🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
'''®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓'''*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
'''ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH'''
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._*MARUBUCIYAR*
'''NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.'''.
*CHAPTER 16*
Lokacin da suka isa cikin ɗakin sa na Hotel ɗin Baby Dil akan sofa tayi wa kan ta matsuguni, taɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tajingina bayan ta da kujeran tana kallon shi, shi kuma Direct cikin Toilet yashige, be jima ba yafito yanemi wuri kan kujera yazauna kana yace da ita
"Ina jinki, Please ina son nasan komi ga mutumin nan".
Ɗan sakin murmushi tayi still tana kallon shi tace
"Ni kuma zan sanar da kai komi insha Allahu, katambaye ni duk abinda kakeso".
Gyaɗa mata kai yayi kafin yagyara zaman sa yace
"Akwai wani Alhaji Mubarak da muke Shari'a dashi acan Nigeria, kuma tabbas an tabbatar min da Mr. Jay pitter abokin harƙallan shi ne, don haka nazo bincike kuma ina son nahaɗu dashi".
Baby Dil tace "tabbas da ka isa wajen shi babu abinda zaka samu, domin Alhaji Mubarak na hannun daman sa ne, kaga kuwa babu abinda zaka samu a wurin sa illa ma kasake jagula abin, kamar yanda nace maka xan sanar da kai komi sabida nasan sirrin su ne, a baya mutane irinka sun zo kamar kai don bincike, wasu ƴan sanda ne wasu kuma lauyoyi ne, but kai bansan menene aikin ka ba?"
"BARRISTER". Yafaɗa ataƙaice
"Ok Amma tun sanda naganka naji zuciyata ta kwanta da kai sosai shiyasa nazo wajen ka bcoz nima ina buƙatar taimakon ka".
Shiru tayi tana sauke numfashi, sai kuma tasauke ƙafan ta tahaɗe hannayen ta waje ɗaya tana kallon shi, sannan taci gaba da faɗin
"Zan soma da baka tarihina duk da baka tambaye ni ba but nasan duk abinda kake nema yana da alaƙa da abinda akai min, shekaru 7 kenan da zuwata wannan ƙasan, ko ince aka sai dani a wannan ƙasan, zaka yi mamaki idan nace maka ta sanadiyan maƙocin mu nazo wannan ƙasa, mun kasance mu talakawa ne don haka maƙocin mu yake taimaka mana kasancewar sa me kuɗi, haka kawai watarana yace inxo zai sama mana aiki awani gida, dama abinda muke nema kenan musami aikin da zamu dogara dashi ni da iyayena, kwana biyu da soma zuwana, uban gidan mu yakai ni wani gida, ni dai ban fahimci ko ina ne ba amma akawai ƴan mata irina da yawa don mun kai mu sha biyu, muna ji muna gani akai mana allura wanda bamu fahimci na menene ba, tun daga lokacin hankalin mu yagushe, ashe makocin mu ne yasiyar dani ga mutumin da yasamar min aiki gidan sa, shima kuma yasiyar dani ga wani uban gidan sa".
Shiru tayi tatsira ma waje ɗaya idanu taci gaba da faɗin
"Wannan alluran da akai mana yagusar mana da hankali, anyi haka ne don su cin ma manifan su akan mu, suna harƙallan sai da coken that's why suke samun ƴan mata sufarka cikin su azuba musu coken ɗin nan aciki, alluran da ake yi yana da ƙa'ida, yana ɗaukan iya awannin da zai kai mu ƙasan da za'a kai mu ne, don haka lokacin da akai mana hankalin mu gushewa yayi bamu sake sanin inda muke ba sai a wannan ƙasar, sun kawo mu nan an kuma mana aiki an cire mana coken ɗin, sai dai basu bar mu haka ba suka sai damu ga Mr. Jay pitter, mutum ne shi da yake safaran ƴan mata ƙasa-ƙasa wasu kuma yamai dasu karuwan sa don samun kuɗi dasu, acikin waɗanda muka taho tare gaba ɗaya yasiyar dasu a wasu ƙasashe sai ni da wata yabar mu a matsayin karuwan sa, tun sanda natsinci kaina a wannan ƙasa nake kuka ina roƙon su da sumai dani ƙasata, sai dai aikin gama yariga da yagama su mutane ne da basu tsoron Allah, daga farko da sukaga ina musu taurin kai har nayi yunƙurin guduwa haka sukai ta gana min azaba, but duk da haka ban sa ran wataran zan ƙi guduwa ba, sai dai duk wani hanya da yakasance zan bar ƙasar nan sun toshe ta, ataƙaice dai zan faɗa maka babu yanda za'a yi nabar ƙasan nan batare da sanin su ba, haka nahaƙura naci gaba da zama dasu nima har lokacin da nasaba, nima nadawo nagoge azahiri namanta da komawa ta gida, sai dai abaɗini abin na nan araina, aduk sanda natuna da iyayena sai nayi kukan baƙin ciki, ina tunanin awani hali suke na rashina, shiyasaka har yanzu ban fid da raina zan koma ba".
