7&8

117 21 2
                                    

👠👠👠
      👠
👜👜👜
      👜
*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*
( _A hanyar lamba_)
_15/6/2020_
👠👠👠
         👠
👜👜👜
     👜

*Written* by _Ameera_ _Adam_ { _Mom_ _Aslam_ }
    
    📚 *HADAKA*📚
   📝 *WRITER'S*📝
🖊️ *ASSOCIATION* 🖊️
_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼
@: *Facebook*
_HADAKA_ _WRITER'S_ _ASSOCIATION_

@: *wattpad*
_AmeeraAdam60_

*SADAUKARWA* *GA* *DUK* *MASOYA* *NA* 😊🤝🏻
_Wannan_ _labarin_ _kirkirarre_ _ne_ _banyi_ _shi_ _dan_ _wani/wata_ _ba._

       7&8
*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*

Hjy iya na zaune a kujerar farko ta kusa da maleji daga ita sai kofa, tana nan zaune da yar jakarta a cinya adogace take ko kadan bataji dadin zaman ba ga malejin ma cike yake da yara ga zafin inji na bugota, "basuyi tafiya me nisa ba wani saurayi ya kara tsaida mator ba musu kwandasta ya buga murfin motar da karfi yana fadin aje ta master ga wani kayan ansamu, cikin tsorata hjy iya ta kankame wata mata dake kusa da ita.

Cikin tsananin fada hjy iya ta fara magana, " kai yaron mota me kakeyi haka sai kace karamin yaro, ji yanda ka tsoratani yanzu daka sa aka tsaya a ina zaka sashi baka ganin motar cike take har maleji, " master sata ta nan, faka ta megida,  yaaah ina zakaje ne babban yaya? Duk fadan da hjy iya keyi kwandasta ko 'kurarta bai kalla ba bare yasan tana yi, magana ma yakewa fasinjan daya tsaidasu, aykuwa iya kuluwa hjy iya ta kule.

" Isyaka rabi'u zani, kudinka naira hamsin amma maleji ne ba kujera  kwandasta ya bashi amsa, " ba musu ya taka mota zai hau bisa tsautsayi ya taka kafar hjy iya aykuwa kmr ya watsa mata ruwan zafi da rufeshi da fada dama ga zafi ya addabeta.

Kai kam wane irin mara kunyan yaro ne dan nema zaka takani ko baka gani ne?  To iya idan naga kafarki zan takaki ne kawai daga andan bigeki zaki ishi mutane da sababi ya kara magana lokacin da ya zauna, " au dan bigeni ma kayi lallai yaran nan baka da mutumci fitsararre wanda baisan darajar manya ba amm............... Sorry iya nifa banasan mita kukuma dama tsofaffin nan kadan kuke jira ku jawa mutum jafa'i dan bakinku kaifi gareshi kamar takobi, "kai kwadasta hawo mu wuce na zauna matashin ya fada yana kokarin saka headphone akunne.

     Sakin baki hjy iya  tayi tana kallonsa kamar tamai magana kuma sai ta fasa, " rufe musu kofar kwandastan yayi ya zagaya ta baya ya shige booth,  " duk bidirin da sukeyi driver yana jinsu,yana jin kwandasta ya zauna ya fizgi mota ya cilla ta titi.

Cikin abinda baifi minti talatin da biyar ba suka karasa kano Gestin hjy iya ta sauko da kyar tana dan dingisa kafa, jakarta  ta rike sosai ta hango wasu mata zasu tsallaka titi ta karasa kusa dasu zuwanta keda wuya wani dan karota yazo ya tsallakar dasu.

motoci ne ajere taji ana kiran kofar ruwa, kurna, rijiyar lemo, bacirawa, multara dawanau ciko saura mutum hudu.

   wannan karan hjy iya jikin window ta samu tana nan zaune ba jimawa fasinja suka cike motar, wanda yawanci motar duk maza ne mata uku ne, " daga hjy sai wasu mata biyu abaya, motar su hjy iya na tashi wani driver ya dora tashi su hjy iya aka shilla titi🤣🤣

Suna cikin tafiya kwandasta ya fara hada kan kudin mota yana bawa mutane canji, tafiya ta fara nisa mutumin dake kusa da hjy iya ya fara gyangyadi idan yayi gaba sai kaji luuuu ya dawo jikin kujera, cen da bacci yayi dadi hjy iya batayi aune ba sai jin mutum tayi ya fado jikinta, ganin baccin da yk yi yasa bata damu ba ta sa hannunta tadan tureshi.

A dan tsorace ya bude ido cikin jin kunya yabata hakura.

Jingina kansa yayi jikin kujera ya cigaba da baccinsa, suna cikin tafiya mota ta taka birki firgigit ya tashi yana yan kalle-kalle amma da ganinsa ya tsorata da yanda yaji birkin motar, " can tafiya na kara mikawa luuuuu mutumin nan ya kara fadawa jikin hjy iya baccinsa yake lakadan dan sai sakar minsharinsa yake, wannan karan hjy iya dan karamin tsaki taja ta dan turesa da hannu.

