MADUBIN GOBE 35.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
....
Da safiyar ranar asabar ƙarfe goma dai-dai Alhaji Inuwa ya samu ƙiran Dr Awwab da mutanen shi sun iso. Tun daren jiya ya iso gidan Alhaji Mamman zaton Alhaji Mamman duk dan auren Nuratu da Mufid da za'a ɗaura ne safiyar gobe.Gidan duk ya cika da mutane abokan Alhaji Mamman da ya gayyato su dan zuwa shaida ɗaurin auren Nuratu da Mufid.
Alhaji Inuwa na zsune yana duba agogo burin shi Dr Awwab ya ƙira shi kar lokaci ya ƙure musu kamar yadda suka ɗiba ya samu ƙiran da shigowar su kenan. Cikin sauri ya ɗauka ya musu kwatancen gidan kafin ya koma ya samu ana haɗa haɗar ɗaura aure Alhaji Kashim ya iso da nashi mutanen. Ciki har da Mufid da yasha bakin yadi da ya amsa sunanshi dan kuɗi da aka zuba aka kwashi kayan, yayi kyau sosai kamar ba ɗan shaye-shaye Mufid ba, dan ma daren jiya sai da su kayi tatil dakyar yau ya samu ya farka ya shirya ya taho sai washe baki yake Faisal da AA suna mara mishi baya.
Alhaji Inuwa da ya iso yana jiransu Dr Awwab ya dubi ƙaninshin Alhaji Mamman yace.
"Mamman ka ɗan ban lokaci akwai bakina da za su iso cikin ƙanƙanin lokaci."Ganin idon jama'a da kuma yayan shi ne ya sashi cewa.
"Shikenan Yaya amma suyi sauri, mahaifin yaron nan sun iso tun ɗazu."Sallamar Alhaji Abubakar ne da mutanen shi ya hana Alhaji Inuwa magana ya tashi ya tare su suka ƙaraso cikin babban falon da yake cike da mutanen da za su shaida auren. Dr Awwab da yayan mahaifinshi Alhaji Abubakar da abokinsa ɗaya da abokin marigayi Alhaji AbdulRamat mahaifi ga Dr Awwab su huɗu.
Alhaji Mamman da Alhaji Abubakar kallon kallo su kayi a junansu, Alhaji Mamman na tunanin ina ya san malallakiyar fuska mai irin nashi. Zuciyarshi ya kasa bashi macece ko namiji? Babba ne ko yaro?."Ga baƙina. Bismillah Docter ku zauna."
Alhaji Inuwa yace yana nuna musu kusa da Alhaji Mamman suka zauna tare da gaishe da mutanen wajen alhazzai masu ruwan kuɗi abokai ga Alhaji Kashim da su kazo shaida ɗaurin auren tilon ɗan sa.Mufid ido kawai ya sakawa Dr Awwab cikin bakin gilashin da ke manne a idanun shi, ya gane shi shekaru huɗu da suka wuce shine Docter da ya bada shaida a kotu shi ya kula da Nuratu bayan barinsu nan. Dole ya masa godiya in an gama ɗaurin auren shi da Baby Noor.
Dr Awwab yayi kyau cikin farin yadin da ɗinkin ya zauna a jikin shi, hula da yake saman kanshi da farin gilashin dake manne a idonshi ya fitar da kyan kyakkyawar fuskarshi. Fuskarshi ba zaka bambance wani yanayi yake ciki ba, babu fara'a kuma ba'a haɗe ba.
"Ayi shuru za'a fara gudanar da ɗaurin aure."
Faɗin mutane masu roƙo dan samun nutsuwar mutanen gurin. Tuni guri ya ɗau shuru kowa ya zuba kunne.Gefe ɗaya Alhaji Inuwa da Dr Awwab da yake kusa da Alhaji Mamman ta damanshi, gefe ɗaya kuma Alhaji Kashim da yake hannun hagunshi dasu Mufid.
"Mamman."
Alhaji Inuwa ya ƙira sunan shi da ya saka gurin gaba ɗaya sauraron mai zai faɗa har shi kansa Alhaji Mamman ɗin ya amsa."Mamman ka ɗauke ni matsayin uba kamar yadda mahaifin mu ya faɗa maka kafin rasuwar shi ka ɗauke ni tamkar shi, ka min biyayya kar ka saɓa umarni na, in har ka saɓa hakan to ka tabbata yana fushi da kai haka Mama ma maganarta na ƙarshe a duniya in za ka tuna."
"Yaya mai ya kawo maganar nan ana cikin shirin ɗaura aure."
Alhaji Mamman yace ƙasa ƙasa da wanda suke kusa duk sun ji kasancewar falon an yi shuru.
ČTEŠ
MADUBIN GOBE
RomanceDuniyar Nuratu cike take da duhun da ta mamaye. Rayuwarta tafe take cikin damuwa da ƙaddarar da ta tsinci kanta. Ko yaushe za ta samu haske cikin duniyarta da rayuwarta? Waye gwanin da zai haskaka mata? Yaya Al-ameen? Col.Ahmad? Dr Awwab ko Mufid? ...