👠👠👠
👠
👜👜👜
👜
*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*
( _A hanyar lamba_)
_21/6/2020_
👠👠👠
👠
👜👜👜
👜*Written* by _Ameera_ _Adam_ { _Mom_ _Aslam_ }
📚 *HADAKA*📚
📝 *WRITER'S*📝
🖊️ *ASSOCIATION* 🖊️
_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼
@: *Facebook*
_HADAKA_ _WRITER'S_ _ASSOCIATION_@: *wattpad*
_AmeeraAdam60_*SADAUKARWA* *GA* *DUK* *MASOYA* *NA* 😊🤝🏻
_Wannan_ _labarin_ _kirkirarre_ _ne_ _banyi_ _shi_ _dan_ _wani/wata_ _ba._9&10
*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*Cikin hikima ya zagayo da hannunsa saitin aljihunsa, yana yi yana fakon idon mutane har ya samu ya zurata cikin aljihu, guntun murmushin gefen baki yayi ya kara adaidaita zamansa yana yi yana basarwa.
Passinger kusa dashi ne yake yiwa kwandasta magana, " yauwa yaron mota nagaya ma idan kaje dawanau zan sauka, eh " aydama ku biyun nan ne kawai zaku sauka a dawanau kai da baba ta baya, ya karasa fada yana kallan wata tsohuwa dake zaune a akujerar baya, "eh yaro kuma ni ce me farin buhun nan me ratsin ja da baki.
Ba matsala ay mun kusa karasawa ku saka takalman ku kar................ Karaf mutumin kusa da hjy iya yace kwadasta bani sauran canji na nima idan kun karasa dawanau zan sauka, "malam ba a badime kace zaka sauka ba ? To na fasa akwai abunda zan tsaya na karba, to ba komai ungo ragowar kudinka, "kwandasta ya mikamai canjinsa.
Ana zuwa kasuwar dawanau kuwa su ukun suka sauka, mutumin kusa da kwandasta kuma ya koma gunda tsohuwa ta sauka a kujerar baya.
Har motar zata tashi wasu passinger su hudu suka tsaidasu daya tsoho uku samari amma kowannensu da inda zai sauka, tsohon shi bichi yayi su kuma matasan a kwa zasu sauka.
Tsohon shi ya fara shiga ya zauna a maleji kasancewar kudin maleji gareshi sukuma matasan suka hau kujera mota ta d'ame taya suka shilla titi.
Dattijon nan Akallah zai girmi hjy iya sai dai dake jikin namiji da mace ba daya ba, "yana zaune kan maleji yana facing din hjy iya da dan buhunsa makale akan cinya, tunda ya shigo idonsa na kan hjy iya itakam titi take kallo ta window bata ma san yanayi ba.
Buhunsa ya bude ya zaro wata leda, gyada ce aciki marau marau, cikin kashe murya yake wa hjy iya tayin gyada 🤣
Ranki ya dade ga gyada amaro ko zaki taba, " dan waige hjy iya tayi ko zata ga da wacce yake sai dai motar duk maza ne ita kadai ce mace, dan murmushi tayi tace Alhamdulillah nago................. Haba ke kuwa wa yace miki ana maida hannun kyauta baya, sai kace wata indo kinsan masu suna Aisha sune suke abu kamar ba wayayyu ba (🙄🙄🙄🙄🙄 *lallai ma ka raina mana hankali😏* ) karbi dan kar muyi haka dake, ya karasa maganar yana mika mata gyada kamar zai ruko hannunta ya dan'ka mata.
Hjy iya karba tayi amma badan ranta yaso ba, sai dai dan karta gwaleshi, " nagode Allah saka da alheri, hjy iya ta fada lokacin da ta karbi ledar gyadar ta dora acinyarta kusa da jakarta.
Haba kekuwa me sunan tsofaffi wannan godiya haka, kamar wacce nayiwa wata babbar kyauta, duk wannan maganar da yake wa hjy iya kasa-kasa yake yin ta.
Hmmmm nifa ba suna na indo ba, suna na hadiza, dama abinda tsohon nan yake son ji daga gareta, " kara kashe murya yayi cikin kwarkwasa yana fadin, Allah sarki kice sunan uwar gida gareki, Allah ya gafarta miki dije halinki na gari ya biki, "au ta rasu ne ? Allah ya jikanta ya kyauta makwanci, cikin nuna halin jimami ya amsa da Aameen.
BINABASA MO ANG
YAWON SALLR HJY IYA Complete
Short StoryGudu yakeyi iya karfinsa amma saboda yanayin girma ga tsufa lokaci guda suka cin masa. A tsakiya suka saka shi suna kokarin rike hannuwan sa, dan tsoho yayi wani kukan kura cikin karaji irin yanda jariman india sukeyi idan suka fusata, yasa gwiwar h...