🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
'''®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓'''*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
'''ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH'''
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya.__Wannan shafin naku ne masoyana na cikin group ɗin Khaleesat Haydar, na gode da nuna soyayyar ku gare Ni, Allah yabiya._❤️
*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Nine*
________🎓Yana zuwa wajen sai dai babu ita, ya dudduba amma be ganta ba don haka yakoma cikin ɗakin da aka kwantar da Fahima, dama kawai don ta tsaya masa a rai ne but tunda yaduba be ganta ba sai be sake tuna ta ba har yabar asibitin.
____________________
Halwa tana tashi a wajen komawa ɗakin tayi, sai dai tana zuwa bakin ƙofa kunnuwan ta suka jiye mata maganganun Abba dake faɗa ma Ummi matsalan Saleema ɗin, sai kawai tazame nan ƙasa tasaki kuka me sauti, daga inda take zaune tana jin kukan Ummi itama don takasa jurewa, sai da Abba yayi ta rarrashin ta yanuna mata zata iya damun Saleema idan bata dena kukan ba tunda an ce kar suyi hayaniya da zai dame ta, hakan yasa Ummi tarage kukan ta takoma kukan zuci da hawayeAbba ne yafito yatarda Halwan anan ƙasa tana nata sharɓan kukan, gaba ɗaya idanunta sun rine sun kumbura suntum wanda kallo ɗaya zaka yi mata katabbatar ta jima tana kuka yanda har fuskarta sai da yakumbura
"Subhanallah.. Daughter me kike yi anan? Kukan me kike yi?" Yatambaye ta yana saka hannu yaɗago ta
Halwa bata iya bashi amsa ba sai ƙara sautin kukan ta da take yi, duk da kuwa ta toshe bakin ta da Hijabin ta hakan be hana an ji fitan sautin kukan ta ba
Dafa kanta Abba yayi cike da ƙarfin halin sa yace "kiyi shiru kinji? insha Allahu ƴar uwanki zata samu sauƙi ki dena kuka haka nan".
Ya daɗe yana rarrashinta kafin yabuɗe mata ƙofar ɗakin yabata umarnin tashiga, shi kuma yajuya yatafi.
Tana shiga taƙarisa gaban gadon inda Ummi ke zaune ta tasa Saleema agaba tana zirarar da hawaye
Gefen gadon taɗan ɗofana mazaunan ta tana kallon Saleeman itama, wasu sabbin hawayen ne suka soma sintiri a face ɗin ta sabida tausayin ta, lumshe idanuwan ta tayi tabuɗe su akan Ummi da har yanzu ko ƙifta idanu bata yi, cikin rawan murya tace
"Yanzu shikenan Ummi.. baza ta haihu ba? Meyasa za'a juya mata mahaifa? Meyasa baza'a nema mata magani ba? Don Allah.. kar ayi.. gaggawan wannan..aikin". Taƙarike maganar nata cikin tsananin rawan baki da jan numfashi
Itama Ummi numfashin taja cike da sanyin murya da idan kaji zaka san tana cikin matuƙar damuwa tace "Ni kaina bansan wani irin ciwo ne wannan dake damun ta ba, sai dai sun tabbatar mana akwai wasu tsirrai a cikin mahaifan ta da baza su taɓa bari ta raini ciki ba, sannan kuma mahaifan ta babu ƙarfi ko anyi mata aiki ba lallai ne asamu nasara ba".

YOU ARE READING
BARRISTER IBRAHIM KHALIL
RomanceLabarin wani matashi ne me farin jini da Sa'a, duk abinda yasaka a gaba to sai yasami Sa'a