13&14

91 23 1
                                    

👠👠👠
      👠
👜👜👜
      👜
*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*
( _A hanyar lamba_)
_22/6/2020_
👠👠👠
         👠
👜👜👜
     👜

*Written* by _Ameera_ _Adam_ { _Mom_ _Aslam_ }
    
    📚 *HADAKA*📚
   📝 *WRITER'S*📝
🖊️ *ASSOCIATION* 🖊️
_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼
@: *Facebook*
_HADAKA_ _WRITER'S_ _ASSOCIATION_

@: *wattpad*
_AmeeraAdam60_

*SADAUKARWA* *GA* *DUK* *MASOYA* *NA* 😊🤝🏻
_Wannan_ _labarin_ _kirkirarre_ _ne_ _banyi_ _shi_ _dan_ _wani/wata_ _ba._

       13&14
*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*

Hayaki ne ya fara tirnike motar daga gaba gurin mazaunin driver, gaba daya suka dau salati masu ihu nayi masu addua nayi, cikin hanzari kwandasta ya bude murfin kofa suka fara fita, hjy iya dai sai wasu mutum biyu ne suka dauko ta dan gaba daya ta rude ta gigice idan kaganta ma bazakayi tsammanin tana cikin hankalin ta ba.

Itama dayar motar mutanen cikinta fitowa suka farayi, kowanne zuciyarsa fal fargaba.

Gefen titi suka koma suka bar kwandastoci da drivers kowannen su ya kunna fitila yana duba irin matsalar da motar sa ta samu.

    *A BANGAREN SU HJY IYA*

Tanacen an shinfitar da ita jikin wata bishiya tana sauke numfashi da kyar, sai jero Addua take ba kakkautawa, tana sakin wannan zata kama wata Addua harta shiga bandaki ta maimata ta yafi a irga.

     Allah cikin ikonsa babu wanda yaji mumman ciwo yawancin su buguwa ce mutum biyu ne suka samu kurjewa daga driver sai na kusa da shi.

Hjy iya ma kafarta ce ta bugu amma ganin yanda motarsu ta yi lokacin da zasuyi accident yasa ta rudewa tana tunanin taji mugun ciwo.

Sannu suke ta jero mata wani matashi shi kuma yana ta mata fifita da gefen rigarsa, jitai abu na yawo  daga cinyarta har zuwa tafin kafarta, cikin rudewa ta kara fashewa da kuka tana fadin,   " wayyo ni Allah ashe ajali ne yake kirana, kaico duniya kaico abinda zai kare mu cikin duniyar nan, mutuwa karshen kowa ashe ajali na ne yaxo shiyasa habibu ya hanani tahowa naki yarda da maganarsa.

Yanxu shikenan nida habibu sai a lahira 😭 Allahu akbar habibu na yafe maka duniya da lahira dama ni ba abinda kamun kullin cikin kyautata mun kake, Allah ya shirya ma zuriyarka habibu, nikam tawa yau ta kare, ganin irin surutun da hjy iya take bame karewa bane yasa wani daga cikinsu ya katse.............. Iya dan Allah ki kwantar da hankalinki duk cikin motar nan babu fa wanda yaji wani matsanancin ciwo ko akwai wani guri da yake miki ciwo ne?

      Cikin rudewa hjy iya ta fara magana yaro nifa tawa taxo karshe, dan Allah ku kira mun habibu a waya, muyi bankwana dashi damin ni nan cikin jiki nake tsamo-tsamo kunga da jinin mutum ya kare ay sai mutuwa 😭, hjy iya ta kara rushewa da kuka.

Aykuwa nan da nan hankalinsu ya kara tashin jin hjy iya tace cikin jini take, da sauri wani saurayi ya ciro wayarsa ya kunna touchlight dama wani dattijo ya kunna tashi fitilar amma batayi hasken wannan ba.

Cikin tashin hankali matashin nan ya cewa sauran mutanen,  " dan Allah yanxu meye abun yi nifa na tsoro ta tunda kunji tace jini ne yake zuba ajikinta gamu cikin dokar daji, eh to hasko mu dubata muga ina ne taji ciwon inyaso ko dankwalinta sai asa adaure ay bama zuba mata ido tana ta fama da ciwo a jiki ba.

Haskata saurayin yayi, mutum biyu daga cikin su suka fara dubata, duk wannan abun da akeyi hjy iya bata daina surutai da Addua ba, " kunga nifa banga wani jini ajikin baiwar Allah nan ba ko kurjewa ban gani va sai dai ko buguwa............ Aykuwa hjy iya tai karaf ta karbe

YAWON SALLR HJY IYA CompleteWhere stories live. Discover now