(1)

432 14 0
                                    

WATA KADDARAR. 
       
               BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

DIVAADOVEYSDIARIES

WATTPAD
@Divaadoveysdiaries03

OKADABOOKS
@Divaadoveysdiaries03

FIRST APRIL ,2020

Page (1)

This book is not a free book, I'll give free pages,then whoever wants the continuation pays for it..price in group is 150, private is 200..transfer through the bank or credit transfer can be made through.. credit  08165992806.
Bank ..0156213892, Ummkulthum Ahmad,Gt bank . evidence of payment through WhatsApp 08165992806

Wannan littafin bana baati bane,Zan bada fejika na baatin,Wanda take ko yake son cigaban shi se ya biya,farashi a group 150,naka Kai kadai 200..biya ze iya kasancewa a turo katin waya ko Kuma kudi ta banki,katin waya a kan Lamba 08165992806,ta banki ..0156213892.ummkulthum Ahmad
Shaidar biya ta WhatsApp a kan 08165992806.

Mairo,.. mairo" wato ba zaki yi da jiki ki fito kije gidan sadaqan nan ba ko, kiyi ki fito dan Allah kizo ki tafi, ko kin samu gaba gaba dan banaso ake shan ruwa ba tare da kun dawo gida ba, ga guri da dan tafiya"..

Inna dake tsakar gida ta chigaba da dan aikin da take yi, jin shiru har lokacin mairo bata fito bane yasa ta sake kwala kiran.... "Mairama" tare da fadin.. "In fa kika barni na shigo rumfar nan se na saba miki, haba, ayi mutum kaman man gyada, ke kenan kullum a kwance" se a lokacin wata yarinya ta fito tana gyara sakun Hijab dinta tana fadin" innar mu wallahi cikina ne ya matsamin, shi yasa na dan kwanta wai in ya dan lafa sai in tafi, kuma fa inna, na fadawa talan din Abuwa ta kama mun gaba da muka hadu a Rafi.. "

Inna ce tace " ke ni ba dogon zance na bida ba, ki wuce kiyi sauri ki tafi, kina nan kina raki, tun dazu Hasina ta kawo kunun gidan Alhaji Zakari, ta koma wani layin, ke ko kina nan.wuce maza,ciki kuma Allah ya sawwake ya baki lafiya, amma abun naki harda raki mairo.. "

Ki daure ki ruka kama jikin ki dan Allah, kina abu kamar ba mace ba,.. "
Cewa mero tayi"toh inna na tafi se na dawo, ayimun addu'ar nasara.. "

Addua'a inna ta fara  cikin nemawa yaran tah kariya, sannan mairo ta fita bayan ta dauki  dan mattaccen kwanon samira da wata robar ruwa wadda taji jiki sannan ta wuce gidan karban sadaqa, ga azumin ranan ba karamin garata yake ba,

ga ciwon cikin da ya matsa mata har ya zamo mata abokin rayuwa.

gashi anyi magani anyi magani amma har yanxu jiya i yau, kuma har a yau ba wanda yasan meya jawo shi ko kuma me yake jawo shin.

Hakan ne yasa ciwon ya zama jiki wasu inna, duk da inna na tausayin ta, amma bata so ta nuna mata karaya,

shi yasa duk sanda mairo ta fara zancen ciki, se inna ta nuna mata ai ba wani abu bane.

  WAI SHIN SU WAYE WA YANNAN BAYIN ALLAH???

SE A NEXT PAGE INSHA ALLAH .  ...

TBC..........

WATA KADDARAR ✅Where stories live. Discover now