👠👠
*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*
( _A hanyar lamba_) 👜👜
_9/8/2020_*Written by*:- _Ameera Adam_
_AmeeraAdam60_
*@wattpad**HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*
45&46
_Kuyi hakuri da yanda kuka sameshi wlh nayi kusan rabi ya goge_😒
Murmushi jin dadi hjy iya tayi sannan tace, " Allah yayi maka albarka habibu sharrin makiya da mahassada Allah ya kare "
" Allahumma Aameen hjy iya ta, idan kin gama anjima sai amun magana, bari nasa aturo miki su inna zainabu" Alh habibu ya fad'a.
Be jima da fita ba sai ga su suwaiba sun shigo falon, da murna sukayi gurin hjy iya cikin so da kauna suna mata murna da zuwa, ita dinma tayi kewarsu cikin sakin fuska take tambayarsu ya yanayin zaman da suke, sun dan tab'a hira sannan suka tashi sukayi sashen su suna murna zasu koma cen gidan hjy iya.
Bayan magriba kuwa Alh habibu da kansa ya da kwashe su gaba daya iyalan gidan hjy iya, su Audi sai yashe baki suke dama gaba daya atakure suke, bayan ya kai hjy iya gida har zai tafi ya koma ya karbo address din garin da zashi washe gari, sallama yayi mata yasa kai ya fice yana kewar hjy iya.
Su suwaiba murna harda tsalle dama gaba daya zaman cen bai musu dadi ba, saboda aikin gidan yawa gareshi ba kamar na hjy iya ba, ita matsalar hjy iya mita da sa aiki amma duk da haka sunfi san gidan hjy iya.
_Washegari_
Alh habibu ne ya shirya tsab cikin wata dakakkiyar shadda ya fito harabar gidan, su sarari yasa aka kirawo masa mota yace su shiga ba musu suka shiga shima ya shiga ya take ta suka fice daga gidan.
Kai tsaye sharada ya wuce gurin DPO , bayan sun gaisa Alh habibu ya bawa DPO labarin duk abinda hjy iya ta gaya masa da kuma address din garin.
Yarasan ya kira masu farin kaya guda biyu ya hadashi dasu kowannen su tsuke yake cikin riga da wando ba wanda zai ce yan sanda ne,, sannan aka hadasu da motar police daya duk irin plan din da zasuyiwa dafta tanimu sun shirya tsab sallama sukayiwa DPO suka dauki hanya.
Suna tafe sannu ahankali sarari yake kwatantawa Alh habibu layin su, motarsu ce ta kutsa kai cikin unguwar miltara, akofar gidan su sarari sukayi parking Alh habibu yasa akayi masa sallama da maifin sarari, bayan ya fito gaisawa sukayi da Alh habibu cikin mutumci, sarari ne ya sunkuya har kasa yana gaida mahaifinsa, da sakin fuska mahaifin nasa ya amsa duk atunaninsa yaron Alh ne yake gaisheshi.
Sai da sarari ya d'ago da kansa mahaifinsa na ganinsa ya fara danna masa ashar, sarari sam baiji dadin abunda mahaifinsa yayi masa ba duk da yasan shine musababbun duk abunda yayi masa, katse shi mahaifin nashi yayi cikin zagi yace, " kai bana koreka daga gidana ba ka dawo ne ka kasheni da bakin cikinka ka cuci sauran 'ya'yana da yan uwana, ka manta me nace maka ko, ba ce maka nayi idan ka dawo mun gida ba sai na tsine maka ba, shashashan banza mara kan gado, uwarka tana nan tana zaryar asibiti saboda hawan jinin daka saka mata, ko ka dawo ne karasa ta itama, wallahi-wallahi tun muna shaida juna ka tashi ka barmun kofar gida, tunda bansan dame kazo ba wa ya sani ma ko zuwa kai da sigar mutanen kirki ku farmakemu ku halaka mu, zaka tashi ko sai na yimaka yekuwa anyi maka dukan tsiya " mlm muttaka ya karasa maganar yana niyyar kai wa sarari duka.
Da sauri sarari ya tashi yayi bayan Alh habibu ya 'buya yana zubda kwallah.
Alh habibu cikin laluma ya farayiwa mlm muttaka magana yace, " Dan Allah idan bazaka damu ba inasan mu shiga daga ciki, akwai maganar da nake san yi da kai, saboda nan naga mutane sun dan fara sa mana ido "

YOU ARE READING
YAWON SALLR HJY IYA Complete
Short StoryGudu yakeyi iya karfinsa amma saboda yanayin girma ga tsufa lokaci guda suka cin masa. A tsakiya suka saka shi suna kokarin rike hannuwan sa, dan tsoho yayi wani kukan kura cikin karaji irin yanda jariman india sukeyi idan suka fusata, yasa gwiwar h...