54.

1.1K 111 5
                                    

MADUBIN GOBE  54.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

***

Awanni saba'in da huɗu kafin faruwar haka.
Da ƙyar Amma Jidda ta sanar da Alhaji Mamman abun da ya ke rubuce a saƙon da aka turomata. Wani jirine ya kwashesa kafin ya daidaita nutsuwarsa sannan ya miƙe.

"Bari in je wajen."

"Muje tare don Allah."

Amma Jidda tace, hawaye take zubarwa mai zafi. Kai kawai ya ɗaga mata ya fita. Da sauri ta ɗauki mayafinta ita ma ta fita, samunsa ta yi har ya kunna motar. Tana shiga a guje ya fita.

A harabar Hotel ɗin ya yi parking ya dubi Amma Jidda da ke kuka.
"Bari in shiga in fito da ita."

Kai kawai ta ɗaga masa ya fita ya wuce ciki. Kiɗane ya ke tashi a gurin, ƴan mata da samari sun cika gurin sai rawa suke yi. Wasu kuma a zaune suna shan drinks da ya ke cike da kayan maye, da alama birthday party ake yi, domin duk an cika gurin da kayan kwalliya da balloons, kuma kowanne ƙananan kayane a jikinsa.

Da ƙyar ya iya jan ƙafarsa ya ƙarasa ciki yana raba idon inda zai hango ɗiyarsa. Ganinsa fa hankalin mutane ya fara yin kansa. Wasun ma zaton ko mahaifin uwar gayyarce.

"Kai old me ye haka? Me ka ke yi anan?"
Faɗin wani saurayi da yake gefen Alhaji Mamman shigowarsa kenan.

Kallon saurayin ya yi da ƙyar ya furta.

"Ameera nake nema. Zainab Mamman Bashir."

"Oh kai ne Daddynta. Ga ta can."

Idanuwansa ya kai gurin inda yayi arba da mummunan gani, ƴarsa ce tsakiyar maza tana tikar rawa, tare da wani namiji da ya ke tayata sai shafa jikinta ya ke.
Jirine ya kwashesa kafin ya kai ƙasa ya dafe kujerar gurin, kusan mintuna biyu ya samu ya dawo daidai yana nufar gurin, yana isa cikin zafin nama ya fizgota tare da kwasheta da mari tagwaye. Duk da cikin maye take ta ji marin ya shigeta sosai, ta ɗago kanta da idanuwanta da suka canza launi.

"Abba!"
Ta faɗa da karfi cike da mamaki da tsoro.

Bai iya bata amsa ba sai wani marin da ya kai mata kafin ya hau dukanta tamkar an aikosa. Duk ihu da ake ya rabu da ita kasawa yayi har sai da samarin gurin suka rirriƙesa, tuni Ameera ta sume don ta bugu. Ko ta kanta bai bi ba ya fizge jikinsa ya fita. Cikin sauri samarin suka ɗagota suka fita da ita. Gaba ɗaya sun fahimci mahaifintane

Amma Jidda da ta ga fitowarsa ta fito da sauri.
"Tana ina?"

"Tana ciki."
Ya faɗa yana shiga motarsa. Za ta yi magana ta ga an fito da ita, da sauri ta ƙarasa gurinsu.

"Me ya sameta?"

"Ku sakata a baya."

Alhaji Mamman yace daga cikin motar, bai bari sun bawa Amma Jidda amsa ba, babu musu suka sakata suna matsawa. Da sauri Amma Jidda ta shiga ya kunna motar sai asibiti.

"Dan Allah Abbansu Rahma ka sanar dani me ya sameta."
Amma Jidda tace cike da tashin hankali, fatanta ya sanar da ita ba abin da ta ke zargi bane.

MADUBIN GOBEWhere stories live. Discover now