🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
'''{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}'''*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*⚜{{F.W.A📚}}*
'''ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH'''
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._*MARUBUCIYAR*
'''NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.'''.
*CHAPTER 9*
"Mom wai yaushe Dad zai dawo?"
Shafo suman kanshi tayi tace
"Inaga sai gobe zai dawo, amma kaneme shi ta waya mana".
"Ok".
Mom tace "ɗazu Sameer yake sanar dani jibi tafiyan ka ko?"
Gyaɗa mata kai kawai yayi yana gyara zaman shi
"Ok Allah yakaika lafiya, kadai ta addu'a banaso kana wasa da addu'a, kasan aikin nan naka akwai maƙiya sosai dole sai kariƙa neman kariya wajen Allah, nima ina nan ina tayaka, Allah yamaka albarka yasa kafi haka Autana".
Murmushi Khalil yayi yace
"Ameen Mom, dama Ina so ince miki zan dawo da Nazeefa wurinki sai tazauna anan".
"Ok ai babu damuwa kadawo da ita, dama nan ɗin yafi dacewa kakawo ta, yanzu katashi muje kaci abinci tunda an gama".
Be musa mata ba yamiƙe yanufi wajen dainning ɗin, itama biyo shi tayi suka zauna a jere sannan tayi saving ɗin sa, yasoma cin abincin ita kuma tana masa hira, shi kuma sai dai yasaurare ta da kunni kawai wani lokacin kuma yana gyaɗa mata kai.
******
Shigowan ta sau biyu cikin ɗakin tana ganin ta kwance, sai dai ta kasa aiwatar da abinda tazo yi ɗin, yanzun ma har zata koma sai kuma tayanke shawaran kawai zuwa, ahankali tatako tazo bakin gadon tasami waje tazauna, shiru tayi don ta rasa ta ina zata fara, ba kasafai suke magana ba tun kwana biyu da zuwanta cikin gidan, daurewa tayi dai ahankali takira sunan taNazeefa da idanuwanta ke kulle sai dai ba barci take yi ba, hakan yasaka tabuɗe idanunta tabi Lubnan da kallo, sai tasakar mata murmushi tace
"Na ganki shiru ne tun ɗazu, shiyasaka nace ko zakizo kiraka ni zanje gidan mu kar in fita in barki ke kaɗai".
Itama murmushi tayi mata sannan tatashi zaune tace
"Ai babu damuwa anty, muje in rakaki, dama zaman ya ishe ni haka".
Murmushin samun nasara Lubna tayi tatashi tana faɗin
"To muje ko".
Miƙewa Nazeefa tayi taɗau hijabinta dake ajiye saman gadon tasaka, tabi bayan Lubna da har tasoma tafiya zata fice a ɗakin, ahankali take takawa sai dai tafiyan ta ba normal take yin sa ba sabida aikin dake cikin, hakan yasaka take ɗan duƙawa kaɗan, fitowa sukayi daga cikin gidan suka tunkari bakin Gate, har suka ƙarisa babu kowa, shima me gadi ya zagaya baya, don haka kai tsaye suka tunkari ƙofan Lubna tabuɗe suka fice
Daga can nesa wata baƙar mota ce aka faka, ba'a ganin cikinta ko kaɗan, tunda suka fito Lubna tahango motan don haka Direct wajen suka nufa, ita dai Nazeefa sai bin bayanta take yi tana yi tana kalle-kallen tsarin wajen, gaba ɗaya layin gidajen masu kuɗi ne kamar g.r.a haka layin yake.
.
_shin me zai faru?🤔 Ina Lubna zatakai Nazeefa?_
_ku bini asannu don jin me zai faru._
*More comments more post* 💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃💃🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️🏃🏻♀️

YOU ARE READING
BARRISTER IBRAHIM KHALIL
RomanceLabarin wani matashi ne me farin jini da Sa'a, duk abinda yasaka a gaba to sai yasami Sa'a