chapter Seventeen

76 5 2
                                    

🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
   *BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
                        ♠️

*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_

*بسم الله الرحمن الرحيم*


*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
'''®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓'''

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattpad: UmmuDahirah*👈

         *\F.W.A📚/*

'''ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH'''
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._

*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._

       *BOOK TWO*

.

_______________________________

        *CHAPTER Seventeen*

________🎓 *2 Hours Ago*

Suna zaune gaba ɗayan su a reception sun yi cirko-cirko hankalin su duk a matuƙar tashe, babu abinda suke tsimaye yanzu sai fitowar doctors su san wani hali suke ciki

Ummi da Mom sai faman share hawaye suke yi domin labarin abinda yafaru da yariske su ba ƙaramin girgiza su yayi ba

Fitowar Babban doctorn da ya jagoranci duba Su Khalil yasaka suka nufe sa gaba ɗayan su suna jera masa tambayoyi ko wannen su yana tare da fargaban amsar da doctor ɗin zai bayar

Likitan be ce komi ba illa ce musu da yayi su bi sa Office

A tare Dad da Abba tare da Sameer suka bi bayan sa yayinda su Mom suka kasa haƙura suka take musu baya

Bayan sun shiga sun zazzauna likitan  yacire Glasses ɗin sa yana saka Handkerchief yashare zufan goshin sa sannan yadube su ɗaya bayan ɗaya yasoma da faɗin

"To alhmadulillah zamu ce tunda komi ya zo da sauƙi ba kamar yanda muka yi zato ba, duk kan su suna da rai, kuma munyi nasaran cire masa harsashin dake jikin sa insha Allahu nan da kwana biyu zai iya farfaɗo wa, sannan..."

Sai yasaki numfashi yana ci gaba da faɗin

"Ita kuma Saleema gaskiya matsalan ta babba ne, domin sanadiyar hakan zuciyar ta tayi wani irin razana wanda yahaddasa mata matsala ainun, kuma hakan ya saka Zuciyar ta tana barazanar bugawa wanda Allah ne kaɗai yatsare be kai ga bugawan ba, but.. yanzu ta shiga Coma farfaɗowar ta sai ikon Allah.."

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Ummi tafaɗa tana fashe wa da kuka, a tsaye take sai taja da baya tajingina da bango tana kuka kashirɓan jin halin da ɗiyarta mafi soyuwa a gare ta take ciki

Su kansu su Dad hankalin su yayi matuƙar tashi musamman Abba da yacire hulan sa cikin tashin hankali, babu abinda yake yi sai salati, sosai zuciyar sa ta taɓu da halin da yaji ƴar sa a ciki, sai dai ƙarfin hali da ya ara ya yafa ma kansa yayi juriyar hana kansa kuka

Shiru ne yaratsa a tsakanin su gaba ɗaya babu wanda ya'iya buɗe baki a cikin su

Girgiza kansa Doctor yayi cike da tausayin su yace "haƙuri zaku yi haka Allah yaƙaddaro, am.. ita kuma ɗayar Allah ya sauke ta lafiya duk da dai itama sakamakon gigitan da tayi jinin ta ya matuƙar hawa, sai dai muyi fatan samun lafiyan ta".

BARRISTER IBRAHIM KHALILWhere stories live. Discover now