21&22

97 18 2
                                    

👠👠
*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*
( _A hanyar lamba_) 👜👜
       _27/6/2020_

*Written by*:- _Ameera Adam_
    _AmeeraAdam60_
*@wattpad*

*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼

*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*

                20&21

Galala me gari ya saki baki da hanci yana kallon dafta tanimu, cikin jin haushi ya kalli mutum daya daga cikin yan zaman fadarsa yace, " aje ataho da dafta tanimu cikin gaggawa, kirar mutumin ita zata tabbatar maka da kakkarfa ne, tun kafin me gari ya rufe baki haladu ya shuri takalmansa ya rufawa tanimu baya.

Gudu tanimu yake sosai, yana tafe dafe da hannu aka yana kurma ihu, duk taran mutanen daya wuce da sunji ya ambaci corona zaka ga kowa ya take kafarsa ya manna da gudu, Haule me kosai da koko tana bakin kaskonta, cike yake da masu siya wasu na jira azuba musu su tafi, wasu kuma anzuba musu suna ci,  tanimu suka hango daga cen nesa ya taho da gudu ga mamaki suke kallansa, balele ne ya kasa rufe bakinsa cikin mamaki ya dubi abokan cin kosansa  yace,    " bukar wai kaga abunda nake gani kuwa? Eh, ka rigani afili na riga ka azuci, kamar dafta tanimu nake hangowa.......... Haba balele ba kama bace shi din ne, lawwalu ya katse balele.

To kuwa akwai babban al'amari tunda kaga mutum dan gayu me ji da boko ga taku dai-dai kamar dafta tanimu yana gudu wallahi akwai muhimmin abu......... Kudai kun cika tsoro kamar ba maza ba, kuluwa yar  haule me kosai ta katse su, to dan kunga tanimu na gudu sai me........... Ke raba kanki kuluwa kinsan duk fadin garin nan ansan waye dafta tanimu, mutumin da ko kasa baya san takawa inyana tafiya, balele ya katse kuluwa.

Kai ka biye ta ma walla............. Wayyo Allah jama kowa yayi ta kansan corona virus ta shigo gagaren hayi, wallahi kowa ya killace kansa karya sake yaje gidan me gari inba haka ba shima ya zama marigayi, tanimu ne yake zabga gudu yana wannan surutan daga dan nesa kadan haladu na biye dashi, har ya karaso gurun su balele.

Jin kalmar corona virus ita tafi tsoratar dasu aykuwa azabure gaba daya gurin aka fashe kowa yayi ta kansa, haula batasan lokacin da tayi gaba da kullin kosantaba, kowa takai-takai yake yi, kuma kowannen su idan yaje guri shima gaya musu yake corona ta shigo gangaren hayi, kafin kace me gari gaba daya ya hautsine da labari.

_A GIDAN ME GARI_

   Hjy iya jikin nata ya dan fara sauki, saboda garwashin wutar da aka kai mata najin dumi, matar megari taje kaiwa dan tsoho abincin karin safe daidai soro ta riski maganar tanimu lokacin da yake ambatar corona virus gabanta ne ya yanke ya fadi, cikin tsoro ta karaso gurin hjy iya take labarta mata,     " iya kinji me nake ji da farar safiyar nan, ay wallahi dama nasan za'a rina tunda dama yau sai da nai mafakin maahe yana fadar wasu maganganu yana nuna waje, tunda na tashi dama nake ta wasi-wasi azuciya ta.

To me yake faruwq agarin ne? Hjy iya ta tambaya,  " kinajin wai muguwar abar nan ce ta shigo.......... Wacce aba kuma, hjy iya ta katse ta, wannan cutar mana da ake ta fada mufa nan gaskiya bamu yarda da ita ba, amma tunda kika ji ta fito daga bakin dafta tanimu to ta shigo din.

Magana kike tamun kin ki kigaya mun wacce cuta ce, hjy iya ta fada, cutar nan mana ta korola baros.

😳😳😳 zare idanu hjy iya tayi, tana fadin, wai dama wannan ciwon gaske ne nima fa ban yarda dashi ba, wallahi gaske ne tun da tanimu dai babban likita ne munan duk garin nan idan harkar lafiya taxo mana shi yake magance ta, to kuwa kinga ay maganar wasu-wasi tq wuce.

A zabure hjy iya ta tashi ta janyo kayanta da suke makale ajikin karfen gado, ta fara kokarin sawa.

Tana yi tana salallami, cikin mamaki matar me gari take tambayarta iya me yake faruwa naga kina hada kaya ko karyawa baki gama ba......... Hjy iya ta katse ta,  tafiya zanyi dan wallahi bazan zauna ba tunda dama habibu yaban labari wai killace mutane ake aguri daban nikam gaba zanyi, dama fakewq mukayi saboda dare amma yanxu tunda gari y waye bari na kama gaba na.

