Part 2

146 12 0
                                    

🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
'''{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}'''

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

         *⚜{{F.W.A📚}}*

'''ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH'''
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*
'''NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.'''

.

     *CHAPTER 2*

Ahankali yatura kan motan sa cikin gidan nashi, yaƙarisa parcking space yatsaya, yaɗau 3mint kafin yabuɗe motan yafito, tun sanda yatunkari Compound ɗin gidan yahango bayan ta tana zaune ƙarshen farandan, ga duk kan alamu bata ma san da shigowan sa ba, har zai wuce sai kuma yatsaya yana kallon ta duk da baya ganin face ɗin ta sai bayanta but yasan da akwai abinda ke damunta, shi mutum ne da yake saurin gane damuwar mutum, sau tari aɗan kwanakin nan yana ganin ta cikin wannan hali, sai dai yasan ba hurumin shi bane shiga abun da babu ruwansa, yanzun ma har yafara takawa zuwa wajenta sai kuma yaja yatsaya kana kuma yajuya yashige cikin Palon sa, dai-dai lokacin da ita kuma tasanya hannunta tagoge hawayen da suka zubo kan fuskarta, sosai in kakalle ta zaka hango tsantsan damuwa a tattare da ita, ahankali tamiƙe tanufi cikin gidan, direct kichen tanufa tafara aikin ta, ta ɗau tsawon minti 30 kafin tagama girkin tazuba cikin coolar taje tajera su kan dainning table dake cikin ƙayataccen palon, bayan ta gama tsayawa tayi awajen tayi shiru tana kallon ƙofan ɗakin sa, ta daɗe ahaka sai da taji idanunta sun cicciko da hawaye kafin taɗauke idanunta dasauri tanufi hanyan ɗakinta, akan gadon ta tafaɗa tasaki kuka me tsuma ran me sauraro, ita kaɗai tasan me ke damunta, kuma tasan babu wanda zai iya cire ta daga cikin matsalan da take ciki sai rabbi, domin ita kanta batasan ta ina zata fara aikin da aka sanya ta ba, sai da tayi kukan ta ma'ishi kafin tamiƙe tashige toilet dan ɗauro alwala.

Tunda yashiga ɗakin sa yacire kayan jikinsa direct yashige toilet, ya ɗau tsawon lokaci kafin yafito, yasoma shirya wa cikin sauri, ƙananan kaya yasanya riga sky blue me gajeren hannu wanda tamatse masa Arms ɗin sa, kana yasaka Black trouser, sosai yayi kyau cikin shigan nasa, flate cover shoes yasaka baƙi yafito yanufi masallaci, da tazara sosai da inda gidan sa yake zuwa masallacin, bayan yayi sallan direct gida yanufa yashige ɗakin sa, wani ƙofa yabuɗe yashige, cikin ɗakin kamar  Labrary yake, anan yake karatun sa yake duk wani bincike abinda yashafi aikinsa, akan Hill chair yazauna yajawo lapton ɗin sa dake saman table ɗin yabuɗe yasoma aikin sa.

Wajen ƙarfe 06:00pm tafito daga ɗakin ta tanufi kan dainnig table ɗin, gani tayi babu abinda aka taɓa awajen, aran ta tunani take yi ko be dawo bane? Bata da masaniya, dan haka tayanke shawaran fita taduba motan da yafita da ita, koda tafita ta hangi motan yana nan a inda yake, ga kuma sauran nan da alama dai yana gidan, komawa tayi jiki a sanyaye tashige ɗakin ta, dama tafito da ninyan tagirka mishi abincin dare ne.

Sai da yaji an kira sallan magriba kafin yatashi yafito, direct toilet yanufa yaɗauro alwala yafita masallaci, be dawo ba sai da akayi sallan isha'i, koda yashigo gidan kan dainning yanufa yazauna, yahaɗa ma kan sa Black tea yasha, bayan ya gama yaɗan ci abincin kaɗan yatashi yashige ɗaki, sai da yayi wanka yasanya sleeping dress yafeshe jikinsa da farpume's ɗin sa sannan yazauna gefen gado, briefcase ɗin sa dake ajiye asaman gadon yajawo yaciro wata Black Computer, buɗe wa yayi yasoma aiki, sai da ƙarfe 11:00pm yayi kafin yarufe yakwanta lokacin tuni dama barci yasoma cin ƙarfin sa, yana shafa addu'ar da yayi ko minti 5 be ƙara ba barci yatafi dashi.

......... ............ .........
Washe gari ƙarfe 07:00am Brr. Khalil yagama Shirin sa, yayi shigansa cikin suit black colour, ta cikin kuma white ne, ya sanya socks and black cover shoes, ya gyara gashin kansa sai ƙyalli yake yi gunun sha'awa, gaba ɗaya in banda ƙamshi babu abinda yake tashi ajikin sa, briafcase ɗin sa yaɗauka yafita da sauri ko kallon dainning ɗin da Lubna tagama jera masa break fast be yi ba yafice, ɗaya daga cikin motocin sa kalan sky blue yashiga yaja yafice bayan da Gateman yawangale masa Gate.

Yana fita Lubna tafito daga cikin Toilet ɗaure da showel ajikin ta, kai tsaye inda kayanta yake a sif tanufa taciro wata baƙar doguwar riga me ƙyalƙyalin kwalliya tasaka, tana cikin shafa lotions bayan da tazauna gefen gadon ta taji wayanta yasoma Ringing, dasauri takalli wayan sai da gabanta yafaɗi ganin wanda ke kiran, jikinta na rawa taɗau wayan takara a kunne, bata kai ga cewa komai ba taji muryan sa yana faɗin

"Da fatan kin aikata abinda muka saki?"

Cikin rawan murya tace

"Ban samu dama ba har yanzu".

"Kina so kice min har yanzu babu wani ci gaba?"

"Ee, har yanzu be bani.."

Katse ta yayi cikin kakkausan murya yace

"Kin san abinda zai biyo baya, karki manta Mahaifiyarki da ƙannin ki.."

Sai kuma yakece da dariya

"Uhmm kinsan sauran, kuma kinsan bazan tsaya jiranki har lokacin da time zai ƙure mana ba, dake na dogara.."

Daga haka yadatse kiran batare da yabari tasake magana ba, ahankali ta'aje wayan cike da sanyin jiki, kasa ci gaba tayi da shafa man sai ma tashi da tayi tafara zagaye ɗakin tana me cike da tunani, so take tasamu mafita amma har yau zuciyarta tagaza barin ta, tsananin tausayin sa take ji aranta duk da ita zata cutu, wani ɓangare na zuciyanta tace

"Haba Lubna kifarka daga mafarkin da kike yi, karki manta fa babu abunda yahaɗa ki dashi, kuma kimanta da wata alaƙan dake tsakanin zuciyarki dashi, ki ceto Mahaifiyarki da ƙannin ki daga halaka, idan har kinyi hakan babu cutarwa a wajen shi, kuma hakan shine dai-dai".

Wannan tunanin yasaka tayi saurin fita tadoshi ɗakin sa cike da tunani kala-kala.

BARRISTER IBRAHIM KHALILWhere stories live. Discover now