MADUBIN GOBE 22.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.***
Shirin kayansa yayi tsaf ya fito da akwatin shi, Umma ta bishi da kallo.
"Ina kuma zuwa da kaya haka? Ko hutun ya kare ne?"
Col. Ahmad da ya zaune saman kujera yace.
"Umma ya ƙare zan tafi an neme ni. Amma ba zan jima ba zan dawo bai fi in yi sati biyu ba. Ki mini addu'a akwai yaƙin da nake son cimma nasara a kai."
"Allah baka sa'a ya dawo da kai lafiya."
Ameen ya amsa dashi ya tashi ya fita direba ya kai shi har airport ya bi jirgi zuwa Ibadan.
***
"Amma ni fa har yanzu ina kan bakana."
"Na me kuma?"
Amma Jidda ta tambayi Al'ameen duk da ta fahimci akan mai yake magana.
Kai tsaye yace.
"Na auren Nuratu.""Ni dai ba zan hanaka auren Nuratu ba, amma da ka bari zuwa wani lokaci kaɗan, yaushe ma ta samu lafiya?"
Ya san hakan amma dai so yake a san har yanzu yana nan akan bakarshi na son aurenta babu abinda ya canza wai dan ƙaddara ya faɗa rayuwarta.
"Shikenan Amma zan ba ta lokaci, amma ba mai tsayi ba."
....
Tun ranar da su Nuratu suka dawo ba ta fita ko nan da ƙofar gida, daga falo sai ɗaki, tsoron fita take, duk bayan kwana biyu sai yayunta sun zo dubata tana jin daɗin haka. Magungunanta baya wuce lokaci take sha akai akai da hakan yana mutuƙar taimaka mata, maganar makaranta ta jinginar shi a gefe ba yanzu ba.
Yau suka samu baƙoncin Rukayya da Walida, gidan ya mata daɗi. Mami ta fita sarin kaya da ɗan kuɗaɗen hannunta da suka rage dan duk ta cinye jarin a jinyar Nuratu dan ma tana samun taimako daga ƴaƴanta da mutane.
Har dare kafin suka tafi, da daren Mami na duba kayan data saro Nuratu na gefe tana gani har ta nuna wani atamfa da ya mata kyau, Mami tace ta ɗauka ta ba ta.
Godiya tayi ta ajiye a gefe tana kallon Mami."Mami ina son miki wani magana, sai dai ban san ya za ki ɗauka ba."
"Ina sauraronki."
Mami tace taci gaba da duba kayanta."Ina son shigar da ƙara, ina son kwatar haƙƙina. Ina son ɗaukar fansa bisa abinda aka min."
Kallonta Mami tayi ta hango tsantsan buƙatar hakan a fuskarta. Numfashi ta sauƙe.
"Kina ganin hakan mai yiwa ne? Ko kin shirya yaƙi da masu hannu da shuni? Ko kina da wani wanda zai tsaya miki ya taimaka miki ya kwatar miki haƙƙin ki. Ko kina da kuɗaɗen da za ki shigar dan samun nasara. Zamani ya canza Nuratu, masu kuɗi ba'a hukunta su, duk abinda suka aikata komin munin shi rufewa ake. Kai talaka in an cuce ka sai dai ka ɗauki hakuri ka kai kukan ka wajen Allah. Cuta an riga an cuce mu an cuci rayuwar ki, bamu da ikon ɗaukar hukunci. Allah kaɗai zai saka miki."
YOU ARE READING
MADUBIN GOBE
RomanceDuniyar Nuratu cike take da duhun da ta mamaye. Rayuwarta tafe take cikin damuwa da ƙaddarar da ta tsinci kanta. Ko yaushe za ta samu haske cikin duniyarta da rayuwarta? Waye gwanin da zai haskaka mata? Yaya Al-ameen? Col.Ahmad? Dr Awwab ko Mufid? ...