👑king's daughter ✨.
After three days sanye take cikin wani hadddan lace meshegen tsada Fara ce tas gata doguwa tana da anjiki tafiya take kamar baza ta taka kasaba cike da kasaita da sarauta dake janta,wani bodyguard dinta ne riki Riki da Kaya a hannunsa,.
Wata zukekiyar mota naga anbude mata tashiga. Binsu mai ribi ribi dan Sanin wace wanan mata shekarun ta baze wuce 40 ko 43 ba kyakyawa ce ta gaske Inka kalleta sekaran tse budurwa ce,.
Tanashiga kuwa Tai wata budurwa nagani agefenta ta turo Baki, murmushi tamata cwthrt sorry nadade ko,
ammi kinda de harnagaji, kallanta nasake da kyau tana Kama da matar itama kyakyawace,
sede dukansu suna min Kama dawasu Wanda nasani Amma namanta dasuwa sukemin Kama,.
To aikece seda nace kibiyoni kikace kinfisan kizauna a mota, driver mujeko, Ansata yayi to rankishidade,.
Binsu naringa to Inga inda wanan mota zata, 😲huh masarautar merah naga sunshiga dawayo nasamu Nawuce dankarun wajan karsu ganni Suhani Shiga itada wanan budurwar daba takai seemah ba
,dan KO Aysha zata girme ta,. Iso aka musu se gaishe su ake,.
Sarauniya hafsat nagani tare da mukarraben ta da alama Shawati tafito yi, se wani smiling take wani mugun farinciki ta tsinci kanta Gani take karshen yarima yazo tinda kusa cimma Nasara akan abinda yakeso,.
Jakadiyar tace tanaso gunta,Kai asunkuye cikin girma mawa irin ta sarauta, rankishidade anyi Baki a masarautar Nan, Kuma ba wata bace illa kanwar Zalihat tare da yarta sunzo,
alamu sun nuna yarima sukazo dubawa.
Afusace takalleta kina nufin Khadija, kwarai kuwa Dan nashaidata,
numfashi mezafi tafitar to uban meyaka wota Yar uwar Tata tamutu Amma Dan susuka fi kowa nachi masarautar namu ma baza akyalemu Misha iskaba,
Kai ni duk wani zuriar zalihat natseshi Bana kauna inde na ga Khadija jinake kamar naga zalihat natsani duk wani Wanda yahada jini dasu, Magana take ta na huci,
Allah yahuci zuciyarki, Amma rankishidade bakya ganin ko maimarta ba ya gaiyace su sukazo.
Wani mugun harara ta wulla mata yakira Su yamusu me banasan wanan banzar tinanin naki, fuuuh takada alkabbarta tawuce bin bayanta sukai ribi ribi,.
Daga nesa tahango Khadija wani mugun kyau tamata, shegiya Anya ba plastic surgery take zuwa akara mataba kuwa,
mutun yagirma kamar begirma ba,duk wanan abinda datake azuci takeyinsa, tsaki tajaa tanajin haushin kanta,haba hafsat kefa Queen ce karki zibda ajinki mana kinfita matsayi she is just princess Kuma karki Manta ba a royal family take aureba,haba wuce nan kinyi da yatta bare ita.
Yakowa sukai harsuka karaso inda Queen take yisukai kamar Basu gantaba,
ganitai da gaske ba kula tazasuyi ba Dan suna gab da Bata kunya, sauri Tai tace Ashe manyan Baki mukai hajiya khadija,
ina fatan de Bawani maganin asirin suka kawo maiba dan bayau akasa ba, kallan sama dakasa Khadija tamata Basar watai Tai wani kayataccen murmushi Wanda hafsat ta fi wa tsanar wanan murmushin nata,
YOU ARE READING
yar sarki 👑(King's Daughter )
Historical FictionLove,hateret, sacrifice, deception, royalty.