👠👠
*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*
( _A hanyar lamba_) 👜👜
_1/8/2020_*Written by*:- _Ameera Adam_
_AmeeraAdam60_
*@wattpad**HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*
41&42
Hjy iya hararar wasa ta watsawa khaleed tace, " meyasa baka biyoni har nan neman nawa ba kabar ubanka yake ta zarya" ta cigaba da cewa, " ke kuma ja'ira ina nan har sai naga aurenki da 'yayanki ke ni nan sai na mammaka miki ganye idan kika haihu.
Juya kai gefe fatima tayi cikin wasa tace, " cab lallai ma hjy iya da kanki zakiji ko da ruwan zafi? "
Musa ne ya katse musu hirar cikin girmamawa yace, " Alh ku shiga daga rumfa mana ga tabarma ku zauna"
Guri suka nema suka zauna larai matar musa ta kawo musu ruwa me sanyi na cikin randa, sha sukayi sosai suna santin sanyinsa.
Hira ce ta barke atsakaninsu anata hirar yausha gamo, hjy iya tana kusa da Alh habibu ta rik'e hannunsa gam kamar wanda zai gudu ko za'a kwace shi sun shafe kusan awa guda suna hira daga karshe Alh habibu ya nemi kebewa da mlm musa.
Dakinsa musa ya jashi suna shiga dakin Alh habibu yace, " mlm musa nagode kwarai da irin taimakon da abinda kamun duk fadin duniya banida sama da mahaifiya ta, ina kaunar hjy iya zan iya rabuwa da kowa da komai akanta, bani da wani abu da zan maka na godiya dan Allah kayi hakuri da wannan " kudi ne yan dubu-dubu bandir biyu, Alh habibu ya janyo hannu mlm musa ya sa masa aciki.
Kamar amafarki mlm musa ya zurawa kudin idanu, yana kallo dan murna fashewa yayi da kuka yana kamo kafar Alh habibu yana zabga masa godiya.
Alh habibu hannu yasa ya d'ago shi sannan yace, " haba mlm musa meye na tsugunnawa sam ni banasan irin haka, kuma abu na gaba banasan idan mun fita kacewa wani daga cikin su na baka wani abun"
Jan majina yayi ya sharce hawaye ya amsawa Alh habibu.
Bayan Alh habibu ya dawo gurin su hjy iya kallanta yayi yace, " hjy iya kin gama komai zamu iya wuce wa ?"
Cikin murmushi hjy iya tace, " nagama komai habibu na yau sai gida, ke fatima tsallaka ga jakata cen jeki dauko"
Hjy iya kudi ta debo masu yawa ta bawa larai sai zabga godiya takeyi.
Fitowa sukayi kofar gida, duk makota sunyi carko-carko suna lekensu, Alh habibu ya kalli yusuf yace, " samari kaida baba ya sunan garin da kuke sai mu saukeku "
Yusuf ne ya fara magana, " nidai a kurna nake baba kuma bansan a ina yake ba"
Kallan sa Alh habibu yayi alamar yana san yaji ta bakinsa.
Dan tsoho kallan hjy iya yayi ya saki wani malalacin murmushi sannan yace, " ummmm d'a habibu dama kai nake jira infayyace maka duk abinda yake faruwa, to kuma bansamu lokaci na maka maganar ba"
Da mamaki Alh habibu ya kalli dan tsoho yace, "To baba lafiya dai ko?"
Ehto dama tun ranar da muka hadu da hadizatu Allah ya dasamun wani abu a zuciya ta, nayi kokarin infahimtar da ita amma kamar tamun mummunar fahimta, so nake na aureta ne muyi zamanmu cikin lumana da kwanciyar hankali"
Khaleed, fatima, khairat da yusuf dariya suka fara harda rik'e ciki, khairat saboda dariya harda hawaye.
Alh habibu murmushi yayi dan dama tun zuwansa ya fahimci wannan batun daga gurin dan tsoho amma ya basar, tsohon ya bashi dariya sosai saboda da alama irin rigimammun tsofaffun nan ne, kuma shi dan tsoho zuciyarsa daya yayi maganar, Alh habibu tunowa yayi da bayan rasuwar mahaifinsa zawarawa sunyi ta kawowa hjy iya tayi tun ma da kuruciyarta amma babu wanda ta bawa fuska bare yanxu da tsufa yaxo, tunowa yayi akallah mahaifinsa zai samu shekara sama da hamsin da rasuwa, da irin gwagwarmayar da hjy iya tasha akansa, nan da nan kaunar mahaifiyar tasa ta kara ratsa jinin jikinsa........."

KAMU SEDANG MEMBACA
YAWON SALLR HJY IYA Complete
Cerita PendekGudu yakeyi iya karfinsa amma saboda yanayin girma ga tsufa lokaci guda suka cin masa. A tsakiya suka saka shi suna kokarin rike hannuwan sa, dan tsoho yayi wani kukan kura cikin karaji irin yanda jariman india sukeyi idan suka fusata, yasa gwiwar h...