👠👠
*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*
( _A hanyar lamba_) 👜👜
_1/7/2020_*Written by*:- _Ameera Adam_
_AmeeraAdam60_
*@wattpad**HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼
@: *Facebook*
_HADAKA WRITER'S_*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*
25&26
Tashin hankali wanda ba'a sa masa rana, huci kawai Alh habibu yake yi gaba daya ransa ya gama baci ga tsananin tashin hankalin da yake ciki, shin me yake faruwa da hjy iya ne? Wa ye ya dauki wayar hjy iya kuma ta yaya har aka shiga cikin gida aka dauki wayar hjy iya me yake faruwa a gidan ne? Amma da ace akwai wani abu daya faru ay zai ji labari ko agidan makotan su hjy iya tunda duk abokan arzikinsa ne wasu ma abokansa ne, Alh habibu shi kadai yake jerowa kansa wadannan tambayoyin, cikin tashin hankali yake ta furta innalillahi wa'inna ilahirraji'un, sa kaiwa yake yana dawowa, gaba dayan yan falon duk sunyi tsuru kowa hantar cikin sa ta kada.
Duk sunyi carko-carko aka rasa me yiwa Alh habibu magana, su dai sunji ya ambaci hjy iya tunda suka ga ya canja yanayi suka san tabbas akwai gagarumar matsala, mami ce tayi karfin halin tambayarsa kirjinta na bugun uku-uku, " Daddyn yara me yake faru da hjy iya ne naji ka ambace ta kuma ga yanayin ka duk ya sauya Allah yasa dai babu wata damuwa? Cikin hanzari ya bata amsa matsala kam akwai ta, wayar hjy iya ce a hannun wani yaro da alama ma irin yan shaye-shayen nan ne amma ina zuwa bari naje gidan yanxu.
Yana gama bata amsa be jira cewar su ba da hanzari yayi get gurin motoci, cikin gaggawa ya shiga horn yake yi ba kakkautawa da gudu ma'awiya me gadi ya fito domin bai saba jin irin wannan horn din ba, har yana shirin yin masifa ganin motar Alh yasa shi saurin wangale get, tun ma'awiya bai karasa bude get din ba Alh habibu ya danna kan motar sa ya fice da gudun gaske.
Ma'awiya ya jima a tsaye yana jimamin halin da ya ga me gidansa aciki, tabbas ya san akwai wata gagarumar matsala data taso dan bai taba ganin sa acikin irin wannan halin ba, jiki a sanyaye yaja get din yana ta'ajibi.
Alh habibu driving yake kamar zai tashi sama duk get din da yaje na titi police da sun tsaida shi ji yake kamar karawa tafiyarsa tsawo suke yi, da sun tsaida shi sun tambaye shi ina zashi saidai yace musu mahaifiyarsa ce aka kirashi bata da lafiya ganin yanayin da yake ciki babu inda ya sami matsala.
Ikon Allah dai shi ya kai Alh habibu unguwar na'ibawa da wani kafirin gudu ya sha kawanar gidan su hjy iya, layin tas yake ba wani alamar damuwa ko tashin hankali yanda ya sa ba ganinsa idan yaje yau ma haka layin yake zuciyarsa ce ta dan fara lafawa.
Horn yake dannawa na tashin hankali ba kakkautawa, lauwali dake dakinsa yana bacci cikin bacci yake jin horn kamar zai fasa gidan afirgice ya mike yana mirza idanu ta dan karamin window din dakinsa ya leka, motar Alh habibu yayi tozali da ita wani irin yamutsawa cikin sa yayi nan da nan gumi ya shiga karyo masa jikinsa har karkarwa yakeyi.
Safa da marwa ya fara yi a dakin daga farkon bangon dakinsa zuwa karshe, ji yayi andakata da horn din ya sauke ajiyar zuciya yana dafe kirji, bai karasa ba yaji anshiga bugun kofar kamar za'a balle ta, da gudu lauwali ya fitar harabar gidan cen bayan dakin su inna zainabu ya shige jikin wani dan lungu ya rabe sai raba idanu yake.
Inna zainabu dasu suwaiba suma a daki kowannen su ya kasa zaune ya kasa tsaye, hansai ce ta kalli inna Zainabu tace, " inna zainabu na tabbata Alh ne yaxo yake wannan horn din yanxu kuma kinji bugun kofa mukam yau mun shiga uku.............. Katse ta Suwaiba tayi tana sharce gumin goshinta ta ce, " to ina lauwali yake kinji shiru har yanxu bai bude ba ko baccin asarar yake yi, ke suwaiba wannan wanne irin bacci ne hk sai dai in yana bandaki, inna zainabu ta basu amsa sannan ta kara da cewa, " yanxu dai wani acikin ku ya je ya bude kofar kar laifin mu ya karu............... Cabdi, hansai ta katse inna zainabu, wallahi bazan je ba haka kawai duk abinda ma zai yi wato a fara ta kaina sai dai suwaiba taje, wallahi bazani ba sai dai a mutu har liman arasa me jan sallah, suwaiba taba hansai amsa, inna zainabu ce tai karfin hali ta tunkari get din kirjinta sai lugude yake tana tafe tana motsa baki ga dukkan alamu addu'a take karantowa 🤣

YOU ARE READING
YAWON SALLR HJY IYA Complete
Short StoryGudu yakeyi iya karfinsa amma saboda yanayin girma ga tsufa lokaci guda suka cin masa. A tsakiya suka saka shi suna kokarin rike hannuwan sa, dan tsoho yayi wani kukan kura cikin karaji irin yanda jariman india sukeyi idan suka fusata, yasa gwiwar h...