MADUBIN GOBE (Haske) 50.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.***
"Wai yau ba za kaje gaishe da Ummi ba ne?"
Murmushi Dr Awwab yayi yana bin Nuratu da kallo yayin da take kwashe kayan da su kayi breakfast, ta masa wannan tambayar.
"Yau kallonki zanyi ta yi, babu inda zan je."
Murmushi Nuratu tayi tana tura baki ta wuce kitchen ta barsa zaune, fara wanke kwanukan tayi ta ji shigowarsa, juyawa tayi ta kalli bakin ƙofar yana tsaye ya zuba mata ido, kanta ta ɗauke, wannan kallon dai yau ya fara takura mata.
'Mutum ko motsi yayi idonsa a kanka.'
Ta faɗa cikin ranta tana tura bski gaba.Ganin ta juya ya saka Dr Awwab ƙarasawa inda take tsaye. Tana jinsa dalilin ƙamshin turarensa da ya ƙara ƙarfi yake shiga kofofin hancinta.
Ba zato ta ji ya rumgumeta ta baya tare da saka hannuwansa ya riƙe kugunta, hakan ya hana Nuratu ci gaba da aikinta ta dakata, yaar taji tare da wani sabon abu yana bin jinin jikinta. Idanuwanta ta lumshe ta buɗe cike da shauƙi da bata san ya ɗebeta ba. Baya tayi ta kwantar ksnta sanan kirjinsa."Zan je wajen Ummi me zan faɗama ta."
Ta tsinci muryar Dr Awwab yana mata magana daf da kunnuwanta. Sake lumshe idanuwanta tayi ta buɗe murya can kasan makogoro tace."Ka gaisheta, ka taho min da Hanan."
"Ok My Sweet Baby."
Dr Awwab yace bayan ya ba ta kiss a tsakanin wuyanta ya saketa, dukkansu biyun suka sauƙe ajiyar zuciya a tare. Kasa tsayuwa Nuratu tayi ta dafa sink tana jinsa ya fita. Ta rasa me yasa duk lokacin da ya mata haka neman nutsuwar ta take ta rasa. Da kyar ta daidaita nutsuwarta ta ci gaba da aikinta tana maganganun zuci.
In ance za tayi sure ta samu farin ciki a rayuwarta baza ta taɓa yarda ba. Ta san dai bata son Dr Awwab a kayi aurensu ko tace ba ta da masaniyar hakan, amma gaba ɗaya ya fara canza mata ra'ayin zuciyarta. Ba ta taɓa tsammanin irin karɓar da Dr Awwab zai mata ba kenan a matsayinta na matarsa, shi yasa take tsoron kasancewa matar aure a rayuwarta. Ita ko da mai za ta saka masa bayan ta basa farin ciki kamar yadda yake sakata, ta basa komai da ta mallaka.
...
Gidan Ummi kai tsaye Dr Awwab ya wuce dan gaishe da ita ya kuma ga ƴarshi. Falon shuru ƴan biki sun watse kowa ya tafi. Sallama yayi har sau biyu kafin Hussaina ta amsa ta fito a kitchen.
"Babu kowa ne?"
Ya tambayeta bayan ya amsa gaisuwarta."Ummi tana ɗaki."
"Ina My Love?"
Da mamaki Hussaina tace.
"Hanan?""Eh ko tana tare da Hassana."
Tsoro ne ya ziyarci zuciyar Hussaina ganin ya juyo gaba ɗaya da hankalinsa kanta, ya kafeta da idanuwansa masu tsoratasu. Masu hana ƴan mata rashin juran gani.
"Ke nake tambaya?"
Dr Awwab yace yana haɗa giran sama da ƙasa ganin kamar bata da gaskiya.Hussaina da idanuwanta sun cika da hawaye da ƙyar ta buɗe baki tace.
"Ba tana gidanka ba. Aunti Binta ta ɗauketa da kayanta jiya tace za ta kaita gurinka."
YOU ARE READING
MADUBIN GOBE
RomanceDuniyar Nuratu cike take da duhun da ta mamaye. Rayuwarta tafe take cikin damuwa da ƙaddarar da ta tsinci kanta. Ko yaushe za ta samu haske cikin duniyarta da rayuwarta? Waye gwanin da zai haskaka mata? Yaya Al-ameen? Col.Ahmad? Dr Awwab ko Mufid? ...