MADUBIN GOBE (Haske) 49.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.***
Har ya gama bayaninsa yana sauraranshi tsaf, bayan ya gama ya sake dubanshi, kansa a ƙasa, numfashi ya sauƙe yace.
"Amma Mamman idonka babu kunya? Duk abin da ka aikata har zaka iya buɗe baki ka faɗi haka ko neman buƙatar haka daga gurinta."
"Yaya ka taya ni addu'a, sannan kai ma ina buƙatar taimakon ka."
Alhaji Mamman yace yana ƙara yin ƙasa da kansa.Jinjina kai Alhaji Inuwa yayi yana cewa.
"Allah yasa ta amince. Amma a jikina nake jin babu nasara a wannan buƙatar ka."Miƙewa tsaye Alhaji Mamman yayi yana cewa.
"Zan wuce Yaya a gaishe min da yarana. Zan yi latti."Daga nan su kayi sallama Alhaji Mamman ya kama hanya, zuciyarshi fes yake ji domin ji yake buƙatarshi kamar ya biya. Burinsa na farko ya cika, saura wannan da yake fatan shima ya cika, kafin na gaba dan sai na biyun ya cika kafin na ukun.
***
"Mene ne hakan Docter?"
Nuratu tace tana ja baya tare da buɗe ido ɗaya tana kallon Dr Awwab. Shigar da ita jikinshi yayi sosai tare da riƙo fuskarta da hannunshi, ta runtse idanuwanta da ƙarfi. Sumbatar saman hancinta yayi yace.
"Inyi kissing ɗin bakinki?"Girgiza kai tayi tana buɗe idanunta da sauri, mamakin rashin kunyar Dr Awwab take,kai tsaye yake faɗa mata abu babu maganar jin kunya. Shima girgiza kai yayi yana murmushi yace.
"Ko bakya so sai na yi.""Ni dai a'a."
Tace har lokacin idanuwanta rufe, hakan yasa ya ɗaura yatsansa saman leɓɓenta ya fara zagayewa, taushi gare su. Bai mata magana ba sai jin sauƙar nashi leɓɓan tayi saman nata ya fara kissing ɗinta. Da kansa ya saketa domin Nuratu ta kasa hanashi.
Fuskarta ya riƙo har lokacin idanuwanta rufe yace."Buɗe idonki."
Ƙi tayi ta girgiza kai, jikinta na rawa. Ganin haka Dr Awwab yace.
"Shikenan bari in sake bai isheki ba."Da sauri ta buɗe idanunta suka sauƙa cikin nashi da suka ƙara ƙanƙancewa da fitina, ya ɗaga mata gira tare da jifanta da murmushin da yake hanata kallon cikin idanuwanshi. Da sauri ta ɗauke kanta tana juyarwa gefe. Sakinta yayi yana murmushi. Tashi tayi da sauri ta shige kitchen dan nan tafi kusa da shi.
Jingina tayi jikin ƙofar kitchen ɗin tana lumshe idanuwanta tare da dafe kirjinta dake bugawa tamkar yanzu yake mata abubuwanshi.Dr Awwab kan saka zuciyarta da kanta cikin wani shauƙi da nutsuwa duk lokacin da suka kasance tare, Yanzu kam jin abin da yake mata take har cikin kahon ranta, wani farin ciki na shiga kofofin jinin jikinta da zuciyarta. Murmushin da bata san daga ina yake ba ta yi, sai dai tasan zuciyarta na farin ciki. Jin maganarshi tayi da ya ankarar da ita, in da yake sanar da ita zai fita sai anyi sallah zai dawo.
Kanta ta saita kafin ta fara ƙoƙarin ɗaura abincin rana. Tsaf ta gama haɗawa ta jera a saman dinning table tana wucewa ɗakinta, sallah tayi ta sauko ƙasa ta ɗauki wayarta ta ƙira Aunti Rahma da su Hasiya. Kowa dai in ya buɗe bakinsa cewa yake ta cire komai a ranta ta riƙe mijinta sannan taci gaba da gyara kanta, dan duk kwalliyar mace da kyau sai ta ƙara da wanka. Da to ta bisu ƙarshe ta ƙira Walida suka sha hiransu, Walida tana tsokanar ta kafin ta kashe ba tayi gigin ƙiran Ameera ba.
Haƙurin nan dai za tayisa dan ganin ribarsa. Babu shskka zuciyarta ya fara amincewa da Dr zai bata dukkan farin cikin da take tsoron rasawa. Wanka tayi ta zuba kwalliya cikin doguwar riga sai ƙamshi turare ke ta shi a jikinta.
ČTEŠ
MADUBIN GOBE
RomanceDuniyar Nuratu cike take da duhun da ta mamaye. Rayuwarta tafe take cikin damuwa da ƙaddarar da ta tsinci kanta. Ko yaushe za ta samu haske cikin duniyarta da rayuwarta? Waye gwanin da zai haskaka mata? Yaya Al-ameen? Col.Ahmad? Dr Awwab ko Mufid? ...