39-40

71 18 0
                                    

👠👠
*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*
( _A hanyar lamba_) 👜👜
       _25/7/2020_

*Written by*:- _Ameera Adam_
    _AmeeraAdam60_
*@wattpad*

*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼

*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*

                39&40

Hjy iya farat tayi ta karbe wayar daga hannun musa ta cigaba da yiwa habibu magana.

Alh habibu har rasa bakin magana yayi dan farin ciki da jin muryar hjy iya, cikin d'oki da murna yace, " hjy iya yanxu kina ina ne naxo na taho dake?" kwallar farin ciki hjy iya ta goge sannan tace, " muna wani dan kauye amma bari ga wanda muke gidan nasa ya gaya maka sunan garin da muke, habibu nayi kewarka dan Allah ka hanzarta kazo taho dani"

cikin kewar mahaifiyarsa yace, " hjy iya karki damu kinmanta habibunki ne, magana bazata yuwu ta waya ba bashi wuyar muji sunan garin insha Allahu baza'a dau lokaci ba zaki ganni"

wayar ta mik'awa musa, sallama ya yiwa Alh habibu bayan sun gaisa ya gaya masa sunan kauyen, godiya ya yi masa yace abawa hjy iya wayar.

     Dan tsoho ne yayi karaf ya karbi wayar da murmushi a fuskarsa ya fara magana, " D'ana habibu barka da safe yau kuma sai kaji muryar hadizatu to muna nan muna jiran isowarka, kai ammafa munsha karakaina........

Fisge wayar hjy iya tayi tana mita, ba tare da dan tsoho ya gama wayar ba, " magana ta cigaba da yiwa Alh habibu cikin farin ciki har suka kammala wayar.

Hjy iya bakinta har kunne, kowa ya ganta yasan tana cikin farin ciki, dan tsoho ne ya kalleta cikin marairaicewa yace, " yanzu hadizatu habibun ma bakya san mu gaisa dashi? Wai ni meye aibuna da ko kadan bana birgeki? Bakisan Abinda Allah ya boye ba, ba'a ja da hukuncin Allah.......
        Cikin jin haushi hjy iya ta katse shi, dan Allah ina cikin farin ciki karka sa raina ya baci, kai ni narasa irinka sai magana kamar ka hadiyi radio, Allah ya sawake maka"

Aameen kawai dan tsoho yace saboda ya lura da gaske hjy iya batayi dashi din, gefen bishiya ya koma ya zauna yana kallan su kowa da Abinda yake yi.

Lokacin da musa ya kira Alh habibu yana toilet yana wanka, shiyasa suka kirashi har sau biyu bai dauka ba sai ana uku wanda yayi daidai da fitowarsa daga wanka ya dauka.

Bayan sun gama waya da su hjy iya agurguje yasa kaya ko mai be shafa ba, fitowa yayi babban falo iyalan gidan duk suna zaune breakfast sukeyi.

Kana kallan fuskar Alh habibu kasan yana cikin matsanancin farin ciki bakinsa har yaki rufuwa, ganin yanayin daya fito yasa Auntyn yara ta fara tambayarsa.
          " Daddyn yara lafiya meyake faruwa na lura kana cikin farin ciki, ko wani albishir din akayi maka.........

Katse ta yayi da, " kwarai kuwa ban dade da samun albishir ba"

Mene ne albishir din, mami ta tambaya.

Wallahi dazun nan wani bawan Allah ne ya kirani wai hjy iya na gidansa.

Gaba daya falon ya rude da ihu saboda murna da farin ciki.

Kairat da khaleed ne sukayi farat suka ce, " dady dan Allah muje tare wallahi munyi missing din hjy iya"

Banasan fa bata lokaci, dan munyi waya da DPO zamu hadu da yaransa a hanya, Alh habibu ya fada yana kokarin fita.

Da sauri khairat ta mike tana fadin, " daddy wallahi ba abinda zanyi hijab dina kawai xan dauko nasan kafin ka tada mota ma na fito" ta karasa maganar tanayin part dinsu da gudu.

YAWON SALLR HJY IYA CompleteWhere stories live. Discover now