7.

1.4K 146 2
                                    

MADUBIN GOBE 7.

Pharty Bb.
Wattpad phartybb.

....

"Nuratu?"

Da kyar ta buɗe idanunta da suka fara canza launi ta dubi Mami da take zaune gefenta, bayan sun shigo gidan ta zube saman kujerun falon tayi kwanciyarta.

Hannu Mami ta saka ta kamo hannuwan Nuratu da ta bita da ido.

"Bana hanaki saka damuwa a ranki ba, bana son ciwonki ya tashi don Allah ki daure ki kawar da komai a ranki, ki duba halin da muka shiga dalilin haka, Nuratu in bana ganin dauriya tattare dake bana jin kwanciyar hankali a rayuwata, sai in ga har yanzu ba ki gama warkewa ba. Duk da nasan kina ƙoƙari, ki daure ki ƙara. "

Mami ta ƙarasa maganar cikin ƙarayar murya.

Murmushi Nuratu tayi ta damƙe hannun Maminta.
"Mami kaina yake ciwo, amma babu komai."

"Shikenan to tashi muje ganin babyn Hasiya, waya sani ma ko sabon miji na samu."
Mami tace tana dariya dom kawarwa Nuratu damuwarta.

Ita ma dariyar Nuratu tayi tana ƙoƙarin danne damuwarta, ta tambayi Mami.

"Sun koma gida ne?"

"Eh muje can, in za ki zauna mata zuwa bayan suna sai ki ɗauki kaya."

To Nuratu tace ta miƙe ta shiga ɗakinta ta ɗauki kayanta cikin kits ƙarami ta fito suka fita.

...

Gidan har ya fara cika da mutane suka karɓi baby suna gani, babynta mace kyakkyawa fara tasha kayan sanyi farare. Bayan Mami ta miƙawa Nuratu babyn ta hana kowa karɓa.

Mami bata jima ba ta koma gida ganin su kansu sun isa kula da mai jego, ga Aunti Rahma ga Walida da Ameera mai bin ta ga Nuratu da Aunti Rukayya.

"Ki kula da ita Rahma dan Allah. Ki tabbatar tasha maganinta a kan lokaci."
Mami take faɗawa Aunti Rahma kafin ta wuce.

"Mami menene? Wani abun ya faru."
Aunti Rahma tace cikin damuwa.

"Kusan hakan ne, lafiyarta ƙalau ta dawo daga gidanki amma zuwanmu asibiti ya kusan dawo mana da aiki baya, ki kula da ita kar ku barta cikin damuwa."

"InshaAllah Mami komai zai wuce."
Aunti Rahma tace cikin tausayin ƙanwarta da wannan ƙaddara ta gifta a rayuwarta da nasu gaba ɗaya.

Tun da Mami ta tafi Rahma ta saka ido akan Nuratu har dare da ta lura ta kasa walwala gaba ɗaya ta zauna ta zuba jaririyar ido, Walida da Aunti Hasiya sai hira suke Ameera da Rukayya sun koma gida.

Da ido Aunti Hasiya ta nunawa Aunti Rahma Nuratu ta ɗaga mata kai alamar ta ganta.

"Ƙanwata!"
Aunti Rahma tace tana zama gefen Nuratu da ta juya a ɗan firgice ganin Aunti Rahma ne ya sata sauƙe ajiyar zuciya.

"Wa kike tunani? Yaya Al-ameen ko sauran samarin ki?"

Ɓata rai Nuratu tayi tana yamutse fuska.
"Babu kowa ciki. Ni fa ba samarina bane, dukkan su mutunci muke, kuma kun sani."

MADUBIN GOBEWhere stories live. Discover now