🎓
🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*BARRISTER IBRAHIM KHALIL*
♠️*Written:✍️ By Nafisat Isma'il*
_(Feenah Jikar Lawal Goma)_*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER'S ASSO📖*
'''®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓'''*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuDahirah*👈
*\F.W.A📚/*
'''ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH
ALHAMDULILLAH'''
_ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._*SADAUKARWA*
_na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._*BOOK TWO*
.
_______________________________
*CHAPTER Seven*
________🎓Tana shiga zaure sukaci karo da Umma dole taja tatsaya tana ƙifƙifta ido
Umma da tafiddo ido waje tana kallon Zainab ɗin da taɓaryan dake hannun ta tace "na shiga uku ni Jummai me zan gani haka Zainab? Ashe dama baki da mutunci dan ubanki? Yanzu abun naki har ya kai kifita da taɓarya kije wajen Nura? To me kike shirin aikatawa kenan?"
Turo baki Zainab tayi tana sosa kai, sai kuma tajuya dasauri tayi ciki tana jefar da taɓaryan
"To dan ƙwal uwar ki zo ki wuce kije wajen shi". Cewar Umma tana bin bayan ta itama tashiga cikin gidan
"Wlh Umma babu inda zani, nifa nace miki bana ƙaunar sa bana son sa bana son sa, Ni bazan iya son sa ba wlh".
Umma kama haɓa tayi tana kallon Zainab ɗin dake masifa kamar batasan da wa take yi ba
"Zainab Ni Sa'an wasan ki ne ina faɗa kina faɗa? Wlh sai kin fita ko in saɓa miki kamanni, shashashan yarinya mara hankali.."
Kuka Zainab tafashe dashi
Sai umma kawai takama haɓa tana kallon ta
Cikin kukan take cewa "wlh Umma bana ƙaunar sa, koda kuwa be so Halwa ba Ni bana son sa, har cikin raina nake faɗa miki bazan iya auren sa ba wlh".
Sai taja majina tanufi wajen butan ta tazuƙuna tasoma alwala
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un yanzu Zainab har kin isa in saka ki abu kice baza kiyi ba? Baza ki tashi ki wuce ba yana jiran ki?"
Cikin tsananin ɓacin rai Zainab tace "Umma zan yi sallah ne lokaci na ƙurewa, kuma kinsan illan rashin yin sallan Asar da wuri, yana ɗaya daga cikin sallolin da ake so mutum yakula..."
"Dalla rufe min baki, kiyi sauri ki idar kizo ki wuce".
Zainab bata sake cewa komi ba taci gaba da alwalan ta, sosai take mamakin Mahaifiyar ta akan yanda tasauya lokaci ɗaya akan Nura, duk da tasan Nura yana banka mata kuɗi da kaya amma kuma bata taɓa tunanin zata sauya har haka ba
Tana idar wa tashiga ɗaki tasaka Hijab tasoma sallah, ta ɗau lokaci tana yin Sallah taƙi tasallame sai da Umma tazo tasake mata magana sai faman masifa take mata
Dole Zainab ba don taso ba tamiƙe tafito tafice
Tana fita kuwa taganshi tsaye gaban motar sa, ta rasa wani irin mayen mutum ne wannan
YOU ARE READING
BARRISTER IBRAHIM KHALIL
RomanceLabarin wani matashi ne me farin jini da Sa'a, duk abinda yasaka a gaba to sai yasami Sa'a