🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
'''®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓'''*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
'''ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH'''
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Twenty*
________🎓 An tsai da ranan auren nan da kwana huɗu masu zuwa ranan juma'a kenan
Kuma duk wannan abun da ake yi babu sanin Khalil, Dad ne yace kar a faɗa masa a bari sai ranan ɗaurin aure
Don haka Sameer da Brr. Tahir ne suke ta shirye-shiryen bikin, wanda yadace su gayyata sun gayyace shi duk da ba wai taron biki za'a yi sosai ba, kuma duk wani gyara na gidan sa su ne kan gaba akai
Abba ya haɗa mata duk wani kayan ɗaki da Yakamata ayi mata, shiyasa da aka kai kayan gidan sai su Sameer suka kwashe kayan Khalil ɗin dake ɗakin sa suka zuba nata, sai suka bar masa abubuwan da zai iya buƙata, amma gadon sa dasu sip ɗin sa duk an sauya dana Halwa
Ummi bata yi ƙyashin gyara Halwa ba duk da kuwa lokaci yazo a ƙure kuma gashi tana cikin jego, but duk wani abinda yakamata tayi mata
Halwa dai bata iya mata musu duk abinda tasaka ta tana yi, ko kaɗan bata damuwa da kanta wai ko tana son sa ko bata son sa, ita kawai Saleema ce a ranta, me zai faru idan har tasan cewa ta aurar mata miji? Hakan na ɗaga mata hankali matuƙa har tashiga ɗaki tayi ta kuka, tana jin cewa bata kyauta ba kuma sannan ita butulu ce, ta ɗau alwashi da dama aranta wanda babu wanda yasan hakan sai ita kanta.
Fannin su Mom sun haɗo akwati guda biyar maƙare da kaya, komi sai son barka, duk da a ƙurarren lokaci aka yi komi amma kasancewar da kuɗi komi ya tafi yanda suke so.
Ranan Friday Dad da kansa yakai ma Khalil kayan da zai saka, sun matsa sai da aka sallame shi a ranan saboda jikin da sauƙi sosai domin har riga yake iya saka wa
Khalil yayi mamaki sosai yanda aka bashi sabbin kaya yasaka, sannan kuma har yau yana fargaban Dad da be mishi maganar jaririn sa ba kamar yadda Sameer yafaɗa masa zasu haɗu ne, saka kayan yayi su Sameer ɗin sai tsokanar sa suke yi
Su ma a lokacin suna cikin ɗakin sun sha sabbin kaya iri ɗaya har Dad, sai dai shi nashi har da malin-malin, abun ya ɗaure ma Khalil kai amma be yi magana ba bare yatambaye su
Haka suka fito suka kwashe komi nasu suka hau mota sukai gida
A ƙofar gidan mutane ne sosai ƴan ɗaurin aure duk da ba wani gayya sukai ba, su ma su Dad basu shiga ciki ba sai suka fito suka nufi masallacin ƙofar gidan
Khalil na biye dasu yana ta mamaki, musamman da yaga wasu daga cikin abokan aikin sa, sai kuma yanda ake bashi hannu ana gaisawa dashi suna kiran sa Ango, sai abun yasake ɗaure masa kai, kallon Brr. Tahir dake kusa dashi yayi yace

YOU ARE READING
BARRISTER IBRAHIM KHALIL
RomanceLabarin wani matashi ne me farin jini da Sa'a, duk abinda yasaka a gaba to sai yasami Sa'a