Part 14

53 2 0
                                    

🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
'''{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}'''

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuƊahirah*👈

         *⚜{{F.W.A📚}}*

'''ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH'''
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*
'''NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.'''

.

      *CHAPTER 14*

Ahankali tasoma buɗe idanuwan ta tana rufewa har sanda tabuɗe gaba ɗaya idanun tana kallon rufin ɗakin, ta ɗan jima ahaka tana son tuno abinda ke faruwa kafin komi yadawo ƙwaƙwalwan ta, dasauri tazabura daga kwancen da take tatashi zaune tana kallon tsararren Palon da yagaji da haɗuwa, idanuwanta akan Nura yasauka da shima yake yashe ƙasa da alamun dai shi be dawo hayyacin sa ba, a gefe da gefen sa kuwa wasu mutane ne manya dasu su biyu sun tsaya a kansa, sai kuma tadawo da ganin ta gefen ta dasauri, nan ma wasu mutane biyun ne kusa da ita, da alama gadin su suke yi

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. ina ne nan?". Ta faɗi hakan ne a fili tana jin zuciyarta na tsinkewa, don tasadakar gidan cin kai ne aka kawo su

"Gidana ne".

Taji maganar ya doki kunnin ta, dasauri tajuyo tana wurwurga idanu, nan kuwa idanun ta yasauka akan sa, yana zaune saman kujera ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya yana sakin murmushi, daga shi sai farar singlate da gajeren wando me ruwan ƙwai da iyakacin sa gwiwa, gefen sa kuma da akwai mutum ɗaya dake tsaye yana gadinsa, wani irin bugawa zuciyarta tayi kamar zatayi tsalle tafaso cikin ƙirjinta, take wani irin tsoro yashige ta har batasan sanda tawaro idanun ta waje ba tana kallon shi, still yana murmushi yace

"Barka da zuwa turaka ta Amarya ta, yau dai gaki cikin gidana abinda nadaɗe ina fata da buri kenan".

Ahankali yatashi yanufo ta har zuwa gaban ta kafin yadakata yana ƙare mata kallo, sai kuma yasoma zagayeta yana tafa hannun sa, wanda duk taku ɗaya da yake yi tana ji ne kamar yana tafiya da bugun numfashin ta, sai da yagama zagaye ta sannan yazuƙuna agaban ta yana kallon cikin idanun ta da tatsayar akan sa ko motsin kirki takasa yi, sosai ganin shi yayi tsananin firgita ta har tana jin komi na jikinta ya dena aiki, murmushi yasaki yana faɗin

"Yau dai na baki mamaki ko? Baki zatan zaki iya zuwa hannun Haris cikin sauƙi ba?"

Sai kuma yasaki dariya yaci gaba

"Dama nace miki zan kafa tarihi cikin rayuwan ki, zanyi miki abinda har kimutu bazaki taɓa mantawa dani ba, to ga ranan tazo, yau duk zan huce wahalan da kika bani, kin bani wahala sosai Babyna".

Yaƙarike maganar yana kai hannun sa saman fuskarta yashafo gefen face ɗinta, kafin yacire hannun dasauri yana zuba murmushi

"Ohh kince in dena taɓa ki ko?" Uhmmm saboda na taɓaki kika cire hannu kika wanka min mari ko? To yau kuma bari inga wani hukunci zaki min, kin san me?"

BARRISTER IBRAHIM KHALILWhere stories live. Discover now