Part 3

127 9 0
                                    

🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO📚*
'''{{Ɗaya tamkar da Dubu💪}}'''

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

         *⚜{{F.W.A📚}}*

'''ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH'''
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

*MARUBUCIYAR*
'''NAFEESAT
LABARIN DEEBIZAH
JARUMAI
RAYUWATA
NUSNIM
BUTULCI
SO MAI ZAFI.'''

.

     *CHAPTER 3*

Har ta kama handle ɗin ƙofan zata murɗa sai kuma tayi saurin saki tajuya dasauri tasauke idanunta kan tanƙamemen agogon dake manne  can saman bango, ƙarfe 07:25am hakan yasaka tasauke ajiyan zuciya don tasan babu shi yariga ya fita, ahankali tamurɗa tashige tasoma dube-duben drowers da sif ɗin sa, ta daɗe tana dube-dube cikin ɗakin bata ga komi ba, ƙarisawa tayi jikin ƙofan da yake shiga yayi aikin sa tare da aje duk wasu muhimman abubuwan sa, tana taɓa ƙofan kamar ko yaushe a kulle yake hakan yasaka tajuya jiki a sanyaye tasoma gyaran cikin bedroom ɗin, bayan ta gama tawanke toilet sannan tafito palow, nan ma sai da tagyara ko ina kafin tanufi ɗakin ta.

.... .... ..... .... .... ....
Nocking ƙofan da akayi ne yasaka shi ɗan tsakaitawa daga aikin da yake cikin Computer

"Yas come in". Yabada umarni yana ci gaba da aikin sa

Ahankali taturo ƙofan tashigo, sai da tajingina da ƙofan tana ƙare mishi kallo na 30soconds kafin daga bisani tasoma takowa cikin office ɗin tanemi kujera tazauna inda aka tanada don baƙi, shiru tayi taci gaba da kallon sa batare da tayi magana ba, sam bata gajiya da kallon shi sabida sosai take mutuwar ƙaunar shi, komi nashi me kyau ne ba inda yake da makusa, ya haɗu ne tako ina duk da kasancewar shi baya da farar fata but skin ɗin sa irin golden colour ɗin nan ne me shaining, yana da kyawun fuska wanda yake zagaye da ɗan siririn saje baƙi siɗik gunun sha'awa, idanuwansa farare ne ƙal kamar zaiba, yana da dogon hanci har zuwa ɗan madaidaicin bakin sa me ban sha'awa da ƙananun lips, shi ma'abocin barin suma ne me tarin yawa, don haka koda yaushe sai dai kaganshi yayi gyaran fuska ba dai yayi aski ba, yana da tsayi sosai da faɗin chest kuma yana da ɗan jiki don baza'a kira sa siriri ba.

"Wai lafiya kika tasani gaba kike kallona?" Muryan shi takatse mata tunanin ta da take yi a kansa

Ɗan firgigit tayi tana sauke ajiyan zuciya kafin tasaki yalwataccen murmushin da yaƙara ma face ɗin ta kyau, cikin sanyin murya tace

"Koda yaushe bana gajiya da kallon ka ne My Ib, Burina ako yaushe kakasance mallakina ni Ni kaɗai, ina Son ka da yawa My Ib, har yaushe ne zan ta jiranka kayarda dani a matsayin wacce zata zama abokiyar rayuwanka? Yaushe ne nima zaka nuna min ƙauna kamar yanda nake tsananin ƙaunarka da begen ka? Yaushe zaka tausaya min kaji ƙaina kagane babu wacce tafini ƙaunarka a faɗin duniyar nan?".

Duk maganar da take yin nan idanuwanta na kansa batare da ko kaɗan ta ƙifta su ba, hakan yasaka har ƙwalla suka taru cikin idanun suna shirin zubowa

Sai lokacin yaɗago kanshi yasauke idanunshi cikin nata, dai-dai da lokacin da wasu siraran hawaye suka ɗigo saman kuncin ta, tsira mata idanun sa masu matuƙar kaifi da kyawu yayi na ɗan wani lokaci kafin yaɗauke kai yaci gaba da aikin sa, cikin sweet voice ɗin sa yace

BARRISTER IBRAHIM KHALILWhere stories live. Discover now