with all these wishes, it will become a great year.*#Disaster🦋
Bashi ya farka ba sai da akayi sallah la'asar kana ya tashi ya a hankali ya zuro kafafunsa kasa tareda mikewa ya shiga toilet alwala yayi ya fito masjid ya wuce Bayan an idar da sallah kuma ya dawo cikin gida abinci kawai yaci bai jima ba ya fita.
_______________
*AFEEFAH*🦋
_______________"Allah bana son karya Waheedah" dariya tayi tace "kai Adda na saba maki karya ne da gaske jibi zamu zo amma one week zamuyi mu koma" numfashi ta fesar tace "what of your lectures?" Waheedah tace "ni dai na gama test amma ban sani ba ko Farouk ba zai zo ba yet bamuyi magana dashi ba dan he isn't yet back" tace "ok Allah kawo ku Lpy ki gaida mommy" tace "zata ji" daga haka sukayi sallama.
Kiran Sulaiman ne ya shigo wayarta a duk lokacin data tunasa sai taji wani haushin sa da zafin sa suna taso mata gaba daya yanzu komai sunan bata din gani shi yasa take gode ma Allah daya saka gidan su ba Mai irin sunan sa. Tana gani har call din ya yanke bata daga sai ma kashe wayar da tayi tare da mikewa ta fice dakin, dakin Aunty ta shiga dan taji kukan Ammi ashe ma Kayane ake chanza mata shine take ta tsawa ihu kamar wacca ake cirewa rai, girgiza kai kawai Afeefah tayi ta fice daga dakin.
_____________
Adda Maryam
_____________Adda Maryam kam yau taci gurin sai ta gama karanta diary din nan gaba daya saboda abun ya tsaya mata arai kawai so take taga karshen sa dan tasan matakin da zata dauka kuma taci alwashin zuwa ta fada ma abban su halin da ake ciki koda hankalin sa zai kwanta hakan yasa ta yanke hukunci karasa karanta diary din gaba daya coux tomorrow is Friday and tasan almost everyone will be present so is better ta sanar da kowa abunda yar uwar tasu ke boye masu.
Jawo book din tayi Bayan sun gama cin abinci ita su waleedah dama yau Thursday suka fita wasa compound din gidan.________
*Diary*Kamar yanda Sulaiman yace Bayan sati biyu mommy ta saka ya fu'ad ya mana booking flight acewarta bazan tafi by road ba saboda cikin jikina sosai naji kunya shi kuma baice komai sai kallona da yayi ya dauke kai tare da mikewa ya fita, ranar friday Bayan an gama sallah muka wuce airport coux flight din by 2:45 zai tashi sosai naji kewar su Waheedah harda dan guntun hawayen ta.
A nawa bangaren kuma fargaba da tsorone suka haduwa suka min yawa kamar kar mu shiga jirkin damuwa ta bayyana karara a fuskana I couldn't imagine what will happen if Sulaiman finds out about my pregnancy I just hope what ever the situation may be kar nayi kasa a gwiwa da tarin damuwa da yawa a raina flight dinmu yayi landing.
Sulaiman ne yazo daukan mu gaba daya sosai ya nuna farin cikin dawowana nikam sai yake kawai nake yi ko hugging dina daya so yi kin yarda nayi saboda cikina ya fara fitowa.
Ya fu'ad dake ta faman daure fuska muka fara sauyewa gida duk da ba kwana zaiyi ba zaibi flight dinne ya koma amma da yake sai 5:15 hakan yasa ya wuce gida dan ya huta godiya na masa sosai duk da bai amsa ba muka wuce.
•••••••••••🦋
Bayan kwana biyu labari na ya fara chanza wa tunda sulaiman ya gano Ina da ciki muka je hosptal akace masa ai cikin yayi 4 month a jikina yace "dr plss is there any possibility da za'a zubar da cikin" sosai gaba na ya fadi da sauri na mike na fice daga office din da kallon suka bini dr yace "no mr sai dai kayi hakuri harta haifesa kawai" bacin rai karara a fuskar sa muka koma gida saboda ba wanda yayi wa dan uwansa magana har muka isa.
Da sauri na fice daga motar hakan yasa yabi bayana ko tsayawa kashe motar baiba Ina saka kafa na cikin parlour yana shigowa da duk karfin da Allah ya basa ya fisgoni na dawo baya ban Ankara ba sai saukar Mari dana ji sosai ya shiga jikina saboda har da wata yar zabura nayi duk na ya fara yi ta ko'ina tun Ina iya ihu har ya daina fitowa sai da ya gaji dan kansa ya fice fuuuuu kamar zaki nayi kuka da tare da nadamar auren Sulamin duk soyayyar da nake masa ta rikide lokaci daya ta koma zallar kiyayya ga wani irin zafi da zuciya ta ke min ga cikina dake murdamin kamar me har aka kira sallar azahar ina kwance a gurin kamar mara rai dakyar nake iya motsa yatsan kafana da rarrafe na shiga daki nayi kusan 30mins kafin na samu dakyar na shiga toilet nayi wanka da ruwa masu zafi na daura alwala na fito. A zaune nayi sallah Bayan na idar na mike dan na dan ji dadin jikina Bayan nayi wanka da ruwa zafin paracetamol nasha na kwanta take baccin wahala ya tafi dani..........
*manage zuwa dare insha Allah za maku posting dayan page din*
_For those asking of this book daga farko dn Allah ku duba wattpad shi yasa na saka username dina #neeshejay plss zaku samu daga farko_
____________________________
*Dedicated to Hassan Atk with love ❤️*
____________________________#TeamAfeefah
#TeamSulaimanVote
Comment
Share*Lioness👑*
YOU ARE READING
Ꮋᴀᴋᴀ Nᴀᴡᴀ Ꮇɪᴊɪɴ Yᴀᴋᴇ
Любовные романыBana gaya miki bana son haihuwa ba wlh saena zubar da wannan cikin naki dan a tsari na haihuwa ki shirya karbar magani" "Wlh baka isa ka sakani zubar da kyautar da Allah ya bani ba Sulaiman kayi duk abunda zakayi" "Kayi hakuri Sulaiman bazan iya kom...