MADUBIN GOBE (Haske) 48.
Pharty Bb.
Wattpad phartybb.
***
"Lafiya lau Jidda ki kwantar da hankalin ki, babu komai sai alheri."
Ajiyar zuciya Amma Jidda ta sauƙe tana fatan hakan, tare da miƙe daga zaunen da take ta ɗauki jakan kayansa da babu komai sai kaya kala ɗaya da abubuwan buƙatarshi. Har cikin motarshi ta ajiye masa jakan tana ce masa.
"A dawo lafiya ka gaishe da su."
"Za su ji. Ki kula da gidan."
Kai ta gyaɗa masa yaja motar ya bar harabar gidan kafin ta koma ciki.
...
Hanyar Gombe ya ɗauka dan tunkaran Yayansa da buƙatarshi, wanda yake fatan bayan yafiya da zai masa ya amshi buƙatarshi, ya tsaya masa bisa cikar burinshi a karo na biyu, ba shi kaɗai ba har sauran yayunsa.
***
Dr Awwab minti minti yake ƙiran Nuratu ya ji ta gamane, sai tace masa da saura domin abin da yawa kuma suna da yawa. Duk ta gaji kamar tayi kuka haka take ji, ba ta taɓa tsammani akwai wahala ba sai yau ga tayi lattin zuwa. Dan ma matan aure na su layin daban da masu ciki da masu shayarwa da kuma wanda ƴan kudune aka turosu nan.
Sai ƙarfe shidan yamma da mintuna ta samu ta karɓi komai nata tun daga uniform, takalma da komai da ya danganci abin shiga camp. Aka sanar da su sai bayan sati biyu za su dawo dan babu zaman camp ga matan aure. Tayi murnan jin haka kuma dama taji labari. Tana gamawa ta ƙira Dr Awwab.
"Na gama Doctor."
Da sauri yace.
"Gani nan zuwa Babyna, kar ki tafi ko ina."To tace masa ta kashe wayar ta zauna tana bin gurin da kallo, kowa da abinda da yake yi. Mintuna kusan ashirin ya ƙirata ta ɗauka.
"Ki fito na iso."
Kayanta ta ɗauka ta fita tana fita bakin get ɗin ya nufeta da sauri ya karɓi kayan hannunta yana mata sannu. Bayan boat ya sakaa zagaya ya buɗe mata ƙofa ta shiga ta zauna kafin shima ya zagaya ya shiga motar suna barin gurin.
"Sannu duk kin gaji."
Dr Awwab yace yana mai da kallonshi kan Nuratu da ta jinginar da kanta kan kujeran motar ta lumshe idanuwanta. Jin maganar Dr Awwab ya sata buɗe idanunta tana faɗin.
"Na gaji sosai wallahi."
"Naga alama. Kina buƙatar hutu da tausa."
Yace yana murmushi ya ɗaura hannunshi saman cinyarta ya matsa kafin ya riƙo hannunta.
Kanta ta kawar gefe. Sauƙar hannunshi da ta ji saman nata ya sata juyowa ta kalleshi, fuskarshi ɗauke da murmushi ya ɗaga mata gira ɗaya yace.
"Ko ba haka ba?""Ni bana so."
Tace ta zare hannunta cikin nashi, bai ce mata komai ba yayi murmushi yaci gaba da tuƙi. Wahalar da ya bata jiyama kaɗai ya isheta, da nashi da na yau duk sun mata rubdugu.Horn yayi aka buɗe ƙofar gidan ya shigar da motar ciki, bayan ya faka Nuratu ta sauƙa tana ɗaukar jakanta. Shi ya shigo da kayanta ciki falon ya samu bata nan, ya wuce da shi ɗakin ƙasa ya saka, ya fito ya wuce bedroom ɗinshi. Alwala yayi ya wuce masallaci jin ƙiran sallar magriba.
YOU ARE READING
MADUBIN GOBE
RomanceDuniyar Nuratu cike take da duhun da ta mamaye. Rayuwarta tafe take cikin damuwa da ƙaddarar da ta tsinci kanta. Ko yaushe za ta samu haske cikin duniyarta da rayuwarta? Waye gwanin da zai haskaka mata? Yaya Al-ameen? Col.Ahmad? Dr Awwab ko Mufid? ...