MADUBIN GOBE 9.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.....
"Ba zan hana Nuratu son Al-ameen ba haka ba zan hana Al-ameen auren Nuratu ba, domin na yarda da tarbiyyarshi da nutsuwar shi. Sai dai hanzari ba gudu ba dukkkan su karatu suke mai zai hana a bari su ƙarasa in yaso sai ayi maganar, sai yaje can Nijar ya samu Yaya Muhammad suyi magana."
Amma Jidda ta gamsu da maganarta kuma gaskiyar ta.
"Hakan ma yayi, dama shima cewa yayi a san da zaman shi ne amma zan ƙara tunatar dashi hakan.""Ba komai sai ya cigaba da neman amincewar Nuratu balle ma ina ga ta amince."
Da murmushi kan fuskar Amma Jidda tace.
"Yaran zamani sai dai muji labari a wajensu bamu san lokacin da suka haɗa kansu ba.""Wallahi fa."
Cewar Mami tana mamakin wannan lamarin, ko ba komai tayi farin ciki da Muhammad Al-ameen ya nemi auren Nuratu shi da yasan komai na rayuwarta tsakaninta da mahaifinta akan wani bare da watarana dole ya mata gori ba fata take ba.Suna cikin hira Nuratu ta dawo daga makaranta ta gaishe da Amma Jidda da taji wani kunyarta ya kamata daga gaisuwar ta wuce ɗakinta suka bita da kallo. Jin ana ƙiran sallar la'asar ya saka Amma Jidda yiwa Mami sallama ta tafi.
Da dare Mami da Nuratu suna zaune gaba ɗaya hankalinta a kan kallon da take Mami na mitar ta hanata kallon wa'azi da za'a gabatar, ganin an fita talla ya saka Nuratu kallon Mami.
"Mami ki saya min waya dan Allah, har Ameera tana da waya. Ni kaɗai ce bani dashi."
"Ki samu damar yin hira da saurayinki ko?"
Wani tashi zaune Nuratu tayi ta zauna tana duban Mami ta kasa magana.
"Kin saka min ido kamar zaki cinye ni, ba gaskiya bane. Wato har kun gama magana da Al-ameen baki sanar dani komai ba."
Kunya ne ya kama Nuratu ta kasa magana, wato dai Yaya Al-ameen dagaske yake har ya sanar da Amma dan ta san ita kaɗai ce zata sanar da Mami.
Ji tayi Mami tana cewa."Ba zan hanaki soyayya dashi ba ko aure, amma ina da burin kiyi karatu Nuratu ki samu ilimi mai amfani ki tsaya da kafafun ki."
"Kiyi hakuri Mami amma har yanzu ban faɗa mishi hukuncin dana yanke ba, zan sanar dashi yayi hakuri kawai in har hakan zai faranta miki rai, in yi karatu nima ina son hakan."
"A'a, bance ba. Jidda tamin abinda bani da abinda zan saka mata dashi sai aura miki ɗan ta. Ki sanar dashi kin amince in har kina son shi. Maganar waya ina sane dake cikin satin nan nake son saya miki dama."
Kan Nuratu ƙasa tace.
"Nagode Mami Allah ƙaro buɗi."Daga haka ta maida hankali kan tv a zahiri kallo take cikin zuciyarta kuma tunani take.
...
Haka kuwa a kayi cikin satin Mami ta harhaɗa kuɗaɗen bashin da take bin mutane ta bawa Nuratu tare da jagorancin Rukayya ta rakata ta siyo waya haɗe da gidan layi. Nuratu tayi murna sosai.
"Sai ki saka numbern Yaya Al-ameen ya daina damuna da ƙira dan jin lafiyarki."
Rukayya dake kwance ta faɗawa Nuratu haka yayin da take duba wayar Nuratu.
YOU ARE READING
MADUBIN GOBE
RomanceDuniyar Nuratu cike take da duhun da ta mamaye. Rayuwarta tafe take cikin damuwa da ƙaddarar da ta tsinci kanta. Ko yaushe za ta samu haske cikin duniyarta da rayuwarta? Waye gwanin da zai haskaka mata? Yaya Al-ameen? Col.Ahmad? Dr Awwab ko Mufid? ...