MADUBIN GOBE 33.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.***
Da safiyar ranar Alhamis bayan Alhaji Inuwa ya gama abin da zai yi kamar ƙarfe goma ya aika Hajiya Maimuna ƙiran Mami da ta shirya tana zaune da zaran sun gama magana ta koma.
Bayan sun isa ta gaishesa ya ɗauki waya ya ƙira ƙanin shi Alhaji Mamman da sai su yi wata ba su yi waya ba sai idan shi ya ƙira, gani yake ko dan ya fishi arziki.
Ya jima yana ƙara bai ɗauka har ya kusa tsinkewa kafin ya ɗauka da sallama. Bayan sun gaisa yake cewa."Mamman ina buƙatar mu yi wani magana in har kana da lokaci, maganar mai muhimmanci ne, da son samu ne ma zan shigo Damaturu amma abin gaggawa ne."
"Ina da shi Yaya Inuwa, ka sanar dani menene. Wani abun ya faru?"
Alhaji Mamman yace ta ɓangaren shi jin maganar yayan shi."Labari na ji ko in ce dagaske ne ka bayar da auren Nuratu ga wannan yaron Mufid?"
"Eh hakane babu maganar ƙarya."
Alhaji Mamman yace ranshi ya fara ɓaci jin maganar da ya zo masa dashi yana mamakin ina ya samu labari."Amma Mamman kana tsoron Allah? Kana tsoron ranar da Allah zai tuhume ka da haƙƙin yarinyar nan. Yanzu abin naka har ya kai ka ɗauki aurenta ka bada ba tare da izinin mahaifiyarta ba wacce tasha wahalarta tun haihuwarta har girmanta. Ina laifin a mutumin kirki ne tun da dole sai an zo wajen ka neman aurenta amma sai wancan banzan yaron."
Sai da ya gama sauraron shi har ya gama kafin yace.
"Kayi hakuri Yaya amma yarinya ƴata ce ko?""Eh ƴarka ce?"
"To kayi hakuri ka fita cikin maganar nan dan Allah ina ganin girman ka. Ita Sadiyar ta ƙira ta faɗa maka, to ka sanar da ita babu fashi domin aure tamkar an yi an gama. Sai anjima ka gaishe da yaran."
Daga haka ya kashe wayar shi cike da jin haushin Nuratu da Mami.Jin ya kashe Alhaji Inuwa ya ajiye wayar cike da taƙaici.
"Kin ji mai ya faɗa Sadiya ko. Mamman ya canza, dama haka yake amma yanzu kwata kwata ya sake canzawa. Mutanen nan ba a banza suka barshi ba Sadiya. Kuyi magana da Nuratu ta turo yaron da take so zan samu Mamman za ayi abu ɗaya."
Mami da kanta ke ƙasa hawaye ya taru a idonta jin har lokacin Alhaji Mamman ya kasa janye kudurin shi ta ɗago kanta.
"Alhaji har yanzu babu aure a cikin ranta tun abin da ya faru, tana da wanda suke sonta, amma yanzu na san dole ta zaɓi ɗaya cikinsu.""To ki sanar da ita ta turo ɗaya cikinsu wanda ya kwanta mata a rai, ni zan gama komai. Zan nunawa Mamman ina da iko a kanshi, ko shari'a ce shi zai wahala domin tauyewa yarinyar nan haƙƙinta."
"Ba ta nan tana Nijar wajen Yayana tsoron auren ya sa na tura ta can."
"Au to shikenan ki sanar da Yayanki ku yi magana ɗaya cikin gaggawa. Ku sanar da ni duk abin da kuka yanke."
"To nagode Alhaji."
Mami tace ta miƙe tana mishi godiya.
Bayan fitarta ya tura Hajiya Maimuna da dubu goma ta bata tayi kuɗin mota, da kyar ta karɓa, ta saka yaron su babba ya kaita tasha ta hau mota.***
DAMATURU.
Bayan gama wayarsu Alhaji Mamman faɗa ya hau yi sosai cikin gidan Amma Jidda na bashi hakuri da bata san kan zancen ba har sai da ya sauƙo ta tambayeshi da ta gwanmace bata tambaya ba dan amsar da ya bata.
ESTÁS LEYENDO
MADUBIN GOBE
RomanceDuniyar Nuratu cike take da duhun da ta mamaye. Rayuwarta tafe take cikin damuwa da ƙaddarar da ta tsinci kanta. Ko yaushe za ta samu haske cikin duniyarta da rayuwarta? Waye gwanin da zai haskaka mata? Yaya Al-ameen? Col.Ahmad? Dr Awwab ko Mufid? ...