MADUBIN GOBE 6.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.Gidan Alhaji Mamman Bashir.
Da dare Alhaji Mamman ya samu labarin zuwan yaran gurin Mami Sadiya, faɗa yayi ta yiwa Amma Jidda da abin ya ɓata mamaki, har tana cewa.
"To wai naga mahaifiyarsu ce, ta ya za ka rabasu, duk yadda kayi fa ɗa baya gudun mahaifiyar shi."
"To ki kiyaye ni, na faɗa miki kar ki ƙara kai su tun da ita ta ƙi bin shawarar da na yanke ta rabu da su." Ya ce cikin faɗa.
Shuru kawai ta mishi tana juyar kanta, haushin maganganun shi take ji. Sannan ƙasan ranta tana son sanin menene Alhaji Mamman ya nema Mami Sadiya ta ƙi yi har take ganin gwara ta bar yaranta.
...Fushin kwana biyu yayi ya sauƙo don tace ba za ta sake kai su ba, amma tasan ƙarya ta mishi kawai don ya daina fushi da ita.
....
Tun daga ranar Amma Jidda a ɓoye take kai yaran gurin Mamin su shima sai a hutun ƙarshen mako. Sannan ta gargade su kar su ƙara sanar da Abban su.
Mami Sadiya tana jin daɗin haka don yana ƙara mata shaƙuwa da yaranta, haka kuma da yar uwar su Nuratu da in ta gansu ta dinga miƙa hannu su ɗauketa don ta gane su.
Mami Sadiya tana ƙoƙarin kyautata Amma Jidda dan yadda ta riƙe mata ƴaƴa, kullum sai ta mata godiya sai dai Mami Sadiya tayi murmushi tace ta daina gode mata."To wai so kike duniya ta zage ni ace na raba uwa da ƴaƴanta, a'a ni kam bana so gwara ki zama shaidana ko da an zage ni."
Murmushi kawai Mami tayi tace.
"Bama mai zagin ki sai yabon ki."Aunti Zarah da ta samu labari itama tayi farin ciki tana yabawa Amma Jidda dan da wuya a samu matar uba mai irin halinta.
A cikin haka Amma Jidda ta haifi ƴarta nace mai sunan mahaifiyarta tana ƙiranta Walida****
Bayan shekaru goma.
Abubuwa da yawa sun faru cikin rayuwar su da suka saka shi cikin kundin Ƙaddarar su.
Yara sun girma su Rahma sun girma shekara goma sha huɗu ba wasa ba, Hasiya mai bi mata da ita suna aji uku na sakandare, Muhsin yana ajin ƙarshe na Firamare sai Nuratu da Walida ajinsu ɗaya suna aji huɗu sai Rukayya data fi su da aji tana aji biyar, Muhammad Al-ameen ya wuce makarantar gaba da sakandare wato digiri a garin Zaria wajen dangin mahaifin shi da yake zama a can gaba ɗaya ya koma.Tun lokacin da Nuratu ta isa shiga makaranta Amma Jidda ta haɗa da Nuratu ta sakata tare da ƴarta Walida. Mami tayi mamaki dan tana da burin sakata makarantar sauran yaran sai gashi ta shammace ta. Godiya ta mata tace sai ta bari za taci gaba da biya mata kuɗin Amma Jidda tace babu komai.
Yaran sun shaƙu da juna musammam matan, Rahma, Hasiya, Nuratu da Walida, duk ƙanƙantar su baka bambanta ya'yan waye.
Tun lokacin da Rahma da Hasiya suka fara girma suka fahimce Mami da Abban su basa tare.Kasuwanci da Mami Sadiya take yi Allah ya sanya masa albarka sai bunƙasa yake, gidan da take ciki ta sayeshi dukka a hannun mijin ƙanwar Zarah ya zama halal ɗinta, ta ƙara gyarashi. Tsakanin ta da Zarah har yanzu suna mutumci.
Alhaji Mamman kuɗi ya zauna masa sosai, kasuwanci ya buɗe, Company sai samun cigaba yake, hankalinshi kwance yake rayuwarshi ya riga ya mance da wata Sadiya balle ƴarta da har yau bai san sunanta ba ko kamanninta.
YOU ARE READING
MADUBIN GOBE
RomanceDuniyar Nuratu cike take da duhun da ta mamaye. Rayuwarta tafe take cikin damuwa da ƙaddarar da ta tsinci kanta. Ko yaushe za ta samu haske cikin duniyarta da rayuwarta? Waye gwanin da zai haskaka mata? Yaya Al-ameen? Col.Ahmad? Dr Awwab ko Mufid? ...