31-32

78 10 1
                                    

👠👠
*YAWON* *SALLAR* *HAJIYA* *IYA*
( _A hanyar lamba_) 👜👜
       _11/7/2020_

*Written by*:- _Ameera Adam_
    _AmeeraAdam60_
*@wattpad*

*HADAKA WRITER'S ASSOCIATION*
_Home_ _of_ _co-opration_, _peace_ _caring_ _and_ _accepting_ _of_ _correction_ _among_ _us_✍🏼

*BISMILLAHIR* *RAHAMANIR* *RAHEEM*

                31&32

Kai mene ne sunan ku kuma meye matsayinku a gidan hjy iya, wani dan sanda me suna samuel ya bugawa lauwali da Audi tsawa da suke cikin cell sai muzurai suke suna zare idanu, duk an tube musu kayansu daga su sai singlet da gajeren wando, kallan juna suka shiga yi basu da alamar magana kowanne kirjinsa sai bugawa yake, aykuwa samuel ya kara buga musu tsawa, " Kai you are very stupid, am talking to you and u  are looking each other kuna hauka ne kunsan a ina kuke kuwa" lokaci daya cikin su ya kara hautsine wa a zabure kowannen su ya amsa lauwali ne ya fara magana, " ni suna lauwali ni ne driver gidan hjy iya kuma wallahi lokacin da hjy iya ta fita................." katse shi samuel yayi da, "shutoff your mouth waya tambaye ka " ay kafin samuel ya karasa magana tuni lauwali ya tsuke bakin sa.

Audi ne ya fara magana,  " ni suna na Audi ni ne me gadin gidan hjy iya" baki Audi yaja ya tsuke ganin yanda akayiwa lauwali yasa yaja baki yayi gum yana fargabar ta kanwa za'a kuma jeho tambayar, samuel ne ya tattara hankalin sa gun audi yace,  " good, like you said you are getman dat mean u are the security of the house,ok? " Audi kallan samuel ya shiga yi kamar me fahimtar wani abu amma sam be gane me samuel yace ba, tsawa samuel ya buga masa, " am asking u and u just looking at me, ko so kake sai na hada maka da duka ne? "

Audi ganin samuel ya fusata da jin kalmar duka yasa yafara magana, " me na me gadi hjy iya go and me nace karta fita, Alh zaiyi fada and hjy iya starting fada and tace everybody gayawa Alh zatasa akore mu, Audi ba karamin bawa samuel dariya yayi ba jin yanda ya takarkare yana zabgo turanci, amma gudin raini yasa shi ya tsuke fuska ya cigaba da tambayarsa da hausa.

Meyesa baku dakatar da hjy ba lokacin da zata fita tunda kunsan bata fita ita kadai? Audi labari ya bawa samuel duk abunda ya faru da hjy iya kafin fitarta, juyawa yayi gurin Lauwali da yake ta raba idanu tambaya ya watso masa,  " kai ne driver ko? Kana ina lokacin da hjy ta fita tunda kaine me kaita duk gurin da zata je ? Lauwali dama jira yake azo gurinsa dan lokacin da samuel yake jero masa tambayoyin ji yake inama ya fara bada amsa tunkafin ya gama, amma tsoro ya hanasa magana har sai da samuel ya bashi dama aykuwa cikin sauri lauwali ya fara  bawa samuel labarin duk abunda ya faru na fitarsa gidan gona da Alh habibu da dawowarsa da yanda yazo ya samu Audi.

Samuel ne ya kalle su sannan yace, " ok duk naji bayanan ku kuma idan wasu tambayoyin suka kara tasowa za'a bukaci ku bada amsa, ya karasa magana ya na kokarin fita, bayan fitarsa ya janyo kafa ya maida ya rufe.

Da sauri Lauwali ya karaso bakin kofar yana fadin, " yallabai dan Allah nidai ka taimaka ka fitar dani tunda na maka bayani kuma ni banida laifi aciki, samuel ko waiwayensa baiyi ba ya kara gaba, haka lauwali da Audi suka dinga magiya ta jikin kofar cell din, wani dan sanda ne ya taso ya zo baki kofar ya buga musu tsawa,  " kai kuyi mana shiru kar ranku ya b'aci sakarkarun banza, tsit suka yi ba wanda ya kara magana, juyawa yayi ya koma gurinsa ya zauna.

        Zuwa wani lokaci yunwa ce ta fara sasukar Audi da lauwali, sake lekowa sukayi suna magana,  " officer dan Allah ku taimaka mana da Abinci wallahi yunwa muke ji ga kishirwa na damun mu, shi kuma Lauwali fadi yake yallab'ai ataimaka afitar dani tunda banida laifi, wani police ne yaxo wucewa yaji sunata ihu cikin fada ya fara musu magana,  " kai wai ku kadai aka kawo nan da zaku cika mana guri da ihu wallah duk wanda na kuma jin maganar Allah idan nazo sai ya goya kansa ko yayiwa kansa makawuya, tsit kake ji kamar anyi ruwa andauke su Audi baki ya mutu ganin yanayin dan sandan ba karamin tsorasu yayi ba kato ne me kiba ga tumbi hannunsa dauke da wani katon kulki, kallansu yayi yace " da kunsan kuna san iskar wajen kuka aykata laifi sai kuyita zama har wanda yasa aka kawo ku nan in yazo ya bude ku, ya karasa maganar yana yin gaba abinsa.

YAWON SALLR HJY IYA CompleteWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu