47-48

76 17 3
                                    

👠👠
*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*
( _A hanyar lamba_) 👜👜
       _17/8/2020_

*Written by*:- _Ameera Adam_
    _AmeeraAdam60_
*@wattpad*

*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼

*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*

                47&48

_ku karbeshi a haka ba editing_

Suna tafe a mota tanimu sai kwala ihu yake cikin kururuwa yana neman agaji, hawan su kan kwalta keda wuya ya kara kurma ihu cikin yekuwa yana bukatar ceto, daya daga cikin yan sandan ne ya buga masa tsawa cikin tsuke fuska yace, " kai rufe mana baki bamasan iskancin banza da wofi, jahilin banza kawai ni ban taba ganin dakikin likita ba sai kai, idan mukaje zakayi bayani, Allah ne ya rufa asiri da tuni ka kashe mutanen garinku wasu kuma ka nakasasu "

Tanimu tsit yayi kamar ruwa ya cinye Shi, banda zare idanu ba abinda yakeyi bai taba dana sani arayuwarsa ba sai yau, tuno zamansa yayi abirni lokacin da suka taho shi da kansilan kauyensu da zimmar yayi karatun likitanci amma yasa san zuciya wanda gashi ya kaishi ga nadama.

Tafiya suke sosai ba wanda yake cewa  wani uffan sannu a hankali har suka iso cikin garin kano, sun danyi tafiya me nisa suka karasa police station din sharada.

     Keyar tanimu aka tasa cikin cell, DPO ne ya fito suka kara gaisawa da Alh habibu, tanimu ne ya ziro kai jikin window ya fara rokon Alh habibu, " Dan Alh ka taimaka mun wallahi na tuba bazan kuma ba zanyi muku bayanin duk abunda ya faru dani lokacin da naxo birni, amma dan Allah kumin rai karku kaini gaba wallahi ko kaza bazan kara bawa wani abu ba da sunan magani.

    Bayan Alh sun gama gaisawa da DPO sawa yayi aka fito da tanimu, tanimu ne zaune a kasa duk yayi wuri-wuri kamar wanda yayi jinyar shekara, DPO ne ya buga mai tsawa yana tambayarsa.
" kai, wanene kai meye matsayin karatunka a ina ka samu shaidar aikin likitanci, duk munaso muji daga gareka "

    Gyara zama tanimu yayi sannan yace,  " ni dai suna tanimu dahiru ni dan asalin garin gangaren hayi ne, mahaifina ya rasu tun ina karami, nayi makarantar arabi da boko, boko har primary na gama na shiga karamar sakandire, garin mu basu wani maida hankali akan karatun boko ba shiyasa ma bamu da wasu wayayyun yan boko, nima sai inshafe wata guda banje ba makarantar kuwa dama wani lokacin da kayan gida muke zuwa, alokacin da muka shiga aji biyu akaramar sakandire sai wani kansilan mu yayi shela yace,  karshen waccen shekarar da muke ciki zaisa ayi jarrabawa a makarantar mu wacce tayi dai-dai da kammala waec, amma bamu zaiyi wa ba yan babbar sakandire aji uku zaisa ayiwa, yayi alkawarin zai zabi mutum uku, acikin duk wanda ya rubuta dai-dai ya dauki nauyin karatunsu, mutum na farko shi zai karanci bangaren lafiya, na biyu ya karanci fannin tsaro na ukun kuma ya karanci bangaren koyarwa, haka akayi jarrabawa lokacin da kansilan mu ya bukaci abashi sunan wadanda sukaci jarrabawa sai aka sa suna na nine na faro, da wadansu mutum biyu hadi da nura, kanin mahaifiyata shi ne principal din makarantar kansancewar haka ne yasa mahaifiyata ta rokeshi alfarma akan yasa sunana, sun dan kai ruwa rana kafin ya amince daga baya kuma ya karbi bukatarta "

    Numfasawa tanimu yayi, Alh habibu yace " muna jinka cigaba da bayani "

     Tanimu yace,  "  akareshen shekarar gaba sai kansilanmu  ya taho damu birni ya kama mana wani shago a unguwar karkasara, duk wannan zancen da nake muku alokacin shekara ta goma sha takwas sauran abokan da mukazo dasu sun girmemun daga me ashirin da hudu sai me ashirin da biyar, mun samu wata biyu da zuwa wata rana yanka shi dade yace na shirya da wuri zai kaini makaranta, hakan kuwa akayi yazo da wuri ya kaini wata babbar makaranta wacce ake kira sch of nursing acikin Asibitin Aminu kano, duk abubuwan daya kamata yayi mun shi abunda yace mun yayi shige da fice akan komai ba abinda zanyi sai fara lecture itama idan lokacin yayi zai  gaya mun, ni dai ba baka sai inbishi da idanu babban farin ciki na da yace mun ba abinda zanyi sai zaman karatu, kanta kalmar lecture da ya bata ban ganeta ba sai da nayi wani dogon nazari sannan nafihimci inda ta dosa "

YAWON SALLR HJY IYA CompleteWhere stories live. Discover now