Tanimu ka dakata daga nan karka bari inkama ka inba haka ba zaka yabawa aya za'kinta, kasan irin daukan da nayi wa musubahu rannann ko? Haladu ne yake wannan maganar ganin irin gudun da suke yi shida tanimu, dan waigowa tanimu yayi yana fadin naki na tsaya din kaima kayi ta kanka, kara gudunsa haladu yayi da kyar ya samu ya dango wuyan tanimu, sama yayi dashi ya sa'bashi a kafada mutane suka zuba musu idanu kowa na tofa albarkacin bakinsa.

Mutane ne dam'kam suka rufawa tanimu da haladu baya kowa na tafe yana tsegumi, wasu har tuntube suke dan suje gun megari suga wanne irin laifi tanimu yayi da har akasa haladu ya daukoshi.

Wasu ma da suka daurewa karya zani ta bayan layi suka biyo dan su riga su haladu karasawa, aykuwa kafin kace kwabo fada ta cika tayi makil da mutane ansa tanimu a tsakiyar tabarma kowa da abinda yake ayyanawa.

Tanimu na zaune ya janyo gefen rigarsa yana rufe hanci dashi, yana yi yana watsawa mutane harara, hayaniya ce take dan tashi kasa-kasa ana ta tsegungumi, gyaran murya me gari yayi nan da nan kowa yayi shiru.

Me gari ne ya kalli tanimu cikin daure fuska yace,       " Tanimu me ka dauki masarauta ne? Idan kana ganin kai kadai ka samu ilimin fannin lafiya, karka manta ni da kaina naje gidan Alh ya'u tsohon kansilan mu na koki alfarmar ya turaka ka karanci fannin ilimi abirni lokacin ko babbar sakandire baka gama idan baka manta ba sai da mukayi yarjejeniya akan zaka tallafi mutanen garin nan muddin ka dawo, bama wannan ba dazu nakira ka ina maka magana akan bakin da muka samu jiya,  har ka na toshe hanci saboda raini, me gari y kara sunkuyo da kansa ya kalli tanimu cikin daure fuska yace,  " ko ka gaya mana dalilinka ko kuma insa abaka horo me tsanani, domin bazamu  dauki wulakanci da raini acin garin gangaren hayi ba.

Dago da idanuwa tanimu yayi ya karewa mutane kallo, duk inda ya kalla idanunsu yana kansa yana waigawa gefensa ya hada ido da innarsa tana goge hawaye, cikin daga murya san kira ya yi wa tanimu magana,  " kai yaro tanimu kasan a inda kake me gari na saurarenka, dan muskutawa gaba kadan tanimu yayi ya fara magana, cikin toshe hanci,    "   Jama'a salamu alaikum me gari ya sameni yau ya sanar dani halin da bakinsa suke ciki, kuma a bincike da manyan likitocin duniya tayi ta tabbatar da duk mutumin da aka samu yana mura da tari da sarkewar numfashi hade da zazzabi to fa yana dauke da corona virus.

Kuma duk alamomin da na lissafa shine abunda me gari ya sameni yake gaya mun, tanimu kara gyara hannunsa yayi ya kara toshe hancinsa da kyau ya cigaba da jawabi, to atakaice dai abunda nake san gaya muku shine bakin me gari suna da corona virus kai harshi kanshi me gari da iyalan sa ina da tabbacin suma sun shaki wannan ciwon,  hayaniya ce ta kaure gurin kowa da abinda yake fada, cikin bacin rai me gari ya bugawa tanimu tsawa, dakata tanimu bamasan maganar banza da wofi mu zaka kawowa maganar shashanci?  Me kake shirin fada ne.............. Daya daga cikin fadawan me gari ne yadan rissana cikin girmamawa ya fara magana,  " Allah ya baka yawan rai me zai hana abar tanimu ya cigaba da jawabi saboda tunda muke da tanimu bai taba mana irin wannan wasan ba, sai nake ganin dafta tanimu maganarsa kamar da kamshin gaskiya acikinta.

Hayaniya ce ta kaure gurun cikin hadin baki mutanen gurin suka fara fadin,  " tabbas dafta nada kamshin gaskiya, tunda haka kawai bazai yiwa me gari karya ba.

Tanimu ne ya mike tsaye ya cigaba da magana, yanxu kowannen ku dole ya dauki matakin kare kansa, danni nan da kuke ganina babu wanda zan iya bawa wata kariya, kowa tashi ta fisheshe....................... Tarin dan tsoho me buhu ne ya katse shi, juyawa suka daga wajen kofar gidan me gari suka ga dan tsoho ya fito duku-duku, tari yake yi yana tofar da ka-ki gefe gurin taron mutanen daya hango yake niyyar zuwa.

       Aykuwa suka ce me gaba daya mutane suka fara gudu, wasu fadawan me gari malin-malin har tad'e kafarsu take suna faduwa.

_Sorry sister's jiya kun ji ni shiru chani ne babu, ina godiya da kulawar ku iya wuya muna tare_.

*Vote*
*Comments*
*Share*

         _MOM ASLAM Ce_😉

YAWON SALLR HJY IYA CompleteTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang