3&4

443 32 1
                                    

👠👠👠
      👠
👜👜👜
      👜
*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*
( _A hanyar lamba_)
_15/6/2020_
👠👠👠
         👠
👜👜👜
     👜

*Written* by _Ameera_ _Adam_ { _Mom_ _Aslam_ }
    
    📚 *HADAKA*📚
   📝 *WRITER'S*📝
🖊️ *ASSOCIATION* 🖊️
_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼
@: *Facebook*
_HADAKA_ _WRITER'S_ _ASSOCIATION_

@: *wattpad*
_AmeeraAdam60_

*SADAUKARWA* *GA* *DUK* *MASOYA* *NA* 😊🤝🏻
_Wannan_ _labarin_ _kirkirarre_ _ne_ _banyi_ _shi_ _dan_ _wani/wata_ _ba._

       3&4
*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*

Subhanallahi nikam me nake gani ni jikar indo, yau ni ce da gudawa a zani, " aykuwa naga ta kaina, " hjy iya ke sallalallami lokacin da takai bakin kofar toilet, " jin cikinta ya kuma hautsinewa da sauri ta banka kofar toilet ta shige.

*BAYAN* *WANI* *LOKACI*

Hajiya iya ce kwance akan carpet magashiyan, jikinta duk ya mutu ba kwari, " cikinta ne yake yamutsawa amma karfin jikinta ya kusa karewa, a hankali ta tashi zaune da rarrafe ta karasa toilet din, "zuwa wani lokaci ta fito da kyar take tafiya tana dafa bango har ta fito babban falon ta, cikin kasalalliyar murya take kwalawa inna zainabu kira, " zainabu  🗣️zainabu magana fa nakeyi hansai wai duk ba me ji na, "sai kace masu baccin mutuwa suwaiba suwaiba🗣️ wai duk babu me ji na ne?

Audi me gadi ya fito daga bandaki sama sama yakejin muryar hjy iya tana magana da hanzari ya karasa falon ganin hjy iya daga ita sai riga da dan tofi yasa shi saurin juyawa, a hankali hjy iya ta kirashi,  "Audi jeka kiramun zainabu kace ta xo yanxu, to hjy amma ina fatan lafiya dai ko, dan na lura kamar akwai abunda yake damunki, " Audi nace ka kiramun zainabu, hjy iya ta fada a kufule, to ayi hakuri hajiya, yana gama maganar ya fita da sauri.

*BA'A* *DAUKI* *LOKACI* *BA*

sai ga inna zainabu da Audi me gadi sun shigo da sauri, hajiya iya ance kina nema na Allah sa dai lfy, kafin hjy iya tayi magana audi ya karbe hjy iya zan iya tafiya ko akwai abunda zan taimaka muku dashi dan naga kamar kina bukatar taimako? Audi  ka kwana anan kaji, idan akwai abinda zakamun zance maka ka kiramun zainabu ne, dauko shinfida ka kwanta idan muka gama abunda zamuyi sai ka tafi sakaran banza sakaran wofi wuce ka bamu guri, "sum sum sum sum Audi ya wuce be kara magana ba.

Zainabu wlh cikina ne ya lalace tun dazu naketa bayan gida har saida na bata kaya na, matso indafa ki mu je ciki ki gyara gurin dan karfina duk yayi kasa, "zainabu cikin zuciyarta take fadin inbanda rigimarki hjy kinci alala ta sakar miki ciki  kuma kin matsa amiki lemon tsamiya ba dole ciki ya lalace ba idan anyi mgn kuma cibi ya zama kari..........

zainabu wuce muje cikina na motsamun kinyi kikam kamar gunki, hjy iya ta fada cikin fada, "to hjy kuma kinsha magani kuwa? Zainabu wannan jawabin sai na fito kyayimun shi, inna zainabu kama hannunta tayi suka wuce ciki.

Inna Zainabu ba ita ta gama gyara dakin hjy iya ba sai kimanin karfe 1:30am lokacin hjy iya har ta samu ta kwanta, gudawar tayi sauki sakamakon maganin da tasha.

Hjy iya nagama zan iya tafiya? Eh zainabu jeki Allah yayi albarka amma karki tasheni da asuba jikina duk ba dadi bazan iya azumi ba, to shikenan hjy iya Allah ya tashemu lfy, 'Aameen ki jamun kofa iya ta bata amsa.

*WASHEGARI*
Kimamin karfe tara na safe hjy iya na kishingide a falonta tana jin radio, karar bude get taji daga baya ta ji shigowar mota, "ba'a dauki lokaci ba taji sallamarsa cikin falon, "barka da safiya hjy iya da fatan kuntashi lfy? Cikin girmamawa habibu ya tsugunna yana gaida mahaifiyarsa.

Lafiya klau muka tashi habibu ni ce ma banji dadi ba jiya da daddare cikina ya dan baci amma da sauki dan yau ma ban iya daukan azumi ba, subhanallah hjy iya me kika ci hk me yaran nan suka girka jiya? A'a ba wani sabon abu suka dafa ba kasan larura idan Allah ya kawo basai kaci wani abun ba, " to ko zamu je asibiti kinsan gudawa cin karfin mutum take inyaso sai su dubaki su rubuta miki magunguna, " haba habibu gudawar ce sai munje asibiti nasha magani kuma ta tsaya.

