17&18

112 10 0
                                    

👠👠👠
      👠
👜👜👜
      👜
*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*
( _A hanyar lamba_)
_23/6/2020_
👠👠👠
         👠
👜👜👜
     👜

*Written* by _Ameera_ _Adam_ { _Mom_ _Aslam_ }
    
    📚 *HADAKA*📚
   📝 *WRITER'S*📝
🖊️ *ASSOCIATION* 🖊️
_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼
@: *Facebook*
_HADAKA_ _WRITER'S_ _ASSOCIATION_

@: *wattpad*
_AmeeraAdam60_

*SADAUKARWA* *GA* *DUK* *MASOYA* *NA* 😊🤝🏻
_Wannan_ _labarin_ _kirkirarre_ _ne_ _banyi_ _shi_ _dan_ _wani/wata_ _ba._

       15&16
*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*

Gudu suma suka sa lokaci daya suka rufawa baba tsoho me buhu baya, gudu ya zage yakeyi iya karfinsa amma saboda yanayin girma ga tsufa lokaci guda suka cin masa.

A tsakiya suka saka shi suna kokarin rike hannuwan sa, dan tsoho yayi wani kukan kura cikin karaji irin yanda jariman india sukeyi idan suka fusata, yasa gwiwar hannuwan sa ya kai musu duka yana fadin, " wallahi bansan da makiya nake tafe ba sai yanxu idan kuka maidani cikin motar nan ban yafe muku ba.

Ku sake ni na karasa bichi a kafa, idan kuka kaini mota wallahi alhakin mutuwata a wuyanku yake, cikin hanzari suka kara matsowa zasu kama dan tsoho, aykuwa ya yi sauri ya matsa baya hadi da buga kafa daya, ya kara kwalla kara yana fadin, " yeeeeeeeee ku matsaaaaaaaa ko in ma ke kuuuuuuu, ya karasa fada yana dunkule hannuwa har huci yake.

      Daya daga cikinsu ya kallin dayen yace,  " wai kuwa Anya bazamu kyale tsohon nan ba yaje yayi ta tafiyarsa, tunda anasan ceton rayuwarsa yana san yayiwa mutane illa, kana ganin yanda ya kaimun duka a gefen fuska badan na kauce ba da ya gwabjeni yayi mun mahangurba,     " kai haba yanxu tsohon nan ne zai gagaremu, idan aka ce mun kasa kamo shi ba muji kunya ba dan Allah rabu dashi bari kaga muma karfi zamu nuna masa, muna zuwa ciccibarsa zamuyi farat daya  zamuyi masa.

     Aykuwa suka tunkari dan tsoho me buhu, yana ganin sunyo kansa gadan-gadan ya fara kai duka ta ko ina, yana yi yana ja baya sai kuma yayo gaba kamar zai doko wani daga cikin su, yan da kasan yana filin danbe.

Basu bi ta kansa ba, sukub haka suka sun kuci dan tsoho suka mammakure hannusa a hammatarsu sai wutsul-wutsul yake da kafafuwa, yanayi yana wani karaji shi bai yarda ba dole kwacewa zaiyi daga hannunsu.

Bakin motar suka karaso suna kokarin saka dan tsoho sai fisgewa yake yana ciccijewa har suka samu suka tura shi ciki, wani daga gefe ya dan leko su yana fadin,  " to ita ma iya ku sata aciki man, kunga kun huta, idan fa kukayi sake tsohon nan ya kubce wallahi dawa zai shiga, dan na lura motar nan ta tsora tasu dayawa,  juyawa sukayi zasu dauko hjy iya, bayan sun rufe kofar motar, Aykuwa dan tsoho ya Duba, ya waiga yaga duk basa kallansa, ya zura kafafuwan sa ta window.

Gurin hjy iya suka koma da zummar su dauko ta aykuwa ta rike kafar wani saurayi dake kusa da ita, duk tabi ta kadandane shi, masu daukan hjy iya sun yunkura zasu ciccibeta aykuwa suka taho da saurayin nan, saura kadan su zube kasa gaba dayansu, da hanzari suka maida hjy iya kowannensu ya cika ya kule dan takaici, " daya daga cikin ne yayi magana.

        " wai dan Allah tsofaffun nan ya suke so muyi dasu ne kowanne ana san taimaka masa amma baya gani, nifa na gaji wallahi yau ko su suka haifeni sai haka, nifa bari ingaya muku gaskiya wlh idan mota taxo ko a booth ne shiga zanyi ta wuce dani wannan wacce irin masifa ce haka, dame zamu ji da lalacewar mota koda hadarin da yake ta haduwa ko kuma da wadannan tsofaffun................. Wani daga gefe shima ya karbe, wlh ina bayanka abokina ko tafiya mukayi muka bar tsofaffunan Allah bazai tambaye mu ba tunda iya hakki mun fita hakkinsu, banda ma zuciyar musulci kana ganin dattijuwar nan yanda tasa aka caje mu wai mun daukar mata waya,  hmmm wallahi dandai taimako nada amfani kuma ina duba darajar tsufansu, da tuni ban sabi hanya ba inyaso idan naje cikin garin, wallahi ko a rumfar me shayi zan iya kwana , Allah na tuba dan yan awanni da zan karasa ko a tsaye bana tsaya gari ya waye ba.

YAWON SALLR HJY IYA CompleteTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang