MADUBIN GOBE 17.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb."Idan har kuɗi yana danne gaskiya ya hana a kwatarwa mai haƙƙi gaskiyar shi to kuɗi zai saka a hukunta mai laifi. Dan haka mu zuba ni da kai."
Dariya Alhaji Kashim ya kwashe dashi ko a jikin shi yace.
"Who are you."Teburin gaban Alhaji Kashim ya dafa yana dubanshi.
"I'm Alhaji Mamman Bashir father of Nuratu Mamman Bashir. Wanda ɗanka ya ɓatawa rayuwa. Dan haka ka shirya shari'a.""Oh shikenan ina jiran ka."
Alhaji Kashim yace ko a jikinshi. Daga haka Alhaji Mamman ya fita a fusace.
Tun da Amma Jidda ta sanar dashi maganar kasa zaune yayi, tun yana son kawar da maganar ya ji ya kasa hakan. Duk da haushin Nuratu da na Hajiya Sadiya da yake ji amma abin da ya faru da ita yaji ya kasa hakura ko ba komai kwansa ce itama kamar sauran, rayuwa ne da ita har lokacin yake jin ba zai iya gida ɗaya ƙarƙashin inuwa ɗaya da ita ba, baya son duniya ta zageshi ya sashi saka kanshi cikin shari'ar.
Dole ya bincika wajen aikin Alhaji Kashim dan shaida mishi shirye yake ya kwatarwa ƴarshi haƙƙinta.***
Asibiti.
Da azahar Mami da Rahma suka hau shirin tafiya Maiduguri bayan sun sanar da Dr Sadiq ya basu copy na komai dangane da rashin lafiyar Nuratu da abin da ya jawo hakan har zuwa yanzu da babu wani canji.
Rahma ce kawai za ta raka Mami, ta sanar da mijinta ya amince ta shirya ita da Babynta. Sauran duk sai sun isa za su bi bayansu daga baya. Hasiya taso zuwa mijinta ya hanata cewa sai ta warke zuwa nan da kwana biyu.Ƙarfe uku su ka ɗauki hanya cikin motar asibiti da Dr Sadiq ya basu. Nuratu alluran bacci aka mata dan karta farka musu a hanya.
Isan su kai tsaya asibitin Asylums suka isa kasancewar an san da zuwansu aka tare su, Dr Awwab da aka sanar da zuwansu ya dubata aka bata ɗaki.
Bincike sosai yayi a foldern ta da ita kanta kafin ya samu zama da su Mami."InshaAllah zata samu sauƙi, firgicin da ta shiga ya haifar mata da haka. Amma sannu a hankali komai zai wuce. Daga gobe zamu fara ɗaurata saman magani in ta farka, babu batun alluran bacci sai dai zuwa dare dan ta samu bacci. Muna so mu ga yanayin yadda sauƙin zai samu."
"Nagode Dr. Allah biya ka."
Mami tace tana sharan hawaye.Murmushin sa mai kyau yayi duk da abinda ya samu Nuratu yana jin shi a zuciyar shi dan ya taɓa masa zuciya ba kaɗan ba, tausayinta ya cika masa zuciya.
"Babu komai. Mu ci-gaba da addu'a."Daga haka suka koma ɗakin da Nuratu take babu kowa, tsakanin su da ita akwai gilashi suna ganin komai na ciki. Tana kwance kamar kullum cikin bacci ba ta motsi sai in har alluran ya saketa. Kuɗaɗen Mami na hannunta duk ya ƙare dan kafin ta zo ma sai da ta saida ɗan kunnenta mai tsada ta samu suka taho.
Burinta kawai Allah tashi kafaɗar Nuratu ta samu lafiya, maganar hukunci da shari'a duk bai dameta ba, burinta lafiyar ƴarta. Ta manta rabonta da taci abinci kwakkwara sai kunu shima sai an matsa mata.Hira sama sama Rahma take mata tana sanar da ita kyan asibitin da kuma halin Dr Awwab da ta kula ya san kan aikin shi, hiran ne ya ja lokacin har aka ƙira magriba suka gabatar da sallah. Sai da Mami tayi kafin ta riƙewa Rahma ƴarta mai shegen ƙiwa kafin itama tayi.
Cikin daren ƙarfe goma Nuratu ta farka, Mami da Rahma suka rirriƙeta suka kai ta bathroom, Mami ta sakata cikin ruwan zafi sai bugesu take tana ture su. Haka suka fito da ita suka canza mata kaya kafin Nurse ta mata allura wani bacci ya ɗauketa suka samu suma suka kwanta.
YOU ARE READING
MADUBIN GOBE
RomanceDuniyar Nuratu cike take da duhun da ta mamaye. Rayuwarta tafe take cikin damuwa da ƙaddarar da ta tsinci kanta. Ko yaushe za ta samu haske cikin duniyarta da rayuwarta? Waye gwanin da zai haskaka mata? Yaya Al-ameen? Col.Ahmad? Dr Awwab ko Mufid? ...