61.

1.3K 126 9
                                    

MADUBIN GOBE  61.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

GANGARA.

***

Abdallah ne ya soma magana bayan kowa ya baza kunnuwa don jin wannan sarƙaƙiyar. Gyaran murya ya yi kafin ya soma da cewa.

"Tsawon shekaru huɗu kenan. Watarana da yamma ina zaune Yaya Awwab ya zo ya same ni har makaranta, nayi mamakin ganinsa a lokacin saboda bamu cika haɗuwa ba sai irin a biki ko a sallah idan ya zo gidanmu, ko idan mun je na su.
Bayan mun gaisa na basa gurin zama, anan ya dubeni ya ce.
"Abdallah naga abin da ya bani mamaki yau, naga abin da ya birkita tunanina da ƙwaƙwalwata, na kasa tunani na kasa gano komai balle samun haske, na rasa wa zan tunkura in sanar balle ya taimaka mini sai kai."

Dubansa nayi yadda yake cikin damuwa, ni ma cike da damuwar dan maganganun sa sun rikitani na ce.
"Yaya Awwab me ya faru? Na kasa gane maganganun ka, na kasa fahimtar su ko sanin ina su ka dosa."

Kallona ya yi a karo na biyu ya ce.
"Shin Baffa ya taɓa sanar da kai suna da wasu ƴan uwa bayan Babban Yayan su Alhaji Yousufa?"

Tambayar da ya min shi ya ƙara dilmaye ƙwaƙwalwata, sai girgiza masa kai da nayi alamar a'a. Numfashi ya sauƙe ya miƙe tare da fara zagaye cikin ofishin da muke zaune. Ni dai kawai idanu na saka masa dan na rasa bakin magana. Haka ya ci gaba da yi tsawon lokaci kafin ya dafa teburin da nake zaune.
Tamkar ba zai ce komai ba ya ɗago ya dube ni da idanuwansa da su ka canza launi.

"Abdallah naga mai kama da iyayenmu, ba kuma namiji ba mace, babbar mace, in taƙaita maka hatta ƴarta babba tana kama da ƴar uwarka Sumayya."

"Kama kuma? Kamar ma da iyayenmu kuma mace?"
Na tambayesa da mamaki.

Kai ya ɗaga mini yana cewa.
"Tabbas hakane Abdallah. Marar lafiya aka kawomin kwana biyu da ya wuce, ƙwaƙwalwarta ya samu matsala. Wallahi farin ganin babbar ƴar matar na ɗauka Sumayya ce, amma da na ji sunan da aka ƙirata da shi sai na tabbatar ba ita bace. Sannan matar ita da su Abba bambancin su kawai ita macece sai ƙarancin shekaru. Hatta ita marar lafiyar tana kama da su."

...

Shuru Abdallah ya yi yana neman guri ya zauna don ya gaji da tsayuwar. Falon tamkar anyi ruwan sama an ɗauke, babu mai iya kwakkwaran motsi sai idanu da suke bin juna da shi cike da mamaki da son fassara kalaman Abdallah.
Bayan zamansa ya ci gaba da cewa...

"Ban san me yasa ya zaɓi ya faɗamin ba. Ban san me yasa ni ƙarami a cikinsu ba kuma ya zaɓe ni. Ban yarda da zantukan sa ba a lokacin haka muka rabu.
Sai dai abun mamaki bayan lokacin Yaya Awwab ya ci gaba da kawomin bayanai akan waɗannan mutane har Allah ya sa watarana na kai masa ziyara asibiti na gansu da idanuna. Tabbas na shiga rudu, sai dai Yaya Awwab ya nunamin kar mu tono maganar ko mu tunkari wani da shi a cikin iyayenmu sai wani burinsa ya cika.
To allahamdulillahi bayan aurensa da Noor mu ka dinga samun ƙarin haske. Misalin ganin Ammi da ta yi ma Aunti Rahma da ita kanta Mamin da kuma Muhsin. Ammi tafi nuna damuwarta a kan Ummi. Na yi ta bibiyarta ta sanar dani damuwarta duk da na fahimci akan menene amma ta ƙi. Anan kuma burin mu idan ta sanar da ni sai in sanar da ita ga yadda abun yake, sai mu tunkari Abba da maganar kamar yadda muka tsara da Yaya Awwab, amma ƙarshema dai ta ƙi maganar gaba ɗaya ta watsar. Hakan ya sa Yaya Awwab neman sabuwar hanya."

Daga haka ya yi shuru yana sauƙe numfashi, ruwa ya tsiyaya yasha ya kalli Dr Awwab ya marairaice masa.
"Yaya ka ƙarasar musu ni na gaji."

MADUBIN GOBEWhere stories live. Discover now