MADUBIN GOBE 32.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.***
Kawu Muhammad sauraran bayanin Mami yake har ta gama ya sauƙe numfashi yana cewa.
"Sadiya anya Alhaji Mamman kan shi ɗaya."
"Ni ma ban sani ba Yaya Muhammadu, ni dai ga Nuratu dan Allah ta zauna zuwa nan da wani lokaci."
Mami tace ta ɓangaren ta."Shikenan amma kar ki damu, kinyi dabara da ki ka turo ta, sannan kar ki damu wannan lokaci ba zamu barshi ba."
Sun jima suna waya kafin ya kashe ya miƙawa Nuratu wayar ta karɓa ta shige ɗaki bayan dogon nasiha da Kawu Muhammadu ya mata akan kar ta damu komai zai wuce.
Da safe ƙarfe tara Dr Awwab ya shirya zai wuce, bayan ya yiwa su Kawu Muhammadu sallama tare da godiya suka ce sune da godiyar dawainiya da yayi da Nuratu. Har ƙofar gida suka suka rakoshi kowa ya koma ciki aka barshi da Nuratu.
Yana zaune cikin motar, ƙofar a buɗe Nuratu ta riƙe murfin motar, duk yanda ya so su haɗa ido ta ƙi yarda.
"Babyna."
Yace yana riƙe da wayarshi ya saita dai-dai fuskarta yana ɗaukar hotanta da bata ma san mai yake ba. Jin abin da ya faɗa yasa Nuratu haɗa rai ta watsa mishi harara.
"Ni ba Baby bace, bana so."
"To Babyn waye? Mami? Kin ma Mami girma. Babyna ce ke soon za ki yarda da hakan Noor."
"Ni dai ka gaishe da Hanan da Ummi sai anjima, Allah ya kiyaye hanya."
Tace ta rufe motar."Ameen Babyna za su ji."
Yace ya kunna motar yana barin gurin ta juya cikin gidan cike da kewa. Haka kawai ta ji kewar rashinsa kusa, yana sakata nishaɗi.Tana komawa gida wanka tayi ta kimtsa jikinta ta canza kaya ta ɗauki wayarta ta ƙira Col. Ahmad, yana shirin tafiya duk ya harhaɗa kayansa zai koma Ibadan ya samu ƙiranta suna tare da Umma tana mishi faɗan da har jiya ta kasa dai masa akan ya rabu da Nuratu ko ta ɓata masa rai, kuma aure ne ta bashi nan da sati biyu in ba haka ba zata aura masa ƴar uwarsa ƴar ƙanwar babanshi.
Col. Ahmad bayan ya gama sauraran faɗan Umma yace.
"Mami maganar gaskiya ba zan miki ƙarya ba bazan iya rabuwa da ita ba amma maganar aure na janye tsakanin mu da ita. Kallon ƙanwata nake mata Umma, abin a tausaya mata ne wallahi, tana buƙatar taimako da kulawan uba ko yaya, dan Allah kar ki rabani da ita. Maganar aure kuma na amince in har hakan zai saka ki yarda da ni."
"Ka amince har ranka, kuma ka min alƙawari ba zaka taɓa kawo min maganar auren wannan yarinya ba ko gaba, in har kayi hakan ka tabbatar zan nuna maka ni na haifa ka."
"Na amince Umma in har za ki barni in taimaki rayuwar Nuratu."
Col. Ahmad yace har cikin ranshi.
Shi ba wai auren bane baya so yawan canje-canje wajen aiki da yake samu ba zai iya yawo da iyalai ba. Rashin aurenshi da Nuratu ya riga ya amince cewa babu aure tsakaninsu sai dai wani ikon Allah. Ko kuma Alhaji Mamman ya janye kudirin shi na auren Mufid da Nuratu.
YOU ARE READING
MADUBIN GOBE
RomanceDuniyar Nuratu cike take da duhun da ta mamaye. Rayuwarta tafe take cikin damuwa da ƙaddarar da ta tsinci kanta. Ko yaushe za ta samu haske cikin duniyarta da rayuwarta? Waye gwanin da zai haskaka mata? Yaya Al-ameen? Col.Ahmad? Dr Awwab ko Mufid? ...