Ko kadan baima san tanayi ba, minshari yake saki ji kake kaaaarrrrr huuuuu mummm kakkakakaka 🤣🤣 ( _kamar_ _minsharin_ _shamsiyya_ 🤪 )

Mutumin dake kusa dashi ne ya dan tasheshi, cikin kosawa yake fadin malam kana dan bige dattijuwan nan, " a kunyace ya hau murza fuska yana gyara zaman hularsa kamar gaske ya zauna yana kallan hanya .

Mutumin hjy iya be daddara ba haka bacci ya kara daukansa wannan karan bacci yake hardasu yawun bacci, luf yayi agefen kafadar hjy iya, sosai hjy iya ta kai bango cikin jin haushi ta hada karfinta guri daya ta hankade shi hadi da danna shi kan dayan mutumin dake cen gefen nasa🤣🤣🤣

Sosai ta bawa yan motar dariya ashe duk budurin da ake suna kallo, " dariya suke a fili yayin da mutumin nan ya kule sosai ya juya ya ballawa hjy iya harara hadi da tsaki yafara maganganu kasa-kasa, " zagina zakayi ne kaa saa uwar bacci naji kana gunguni me baccin larura, dan wannan baccin naka bana lafiya bane Allah ya yaye maka cutar nan da kake fama da ita, mutum sai baccin asara ta karasa maganar tana juya kanta wajen window.

A harzuke ya juyo gurinta yana fadin, " ni babu wata cuta da take damuna haka kawai ina zaman zamana zaki ja mun ciwo muji da  wannan annobar cutar ta corona mana, ba dama mutum ya kishingida sai afara jamai masifa, to ni lfy ta klau na ma kusa sauka na huta.

kai karan mota idan kaje Bacirawa kwanar madugu zan sauka, kwandastan da aka kira da karan mota ya dago da rinannun idanuwansa jawur cikin dakusashiyar murya yake fadin "kai master ka iya bakin ka fa, na rantse da buwayar Allah idan ka kuma cemun karan mota sai na maka aikin karnuka, ya karasa maganar yana cije baki gefe.

Tsit kake ji ba wanda ya kara magana har akaje inda mutumin nan zai sauka.

Motar su hjy iya ba ita ta kaisu multara ba sai karfe 3:10 pm  lokacin kowa ya fito hjy iya wani gida ta hango daga cen tsallaken titi, yanayin gidajen kanana ne wasun su ma ginin kasa ne.

kasancewar titin babu motoci sosai nan da nan hjy iya ta tsallaka da sallama ta shiga gidan, bayan sun gaisa ta koki alfarmar zatayi sallah, ba musu matar gidan tazuba mata ruwa a buta, hjy iya tayi sallah azahar tana nan zaune tana lazumi matar gidan ta zubo mata tuwo miyar taushe da kunun gyada ta ajiye mata agefenta.

Hjy iya na idar da lazumi ta dau kofun kunu ta fara sha ( _nikuwa_ _nace_ _su_ _hjy iya babu ma dan jan aji_) sai da ta kusa shanyewa ta ajiye jin kiraye kirayen sallah la'asar take yi , sallah  tayi ta fito tana yiwa matar gidan godiya,  dubu biyu ta zaro ta mikawa yaron matar wanda befi shekara hudu ba, aykuwa tasha godiya har kofar gida matar ta rako hjy iya tana mata Allah ya tsare hanya.

Tafiya ta danyi cen tsallaken titi cen ne ta hango yan gada-gada suna lodin motar bichi lamba dan zqbuwa, tana zuwa motar ta cika har driver ya janyeta.

Wata bus din aka matso da ita hjy iya itace farkon passinger wannan karan ma itace jikin window, a hankali mota take ta samun passingers har ta cika, hjy iya na nan zaune mutumin dake kusa da ita ya dan fara janta da hira tun hjiy iya na maze fuska harta saki jiki, cikin hikima yake tambayarta, baba yanzu karfe nawa ne wlh wayata ta mutu ba caji, gashi kuma inda zani  ana jirana, akan idonsa 👀 ta zuge jaka ta dauko wayarta " cikin mamaki take kallon agogo karfe 4:50 pm wato biyar saura, afili ta furta lokaci baya jira Allah dai yasa mu cika da imani Aameen.

Shi dinma da Aameen ya amsa mata, yana nan yana fakon hjy iya harta zuge Aljihun jakarta tasa ta rufe.

Shiru ne ya biyo baya bame cewa wani uffan, hannu ya fara mikawa sannu a hankali har Allah yabashi sa'a akan wayar hajiya iya.

   _Tabdijan anyi WUFF da wayar hjy iya akwai sabon rikici_

*Vote*
*comments*
*Share*

YAWON SALLR HJY IYA CompleteWhere stories live. Discover now