👠👠
*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*
( _A hanyar lamba_) 👜👜
_6/7/2020_*Written by*:- _Ameera Adam_
_AmeeraAdam60_
*@wattpad**HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*
29&30
Wani irin abu ne ya kara tasowa Alh habibu jin irin maganganun da lauwali yake fada akan hjy iya, zuciyarsa ce ta karye ya tuno bayan sallar idi daya zo gaisheta da lokacin da suke cin Abinci, nan da nan yaji kwallah na shirin zubo masa, cikin dakiya da jarumta ya kalli lauwali yana fadin, " Karka damu lauwali insha Allah hjy iya aduk inda take muna sa ran tana cikin koshin lafiya, maganar laifi kuma ni ba wani laifi da kamun hasalima lokacin da hjy iya zata tafi ay muna tare da kai a gidan gona ta, nayiwa Dpo magana da yardar ubangiji za'a bincika inda hjy iya take.
Zaro idanu gaba sukayi su hansai da lauwali kamar hadin baki suke tambayar sa, Alh bamu gane za'a binciko hjy iya ba 'bata tayi ne? Dan jim kadan yayi ya hadiyi yawu me d'aci sannan yace, " nayi waya rigana bata karasa ba kuma wayarta na hannun wani yaro, shi ne kiran da nayiwa Dpo dazu tafiyar da za'ayi da ku inna zainabu zaku amsa tambayoyi ne ba wani abu ba.
Wannan karan ba su inna zainabu ba hatta lauwali sai da yan hanjinsa suka kad'a saboda tsananin tsoro da tashin hankali, shi duk a tunaninsa ya zaci fada Alh yake wa su suwaiba akan tafiyar hjy iya, ashe babban lamari ne, gumi ne ya shiga karyowa dukkanninsu aka rasa me bakin magana.
Audi dake cen jikin katanga hankalin sa ya bi duk ya tashi, cikinsa ne yake hautsina masa ga gumi yana karyo masa.
Lauwali na nan gefe a tsugunne kamar wanda aka tsunkula yace, Alh ina Audi ko shi babu shi acikin laifin? Baya gidan, Alh habibu ya bashi amsa atakaice, suwaiba ce tace, " nifa Alh ina ganin kamar Audi yana cikin gidan nan saboda ban dade da barin gurin cen ba naga ya shiga d'aki.
Idan yana gidan zanzo inyita horn be bude ba? Hjy habibu ya tambaya fuska ba walwala, ganin yanayin da Alh habibu yake ciki yasa duk suka yi shiru.
Turo kofar suka ga anyi a tsammanin Alh habibu ko yan sanda ne suka iso, khaleeda, huzaifa, Ameer da Sulaiman ya gani, kowannen su daka kalli fuskarsa kasan yana cikin damuwa, cikin halin jimami suke tambayar mahaifinsu, " Daddy d'azu mami take sanar mana abunda yake faruwa wai hjy iya ta tafi Rigana kuma wayarta na hannun wani yaro"
Eh haka ne, kuma na kira cen riganan ma bata karasa ba, 😳 zaro idanu suka yi lokaci daya suna tambayarsa, " ba tun jiya akace ta tafi ba? To me yake faruwa"
Kofa aka banko da karfi gaba daya idanunsu yayi bakin kofar, police ne sun kai su bakawai sai human police daya, Alh habibu nuna musu su hansai yayi, aykuwa su inna zainabu suka fashe da ihu duk wanda yake gurin ya ga irin kukan da sukeyi sai sun bashi tausayi.
Lauwali ihu yake yana fadin wallahi ba hannuna asace hjy iya, ku tambayi Alh kuji muna gidan gonar sa, dan Allah ku min rai ko shaida bantaba zuwa bayarwa ba offishin yan sanda, babu wanda yabi ta kan Lauwali, incharge dinsu ne ya kalli Alh habibu yace, "Alh suke nan ko? Eh su kenan Alh habibu ya bashi amsa, sallama yayi wa Alh habibu har ya yi hanyar get ya juyo da niyyar tambayarsa, Aykuwa ya hango d'an kai daga jikin bango ana lekowa, kallan gurun yayi da kyau Audi na ganin sun hada ido ya koma ya ma'ke yana maida ajiyar zuciya.
Alh wancen me lekowar kasan da shi ne, waye yake lekowa? Alh habibu ya tambaya, tun kafin ya rufe baki, incharge din yabi lungun da gudu, Audi najin antaho gurin da yake yayi sufa ya kama jikin wata bishiya ya kankame, police din na zuwa ya d'aga kai sama ya hango kafafun Audi na rawa a sama.

ESTÁS LEYENDO
YAWON SALLR HJY IYA Complete
Historia CortaGudu yakeyi iya karfinsa amma saboda yanayin girma ga tsufa lokaci guda suka cin masa. A tsakiya suka saka shi suna kokarin rike hannuwan sa, dan tsoho yayi wani kukan kura cikin karaji irin yanda jariman india sukeyi idan suka fusata, yasa gwiwar h...