42.

1.1K 129 13
                                    

MADUBIN GOBE  42.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

....

"Babyna shine babu ƙira ki tambaye ni na isa lafiya."
Dr Awwab yace jin Nuratu ta ɗauka tayi shuru.

Kamar ba za tace komai ba ƙasa ƙasa tace.
"Ya hanya? Ina Hanan?"

"Allahamdulillahi lafiyarta ƙalau. Me ki ka cewa Mami da ta tambayeki ina ki ka je?"

"Babu komai."

"Sai ki sanar da ita mijinki ya ɗauke ki kun fita."
Yace yana murmushin da take jin sautin shi.

"Ni dai sai anjima, bacci zan yi."
Nuratu tace da sauri ya dakatar da ita.

"Wayo za ki mini dai. To ki yi bacci lafiya sai da safe."

Kit ta kashe wayar ta ajiye tana sauƙe numfashi, ji take kamar yau suka soma waya da shi, dan jin yanda numfashinta yake riƙewa kamar budurwar da take hira da saurayin da ta mutu a son shi da ko muryarshi ta ji sai jinin jikinta ya tsaya.

***

New Delhi.

Ɓangaren Mufid yana samun dukkan kulawar da ya kamata a bashi daga Ummu da likitoci, jikin shi yayi sauƙi har ya fara wasu abubuwa da kanshi. Daddy kuɗaɗen hannunshi duk ya ƙare burin shi su cika sati uku a sallamesu. Can gida yayi waya a turo masa kuɗi, an sai da motar Mufid da nashi ɗaya an haɗa an turo shima ya kusa ƙarewa.

Cikin ikon Allah Mufid tun farkawar shi bai ƙara musu maganar Nuratu ba, hakan ya yiwa Ummu da Daddy daɗi, na shi bangaren kuwa har lokacin da tunaninta yake kwana yake tashi. Duk da ya san zuwa yanzu ta masa nisa ta zama matar wani ya san abu ne mai wahala ya cireta a ranshi. Wahalar da ya sha ganin ya kusa mutuwa ya sashi jin tsoron Allah da duniya ta shigesa. Ya cire komai na harkar barikanci a ranshi, yaji komai ya fice masa a rai.

Burin shi ya koma gida ya nemi yafiyar duk mutanen da ya zalunta ko zai samu rahamar Allah. Bashi da aiki kullum sai zama cikin tunanin rayuwar da ya gudanar da babu komai na khairi sai lalaci da hakan yake saka shi nadama sosai.
Shuru shurun da ya zama shi yafi damun Ummu, take cewa ko dai bashi da lafiya, ya nuna mata lafiyar shi lau kawai hayaniya ne baya so.

***

DAMATURU.

Ranar wata alhamis karfe taran safe Alhaji Mamman ya shirya bayan ya yi breakfast ya miƙe yana kallon Amma Jidda.

"Zan leƙa kasuwa in dawo. Ki shirya za ki min rakiya in na dawo."

"To a dawo lafiya."

Amma Jidda tace ta miƙe ta tattara wajen ta koma ɗaki. Ameera ce ta shigo ta mata sallama za ta wuce makaranta ta ciro ɗari biyar ta bata.

"Gashi kiyi kuɗin mashin, har yanzu Abban ku bai samu kuɗi ya gyara wancan motar ba."

"Amma, Amma ya haka dan Allah yau fa wajen sati biyu mashin nake hawa."

Fuska Amma Jidda ta ɗaure tana duban Ameera.

"Eh sai aka yi ya? Ke da fa ba yanzu bane komai ya lalace sai addu'a. Kina ganin dai abubuwan da suke faruwa a gidan nan. Abban ku bashi da aikin yi sai kasuwanci da yanzu shima ba tafiya yake ba."

MADUBIN GOBEWo Geschichten leben. Entdecke jetzt