MADUBIN GOBE 26.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb....
Shekara ɗaya kenan da dawowar Mufid Nijeriya ya kasa zaman ƙasar waje, duk da kuɗi da Daddynshi yake tura mishi kuma yana jin daɗin zaman gidan abokin babanshi da babu mai shiga harkar wani kowa rayuwarsa yake a gidan.
Kasa zama yayi a ƙasar dan har lokacin son Nuratu ya kasa barin zuciyarshi, wani mahaukacin so yake ji a ranshi na Nuratu, siffanta da zumarta ya kasa barin ƙwaƙwalwarsa. Mafarkin shi take zuwa da hakan yake ƙara kusanta zuciyarsa da sonta, sai ya farka yake ganin mafarki yake. Haka yasa ya tattaro ya dawo gida.
Alhaji Kashim yayi ta faɗa amma Hajiya Hindatu ta nuna tana son zaman ɗanta kusa da ita ya sa Alhaji Kashim hakura ya barshi. Tsakanin shi da AA da Faisal sai dai waya dan basu ƙara haɗuwa ba tsawon shekarun sai dawowar shi suka ci-gaba daga inda suka tsaya. AA mahaifinshi ya kore shi a gidan dan ya gaji da iskancin shi, ya koma gidansu Faisal da zama da shima mahaifinshi ya cire hannunshi a komai na rayuwarshi ya zuba masa idanu.Yau ake birthdayn Faisal tun jiya suke shirye-shirye, babban hall suka kama inda za su gudanar, sun gayyaci abokansu manya manya har daga wata ƙasa banda ƴan matansu da suma suka zo.
Karfe takwas aka fara gudanarwa gurin cike yake da yara masu ji da kuɗi da iskanci da duniyanci, kiɗa ke tashi wasu na busar sigari, wasu shisha wasu suna kora ruwan wine wasu kuma rawa suke yi kamar ba gobe.Mufid da busar sigari ya zame masa jinin jikin, yana zaune yana ta busar abin shi yana buɗe idanuwansa lumshashshu yana rufe su yana jin daɗin kiɗan dake tashi. Ƴan matan gurin rabi da kwata duk hankulan su na gurinshi da ya tafi da imaninsu domin yayi kyau sosai, dan Mufid akwai kyau ga haske, sai ya zama tamkar gayun Amurka da suke jin daɗin duniyarsu.
Idonshi ne ya kai kan wata black yarinya da take sanye da bakaken kaya riga da wando ta juya baya, rabin fuskarta yake kallo tana magana da yar gefenta tana murmushi, dimple ɗin ta dake na gefe ɗaya ya lotsa. Zuciyarshi ta kasa hanashi da yarda cewa ba ita bace domin idanuwansa sun nuna masa tabbas ita ce.
Bai yarda ba ita bace sai da ya kai kanshi gurinsu ta juyo ya ga ƙarya idanuwansa suke masa. Tsaki yaja ya bar gurin, cikin hall ɗin gaba ɗaya ya bari ya fita waje, motarshi ya shiga ya cigaba da shan sigarin shi. Sai da ya shanye tas kafin yana ƙoƙarin barin gurin AA ya fito."Ina zuwa?"
Fadin AA."Gida."
Mufid ya faɗa yana ƙoƙarin kunna motarshi."Na ga dai ba'a tashi ba."
"To nace maka gida zan je."
Mufid yace ya kunna motarshi ya ja da ƙarfi yana barin gurin. Kai tsaye gida ya nufa ya samu kowa ya kwanta hakan yasa ya wuce ɗakinshi bai iya ko wanka ba ya zube saman gadonshi.
***
MAIDUGURI.
"Ahmadi wai ba za ka yiwa kanka faɗa ba, shekarunka talatin da bakwai amma har yanzu ka kasa ajiye mata. Abin nan fa yana damuwa, kawai magana ne bana yi."
"Kai ma dai ka mishi magana, nayi faɗan nayi har na gaji. Kamar wanda aka asirce shi."
"Babu batun asiri, ra'ayi ne ina ga har yanzu bashi dashi ko Ahmadi? Ko dai budurwarka ta yaudare ka?"
Baban Ahmad da Umma suke mishi faɗa akan rashin aurenshi, shi kam banda murmushi babu abinda yake yi sai ma dariya da yayi jin abin da babanshi yace ya girgiza kai.
YOU ARE READING
MADUBIN GOBE
RomanceDuniyar Nuratu cike take da duhun da ta mamaye. Rayuwarta tafe take cikin damuwa da ƙaddarar da ta tsinci kanta. Ko yaushe za ta samu haske cikin duniyarta da rayuwarta? Waye gwanin da zai haskaka mata? Yaya Al-ameen? Col.Ahmad? Dr Awwab ko Mufid? ...