To shikenan Allah kara afuwa amma zan wa su inna zainabu magana su dinga lura da abunda zasu dinga girkawa, "sallamar Audi me gadi ce ta katse su falon ya shigo hannunsa dauke da babbar leda, "agaban hjy iya ya ajiye ya juya ya fita, "yauwa hjy iya ga kayanku fa'iza da ciwon kai ta tashi amma tace agaya miki cikin satin nan zata zo, "to madalla ashe kaya sun iso, Allah sarki  yanxu nake shirin ma tambayarta ashe batajin dadi Allah ya sawake yasa kaffara.

Hjy iya ce keta fito da kaya cikin farin ciki kayanta ta fara ware wa agefe sannan ta ware nasu inna zainabu, ta gama ware kayan kenan Audi ya kara shigo da wata katuwar ledar, " ya ajiyeta gaban hjy iya, "Audi maza jeka kirawomun su zainbu kace dukkansu inasan ganinku Auwalu (Driver) ma kace yazo ku taho tare, Audi washe baki ya farayi  😃  cikin murna yace angama hjy iya ya juya da sauri ya fita.

*BA'ADAUKI* *LOKACI* *BA*

Gaba daya yan aikin gidan suka hallara afalon hjy iya, "kowannen su cikin farin ciki yake, murnanr su taki boyiwa.

Cikin dan lokaci hjy iya ta raba musu kowanne kayansa set biyu da takalmi su zainabu harda hijabai, " cikin farin ciki da girmamawa suka durkusa suna kwasar godiya harsai da Alh habibu ya dakatar dasu ya sallamesu kowa ya kama gabansa.

Habibu ina bukatar yan kudi, dan na hannuna bazasu isheni ba dan guraren da zani da yawa kuma kowanne naje zan musu hasafi. Hjy iya kudi ko nawa kike so zan baki amma dan Allah hjy iya ki hakura da wnn fitar na rokeki ba dan niba, idan  komai ya lafa na miki alkawari da kaina zan kaiki duk inda kike so. Kai habibu ka kiyayeni wai sa'arka na koma ko abokiyar wasanka, wai ma yaushe ka koyi ja'inja dani ne to ka fita ido na rufe inba haka ba ranka zai baci.

Hjy iya dan Allah kiyi hakuri ki fahimceni bada wata manufa na hanaki fita ba, wlh ko fita kukayi go slow ma kadai ya isheku, go slow yau na fara haduwa dashi kaga habibi idan zaka bani kudi kaban idan kuma bazaka bayar ba ka rike abunka zumuncin Allah dai bazaka hanani ba.

Ayi hakuri hajiya iya ga wannan, "ya karasa maganar yana zaro kudi a aljihu, " yan dubu-dubu ne na dubu dari da hamsin ya mika mata, "cikin farin ciki hjy iya ta karba tana murna. Nagode habibu Allah dada budi Allah shirya zuri'a, Allah yayi ma albarka, cikin jin dadin addu'ar mahaifiyarsa yake amsawa da Aameen.

*INA* *TARIHIN* *HJY* *IYA*?

Hadiza shi ne aynihin sunan hjy iya asalinsu yan kauyen kano ne cikin  wani kauye  me suna rigana dake cikin garin lambar kunci, "ita da mai gidanta marigayi mlm sani auren zumumci aka musu hjy iya su uku ne gurin iyayensu itace babba laraba take binta sai Auwalu "mlm sani ya rasu tun Alh habibu nada shekara biyar aduniya, shi kuma su biyar ne gun mahaifansu maza hudu sai mace daya itace autarsu

Mlm sani kasuwanci ne ya ke kawo shi kano ya koma daga baya ya dauko matarsa suka dawo kano inda suka zauna a unguwar bacirawa, sana'ar icce yakeyi a hakali Allah yasa mai albarka har ya fara janyo yan uwansa suma a hankali kowa ya nemi sa'ar da yakeyi    sannu a hankali suma suka dauko iyalansu.

Alh habibu shi kadaine dansu rayayye hjy iya ta haifi yara takwas duk mutuwa sukeyi sai akan habibu Allah ya bar mata kuma daga kansa bata kara haihuwa ba.

Hadiza (Hjy iya) mace ce me fadan gaske bata da daukan raini sai dai bata da riko, gata mace ce mai kyauta   ga san zumunci, hjy iya tasha wahala matuka bayan rasuwar mlm sani domin yan uwan mahaifinsa ba wanda yake taimaka mata, itace wankau sirfau dakau har sana'ar kosai da waina tayi dan ta samu habibu yayi karatu, ' ahaka har ya zama saurayi ya fara buga buga suna  rufawa kansu asiri dg nan hjy iya ta daina wahala sai dai ya fita ya nemo musu har Allah yasa ya kammala karatunsa ya sami aiki kuma yana hadawa da kasuwanci, " yayi aure, " yanada mata biyu da 'yaya goma sha uku, sai jikoki guda goma sha takwas.

Alh habibu yanaji da mahaifiyarsa matuka duk abunda zayi dan ya faranta mata yanayi iya kokarinsa, tunda dadewa ya bukaci hjy iya ta koma gidansa dake gyadi-gyadi fir taki wai batasan zama da sirikai ko unguwa daya bata bukatar su zauna, " shiyasa yasai mata katafaren gida a na'ibawa ya zuba mata yan aiki da me gadi da driver.

hjy iya tayi yan aiki sunfi a irga sbd fadanta kanayin abunda bai gamsheta ba zatasa
a sallameka inna zainabu ce suka shafe shekara da shekaru suna tare kasancewarta mace me hakurin gaske typin.....😉

_BACK_ _TO_ _LABARI_ ✍🏼

*Vote*
*Comments*
*Share* 😎

YAWON SALLR HJY IYA CompleteWhere stories live. Discover now