🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
'''®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓'''*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
'''ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH'''
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Twenty Eight*
________🎓Yana tura ƙofan Halwa tabuɗe idanun ta, dama tun ɗazu bata yi barci ba tunani ya cika mata zuciya
Jin ya nufo wajen gadon sai tasake Rufe idanun ta tana sauraron bugun zuciyar ta dake sake hauhawa
Ajiyan zuciya yasauke lokacin da ya'iso bakin gadon yasami waje yazauna, fuskarta yake kallo kasancewar Facing ɗin sa take yi kuma da hasken lantarki da yakunna shigowar sa, yasan ba barci take yi ba don haka yace
"Tashi zaune muyi magana".
Runtse idanuwan ta tasake yi, sai kuma ahankali taware su kan bayan sa da yajuya mata, tashi tayi tazauna tana sake jawo bargon jikin ta duk da ba wai ta saka kayan barcin me nuna tsiraici bane, sai dai kasancewar yanda yalafe a jikin ta ana ganin komi, gashi kuma rigan iyakan ƙasan gwiwan ta yatsaya
Shima gyara zaman sa yayi sosai yana fuskantan ta
Kanta a ƙasa tana jiran abinda zai biyo baya, sai dai shiru yaƙi yin magana, ita kuma ta kasa ɗago kai bare ta kalle sa sabida tasan idanun sa na kanta
Zuba mata idanu kawai yayi yana kallon ta, jujjuya maganar da yake son furta mata yake yi a zuciyar sa, sai da ya ɗan ja lokaci kafin yafesar da numfashi yabuɗe baki yasoma magana
"Halwa". Yakira sunan ta a hankali
"Na'am". Ta'amsa masa batare da ta ɗago kanta ba
Hannayen sa yahaɗe waje ɗaya kafin yace "Da farko dai ina so in baki haƙuri agame da zamantakewar da mukayi abaya, sabida yanda na nuna miki halin ko in kula a matsayin ki na Matata, duk da ba wai nayi hakan a son Raina bane, har a cikin zuciyata ina jin zafin abubuwan da nayi miki, don Allah idan na ɓata miki ki yafe min yanzu ina so mu gyara zaman auren mu ne shiyasa nake so mu soma fahimtar juna a yanzu ɗin".
Lumshe idanuwan ta tayi hawayen da suka soma sintiri a fuskarta tun soma maganar sa suka ci gaba da tsiyaya, wani irin sanyi ne yake ratsa ta har cikin zuciyarta, har a yanzu ɗin ma bata ɗago kanta ba tace dashi
"Yaya Khalil wlh baka yi min komi ba, idan ma har kayi min to na yafe maka domin ban taɓa kallon ka matsayin me cuta min ba".
Tattausan hannayen ta yariƙo cikin nasa wanda sai da yasaka suka ji tsigan jikin su ya tashi, domin hakan ba wai ya taɓa faruwa bane dasu, fatar jikin junan su be taɓa haɗuwa waje ɗaya ba

YOU ARE READING
BARRISTER IBRAHIM KHALIL
RomanceLabarin wani matashi ne me farin jini da Sa'a, duk abinda yasaka a gaba to sai yasami Sa'a