End

115 21 5
                                    

👠👠
*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*
( _A hanyar lamba_) 👜👜
_19/8/2020_

*Written by*:- _Ameera Adam_
_AmeeraAdam60_
*@wattpad*

*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼

*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*

🔚🔚🔚

49&50

Tanimu gyara zamansa yayi ya cigaba da cewa, " to akwai yan hikimomin da nayi nakesan gwada su akan bakin nan da me gari amma fir suka ki amincewa, shi kanshi me gari a yanda na fuskanta tawaye yake san yayi mun, ganin karna takura suyi saurin fuskanto ni yasa na kyale su, to bayan tafiyarsu da kwana biyu sai naji labarin dan asabe shi ya ragewa bakin nan hanya har ya kaisu gidan maigari shi ne naje dan inyi bajinta na tafi da kayayyakin aikina to shine na riski kiran ku da me gari, dan Allah ku mun rai kuyi hakuri sharrin shaidan ne "

Ajiyar zuciya Alh habibu ya sauke yana kara karewa tanimu kallo, sannan yace , " tanimu yanxu kai duk wannan kayan haukan daka hada baka tsoron kaje d'an mutane ya mutu a hannunka, gaskiya kayi babban kuskure kuma acikin maganar nan bai kamata kace shaidan bane, tunda kaima ka sanya san zuciya alamuranka "

DPO ne ya fara magana, " Tanimu ka aikata babban kuskure kuma dole ne hukuma ta hukunta ka, yanxu idan kace kar mu kaika gaba muka sakeka mukasan abun da zaka kulla gaba, mukasan me zaka fadawa yan garinku idan ka koma, dole ne mu mika ka kotu ta yanke maka hukunci dai-dai da laifin da ka aikata, kuma zamu sanar da me garin garinku halin da ake ciki, amma idan muka sakeka mun bawa masu laifin irinka dama su yi ta aikata laifi yanda suke so, dan haka wannan izna ne ga masu shiga aikin ma'akatan da bana su ba, kai Cp sani kuxo ku maidashi kafin muyi refferral dinsu zuwa kotu " DPO ya bada umarni.

Tanimu kuka yake harda hawaye yana rokon ataimaka masa kar akaishi kotu, Alh habibu yaso ya sa baki asakeshi amma nazarin da yayi ya kamata ahukunta tanimu domin ba karamin laifi ya aikata ba, kusan wasa yayi da rayukan ai'umma.

DPO ne ya dakatar da tanimu sannan yace, " tanimu zansa ka raka yarana gidan shi wannan victor din wanda kace shi ya koya maka saida magunguna, shima bazamu barshi a baya ba sai ya fuskanci fushin hukuma " DPO na kammala yasa aka tasa keyar tanimu cikin cell aka rufe.

Sallama Alh habibu yayi masa kai tsaye gidan hajiya iya ya wuce, kamar kullin tana zaune a katafaren fallonta hannun rike da carbi tana ja, da fara'a ya karasa cikin falon har k'asa ya tsugunna ya gaida mahaifiyar tasa, cikin jindadi hjy iya take amsawa tana sa masa albarka, cikin kankanin lokaci su hansai suka cika gaban Alh habibu da kayan shaye-shaye.

Alh habibu cikin girmamawa ya fara yiwa mahaifiyarsa bayani, " hjy iya bamu dade da dawowa daga kauyen gangaren hayi ba, munje antaho dayaron nan da kika kwatanta mun shi, kuma har yayi mana bayani tas da irin tabargazar da yake aykatawa, lokacin da mukaje dama akan aikin shirmen nashi muka sameshi yanayi, gaskiya Allah ya rufa asiri hjy iya kin ceto mutanen garin nan daga cikin wani yanayi "

Hannuwa hjy iya ta d'aga sama tana fadin, " kai Alhamdulillah gaskiya naji dadi habibu da aka kamo yaron nan mara d'a'a, amma baka san wani abu ba habibu " hjy iya ta fada tana kallan Alh habibu.

Cikin kulawa Ya amsa, " sai kin fada hjy iya"

" Abu daya nake so kuyimun " inji hjy iya.

" Wane abu ne haka hjy iya, fadeshi ko mene ne " cewar Alh habibu.

" Habibu yaron nan akwai wasu abubuwa da ya hada lokacin da muna garin nan yace zai mana amfani dasu wai corona garemu, to so nake anemo su duka dan Allah shima yaron nan ayi masa haka kafin akaishi kotun, ja'ir har cewa yayi ayi mana siracen tafarnuwa da citta " inji hjy iya.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 20, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

YAWON SALLR HJY IYA CompleteWhere stories live. Discover now