Muryan ta da yasoma rawa ne yasaka ta yin shiru, sai da tashare hawayen fuskarta kafin taci gaba
"Shi kuma Alhaji Mubarak tare suke harƙalla da Mr. Jay Pitter, yana kawo masa ƴan mata sosai, duk wani aikin da Mr. Jay yake yi tare suke yi dashi, nasan shi sosai domin yana yawan zuwa nan ɗin, kuma insha Allahu duk wani sirrin su zan iya nemo maka inhar kayi alƙawarin zaka mayar dani ƙasata, ina son nakoma gun iyayena, kataimake ni don Allah, sosai naji zuciyata ta aminta da kai". Taƙarike maganar tana fashewa da kuka
Brr. Khalil kallon ta kawai yake yi cike da tausayin ta, sosai tabashi tausayi kuma yana ji aran sa insha Allahu sai ya taimaka mata, dama wannan daman yake nema wanda zai kawo ƙarshen masu safaran mata, koda iyakan Alhaji Mubarak da mutanen sa yakawar tabbas yasan ba ƙaramin Jihadi yayi ba, ko ba komi za'a rage yawaitan mugaye irin su, ajiyan zuciya yasauke yana tuno Nazeefa
"Yanzu shikenan da itama nan za'a kawo ta? Yarinya ƙarama, kai amma waɗannan mutanen basu da imani, Allah kaɗai yasan iya adadin yaran da suka kawo waɗanda ma basu kai ta ba".
Numfashi yaɗan ja yana kallon ta yace
"Kiyi shiru Fadila, insha Allahu zan taimaka miki kibar wannan ƙasan, zaki koma ga iyayen ki in Allah ya yarda nayi miki alƙawari".
Kallon shi tayi da idanuwanta da sukai jazur tayi masa murmushi tace
"Nagode sosai".
"Babu godiya tsakani na dake, ke dai ki aiwatar da duk abinda zan saka ki".
Daga nan yasoma bata bayanai akan abinda yakamata tayi masa, sun daɗe suna tattaunawa kafin tatafi, shi kuma tashi yayi yashige toilet yayo wanka tare da ɗauro alwala yafito, shirya wa yayi cikin farar jallabiya da dogon wandon jeans yashimfiɗa sallaya yayi sallah, sannan yamiƙe yaɗau tellphone ɗin dake ɗakin yakira Receptionist yayi odan abinci, yana zama babu jimawa akayi nocking door ɗin yaje yabuɗe ya'amso yadawo yazauna yasoma ci, abincin yake ci sai dai hankalin sa baya wajen yana nazari, wayan sa dake saman gado tasoma ringing hakan yasaka yaɗan kalli wajen kafin yasauke ajiyan zuciya, yamiƙe yanufi inda wayan take yaɗauka, ganin Bro ɗin sa ne babu ɓata lokaci yayi peacking call ɗin yana zama
"Hello My Bro".
"Hi ɗan ƙanina ya kake?"
Ɓata fuska Khalil yayi yana shafa goshin sa yace
"Bro bana so".
Dariya Sameer yayi yace
"Sabida me um ɗan ƙanina?"
Shiru yayi yaƙi magana
Still dariya Sameer yasake yi yace
"I'm sorry dama tsokanan ka nake, ai yanzu kai big boy ne tunda kafara aje yara, kasan fa Hakima ta haihu".
"Dagaske Bro? Yaushe? Me tahaifa?" Yayi masa tambayoyin ajere yana miƙewa yakoma wajen abincin sa
"Yanzu babu daɗewa, ai nayi tunanin Mom tariga ni sanar maka, namiji tahaifa".
"A'a tun safe da mukai waya bamu sake ba, Allah yaraya shi Yaya, ina fata ni za'a yi wa takwara ko?"
Sameer yace "tabb kai awa?"
"Ni a Dadyn sa, Please Bro kasan munyi alƙawari dani da kai, duk wanda yahaihu cikin mu zamuyi ma junan mu takwara".
"A'a to ai bance maka na fari ba, ni Dad zan ma takwara sai dai kabari tasake haihuwa lokacin ma kayi naka auren, kaga sai su tashi tare ko?"
Ajiyan zuciya Khalil yayi yace
"Dama haka zakace ai, kafison Dad dani, shikenan sai kayi ta sakawa".
Dariya Sameer yasaki jin yanda Khalil ɗin yayi maganan cike da shagwaɓa, cikin dariyan yace
"Haba autan Mom Kar kayi fushi tunda nace zan saka, kuma kasan da cewa ni dama na wurin Dad ne, dole na fifita shi akan ka, amma fa ina son ka sosai fa, daga shi sai kai a zuciyata".
Murmushi Khalil yayi yace
"Uhmm naƙi daɗin bakin, ai dama Mom ta sanar dani kuma yanzu na yarda, yanzu ni dai kagaishe min da me jegon da kyau da kyau tare da My Son".
"Ok zasu ji, ya aikin naka? Dafatan komi yana tafiya normal?"
"Alhamdulillah Yaya, Ina samun duk abinda naje nema".
"To Allah yataimaka yabaka Sa'a".
"Ameen Bro, katura min photon Baby ta WhatsApp in ganshi".
Sameer yace "ok yanzu kuwa".
Daga nan sallama suka yi, yaci gaba da cin abincin sa yana latsa wayan sa.
YOU ARE READING
BARRISTER IBRAHIM KHALIL
RomansLabarin wani matashi ne me farin jini da Sa'a, duk abinda yasaka a gaba to sai yasami Sa'a